ICPC ta shiga binciken badaƙalar sayar da guraben aiki
Ana zargin mambobin kwamitin da tatsar kuɗi daga shugabannin ma’aikatu.
Hukumar Yaƙi da Almundahanr Kuɗaɗe ta Najeriya ICPC ta fara bincike kan zarge-zargen cin hanci da ake yi wa Kwamitin Majalisar Wakilai mai bincike kan badaƙalar sayar da guraben aiki a ma’aikatu da hukumomin Gwamnatin Tarayya.
Kamar yadda BBC ya ruwaito, mai magana da yawun hukumar ta ICPC, Azuka Ogugua ce ta bayyana haka cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Juma’a a Abuja.
- Cire Tallafi: An yi wa ma’aikatan Gombe karin albashi
- Barayin da suka cinna wa Kasuwar Gombe wuta sun shiga hannu
Ogugua ta ce ICPC ta karɓi ƙorafe-ƙorafe daga jaridar Premium Times da ake wallafawa a intanet da kuma shugaban kwamitin wucin gadi na Majalisar Wakilan mai binciken badaƙalar sayar da guraben aiki, Hon. Yusuf Adamu Gadgi, inda suka buƙaci hukumar ta binciki zarge-zargen da ake yi wa kwamitin.
Jaridar Premium Time ta wallafa wani labari da a ciki ta zargi wasu mambobin kwamitin da neman shugabannin wasu jami’o’i da na manyan makarantu, su zuba kuɗi a wani asusun banki da sunan cin hanci.
Labarin ya yi iƙirarin cewa kwamitin na ɗaga ƙafa ga duk makarantar da ta biya kuɗaɗen da ’yan kwamitin suka nema.
An kuma zargin mambobin kwamitin da tatsar kuɗi daga shugabannin ma’aikatu da hukumomin gwamnati, ciki har da manyan makarantu.
A ranar Alhamis ne, Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito Yusuf Gadgi na cewa kwamitin ya rubuta wa hukumar ICPC wasiƙa yana neman ta gudanar da bincike kan zarge-zargen cin hanci da ake yi wa mambobin kwamitin nasa.
Shugaban kwamitin ya ce sun rubuta wa hukumar tare da buƙatar ta binciki asusun bankin da aka ce shugabannin makarantun na tura kuɗaɗen cin hancin.