Ice Prince: Mai wakar ‘Oleku’ ya shiga hannu kan barazanar dukan dan sanda

Ice Prince ya yi kurarin jefa dan dan sandan da ya kama shi a kogi

Ice Prince: Mai wakar ‘Oleku’ ya shiga hannu kan barazanar dukan dan sanda

Ice Prince

Fitaccen mawakin Najeriya, Penshaw Henry Zamani, wanda aka fi sani da Ice Prince Zamani, ya shiga hannun hukuma, kan barazanar dukan dan sanda da jefa shi a kogi.

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Legas, SP Benjamin Hundeyin, ya sanar a shafinsa na Twitter cewa lamarin ya faru ne bayan jami’an rundunar sun kama mawakin yana tuka wata mota mara lamba da tsakar dare, wanda kuma ya amsa cewa ya aikata laifin.

Amma sai mawakin ya dauki dan sandan zuwa wani guri, ya yi barazanar lakada masa duka da kuma jefa shi a kogi.

“Da misalin karfe 3:00 na dare kafin wayewar garin ranar Juma’a dan sanda ya tsayar da mawakin a kan titi, sakamakon ganin motar da yake tukawa ba ta da lamba,” inji sakon.

Ya ci gaba da cewa, “Da farko Ice Prince ya nuna masa ya yarda ya yi laifi su je ofishin ’yan sanda domin warware matsalar.

“To sai dai bayan jami’in ya hau motar tasa, sai ya wuce da shi wani wajen daban, inda ya yi barazanar lakada masa kuda da kuma jefa shi a kogi”, in ji Hundeyin.

Benjamin ya ce runudnar ta kamo mawakin a yau, bisa zarginsa da aikata wadannan laifukan, kuma za ta gurfanar da shi a gaban kuliya.