ICPC ta hana El-Rufai samun magani da abinci —Iyalinsa
Likitan El-Rufai ya je hedikwatar ICPC domin tattaunawa da shi kan sakamakon gwaje-gwajen da aka yi masa, amma jami’an hukumar sun hana shi ganin tsohon gwamnan
Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai
Iyalan tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, sun zargi Hukumar Yaki da Rashawa ta ICPC da hana shi samun kulawar likita da abinci yayin da yake tsare.
Sun bayyana cewa duk da umarnin kotu da ya ba shi damar ganin likitansa ba tare da takura ba, har yanzu ICPC na ci gaba da kawo tarnaƙi.
A cikin wata sanarwa da iyalan suka fitar a ranar Alhamis, sun bayyana matakin a matsayin tauye masa ’yancin da kundin tsarin mulki ya ba shi.
Sanarwar ta bayyana cewa likitan El-Rufai ya je hedikwatar ICPC da misalin karfe 3 na rana a ranar Juma’a 15 ga Mayu domin tattaunawa da shi kan sakamakon gwaje-gwajen da aka yi masa. Amma jami’an hukumar sun hana shi ganin tsohon gwamnan, bisa hujjar cewa sai an kawo rubutaccen izinin yin hakan daga shugaban ICPC.
Iyalan sun bayyana wannan mataki a matsayin karya umarnin kotu da kuma take haƙƙin ɗan Adam.
Sanarwar ta ƙara da cewa matarsa, Hajiya Aichatou, ma an hana ta kai masa abincin dare da ta kawo da misalin karfe 7 na yamma, inda aka shaida mata cewa hukumar ba ta karɓar abinci bayan karfe 6:30 na yamma bisa wani umarni na cikin gida.
Iyalan El-Rufai sun yi Allah-wadai da wannan mataki, da cewa babu wata doka da ta halatta a hana kulawar likita ko kuma a taƙaita abinci bisa wasu ƙa’idoji marasa tushe.
“Ba za mu kara yarda da wannan tsarin tsoratarwa da aka lullube da sunan ƙa’idar aiki ba. Dole ne ICPC ta bi dokokin da take iƙirarin tana aiwatarwa,” in ji sanarwar.
Iyalan sun ce, har yanzu suna ci gaba da ƙoƙarin tabbatar da cewa El-Rufai ya samu abincinsa.
Tun da farko matar El-Rufai ta wallafa wani bidiyo daga harabar ICPC inda ta bayyana irin wahalar da ta sha.
Wannan lamari ya biyo bayan kira da tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya yi na a saki El-Rufai cikin gaggawa.