ICPC na binciken shugaban KAROTA kan zargin zamba

Jami’an KAROTA sun kai karar shi ICPC kan zargin ba da rasidan bogi.

ICPC na binciken shugaban KAROTA kan zargin zamba

Jami’an Hukumar Kula da Zirga-Zirgar Ababen Hawa ta Jihar Kano (KAROTA) sun kai karar Manajan Daraktan hukumar, Baffa Babba Dan’agundi, ga Hukumar Yaki da Rashawa ta Kasa (ICPC) kan zargin shi da zamba.

Tuni ICPC ta fara bincikar Manajan Daraktan na KARORA kan zargin da jami’an suke masa na bayar da rasidin bogi ga mutanen da hukumar ta ci tara.

A takardar korafin, jami’a hukumar na zargin tun a shekarar 2019 da shugaban ya fara aiki ya ba wa ofisoshin shiyya na hukumar damar su rika bayar da rasidin bogi ga mutanen da aka ci tara.

Suna kuma zargin shi da hannu wajen bayar da jabun rasidai ga wadanda aka ci tara a hedikwatar hukumar, sabanin sahihan rasidan da kotunan tafi-da-gidanka ke bayarwa ta hannun jami’an Hukumar Tara Haraji ta Jihar Kano (KIRS).

Takardar zargin ta ce Baffa Dan’agundi yana yin wannan kazamar harkar ce ta hannun wani dan uwansa, wanda ba ma’aikacin Gwamnatin Jihar Kano ba ne.

Kwamishinan Hukumar ICPC Shiyyar Jihar Kano, Ibrahim Garba Kagara, ya tabbatar wa Aminiya da samun takardar korafi kan Manajan Daraktan na KAROTA.

Sai dai ya ki yin karin bayani saboda a cewarsa, ana kan gudanar da bincike a game da lamarin.

Kokarinmu na jin ta bankin wanda ake zargin bai kai ga nasara ba, har zuwa lokacin kammala hada wannan labari.

Da wakilinmu ya nemi jin ta bakinsa, sai ya bukaci wakilin manu ya tura masa tambayoyin ta hanyar rubutaccen sako.

Amma har zuwa lokacin da muka kammala hada wannan rahoto bai amsa tambayoyin ba.