ICPC ta kulle asusun Novomed kan badaƙalar magunguna a Kano

Hukumar ta ce za ta bincike yadda aka bai wa Novomed kwangilar samar da magunguna a jihar.

ICPC ta kulle asusun Novomed kan badaƙalar magunguna a Kano

Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (ICPC), ta kulle asusun bankin kamfanin Novomed Pharmaceuticals saboda binciken da ake yi kan badaƙalar magunguna a Jihar Kano.

Ana binciken wata kwangila da Ma’aikatar Harkokin Ƙananan Hukumomi da Masarautu ta Jihar Kano, ta bayar ga kamfanin don samar da magunguna ga ƙananan hukumomin jihar 38.

Ana zargin cewa an karya dokokin saye da sayarwa na gwamnati wajen bayar da kwangilar.

Wata majiya daga ICPC, wadda ta nemi a sakaya sunanta, taa bayyana cewa matakin da hukumar ta ɗauka na da nufin hana zurarewar kuɗaɗen da aka samu ta hanyar wannan kwangila mai cike da ayar tambayoyi.

Kamfanin Novomed Pharmaceuticals, wanda mallakin Garba Kwankwaso ne, kuma ɗan uwa ga jagoran jam’iyyar NNPP na ƙasa, Rabi’u Kwankwaso.

Wannan dai na zuwa ne bayan da Dan Bello, mai barkwanci a shafukan sada zumunta ya bankaɗo yadda aka bayar da kwangilar ga ɗan uwa ga jagoran Kwankwasiyya, ba bisa ƙa’ida ba.

ICPC, tana binciken ko an yi kuskuren bi dokoki wajen bayar da kwangilar.

Hukumar ta jaddada cewa dole ne duk kwangilolin da gwamnati za ta bayar su bi dokokin ƙasar, ba tare da la’akari da dangantakar siyasa ba.

Binciken, ya biyo bayan kama mutane biyar, ciki har da Alhaji Mohammed Kabara, Sakataren Ma’aikatar Harkokin Ƙananan Hukumomi da Masarautu, da kuma Garba Kwankwaso.

Ana zarginsu da hannu a yin zambar biliyoyin Naira wajen samar da magunguna ga ƙananan hukumomi 38 a jihar.

Ana zargin waɗanda aka kama da haɗa baki don ba da kwangilar ga Novomed, tare da karya dokokin saye da sayarwa, da karɓar kuɗaɗe don samar da magunguna.

Jami’in Hulɗa da Jama’a na hukumar, Kabiru Kabiru, ya tabbatar da kamen, kuma ya ce hukumar na gudanar da bincike.

Ya tabbatar da cewa hukumar za ta gano yadda aka bayar da kwangilar da kurakuren da aka yi, kuma za ta tabbatar da cewa waɗanda ke da alhaki a lamarin sun fuskanci hukunci.