ICPC ta tsare El-Rufai bayan EFCC ta ba da belinsa
A cikin daren ranar Laraba jami’an ICPC suka tsare El-Rufai bayan da Hukumar EFCC ta ba da belinsa bayan ta tsare shi tun ranar Litinin kan zargin badaƙalar Naira biliyan 432 a lokacin mulkinsa.
Nasir El-Rufai, Gwamnan Jihar Kaduna
Hukumar Yaƙi da cin hanci da rashawa (ICPC) ta tsare tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, jim kaɗan bayan Hukumar EFCC ta sako shi.
A cikin daren ranar Laraba jami’an ICPC suka tsare El-Rufai bayan da Hukumar EFCC mai yaƙi da masu karya tattalin arzikin ƙasa ta ba da belinsa bayan ta tsare shi tun ranar Litinin kan zargin badaƙalar Naira biliyan 432 a lokacin mulkinsa.
Wata gajeruwar sanarwa da Jami’in Hulda da Jama’a na Hukumar ICPC, J. Okor Odey, ya fitar ta ce, “Hukumar ICPC tana sanar da cewa tsohon Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai yana hannunta zuwa lokacin da aka tashi aiki yau yau (Juya), Laraba 18 ga watan Fabrairu, 2026, saboda wani bincike.”
Kawo yanzu dai babu cikakken bayani game da ainihin zargin da ICPC take neman yi wa tsohon gwamnan tambayoyi a kai.
Wasu majiyoyi a EFCC sun bayyana cewa fitowar El-Rufai ke da wuya bayan cika sharuddan belin da EFCC ta ba shi, wasu jami’an na daban suka kama shi tare da yin awon gaba da shi.
Hakan na zuwa ne bayan a ranar Juma’a El-Rufai ya bayyana cewa zai gabatar da kansa a EFCC domin amsa tambayoyi daga nan ya wuce ICPC, domin nan ma ya amsa wasu tambayoyi.
Ya bayyana cewa bayan dawowarsa Najeriya ICPC ta aike masa takardar gayyata bayan yunƙurinta na amfani da Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) wajen kama shi a filin jirgin bai yi nasara ba.
Sai dai bayan zuwansa EFCC, hukumar ta riƙe shi har zuwa ranar Talata da dare da ta bayar da belinsa, inda bayan nan kuma ya faɗa hannun jami’an ICPC.
Dambarwar El-Rufai da Gwamnati
El-Rufai ya kasance a labarai tun bayan dawowarsa daga ƙasar waje, inda jami’an tsaro suka yi yunƙurin kama shi a filin jirgin sama na Abuja, inda suka ƙwace fasfo ɗinsa na ɗan taƙaitaccen lokaci.
Bayan turjiyarsa da boren jama’a ta hana jami’an tafiya da shi, daga bisani ya sanar a yayin hirarsa da gidan talabijin na Arise cewa Hukumar ICPC ce ta yi yinƙurin kama shi ta hanyar amfani da Hukumar DSS.
A yayin hirar, El-Rufai ya yi zargin Mashawarcin Shugaban Ƙasa, Nuhu Ribaɗu da bayar da umarnin kama shi, inda a ya yi iƙirarin samun bayanai daga wani wanda ya naɗi wayar Ribaɗu lokacin da yake bayar da umarnin kama shi.
Sai dai zargin nasa ya haifar da ce-ce-ku-ce inda, aka bayyana iƙirarin nasu a matsayin katoɓara da kuma daɓa wa kansa wuƙa.
Daga bisani Gwamnatin Tarayya ta hannun Hukumar DSS ta maka shi a kotu bisa zargin hannu barazanar tsaron ƙasa, rashin kai rahoto ga hukumomin da suka dace bayan samun masaniyar kan naɗar wayar Mashawarcin Shugaban Ƙasa kan Sha’anin Tsaro ba bisa ka’ida ba.
Bayan hirar El-Rufai da Arise ya fitar da wata takarda da ya aike wa Ribaɗu yana mai zargin Mashawarcin Shugaban Ƙasan da yin odar sinadarin gubar Thallium Sulphate mai haɗarin daga ƙasar waje.
Daga baya Ofishin ya aike masa da martani da ke ƙaryata zargin yin odar gubar Thallium Sulphate ko niyyar yin hakan.
Takardar ta kuma bayyana cewa za ta gudanar da bincike kan lamarin domin samun bayanan da suka dace daga El-Rufai da kuma shugabannin adawa da ya yi iƙirarin cewa ya sanar da su game da lamarin.
A halin da ake ciki dai ana ganin bayan ICPC ta gama yi masa tambayoyi game da zarge-zargen da take masa, zai fuskanci shari’ar zargin naɗar wayar Ribaɗu a gaban kotu, da kuma wani bincike na daban kan dambarwar shigo da gubar Thallium Sulphate.
Tun da farko wasu majiyoyi a DSS sun bayyana cewa hukumar DSS ta sake buɗe bincike kan ɓacewar wani matashin malamin jami’a, Abubakar Idris, wanda aka fi sani da Dadiyata, wanda wasu masu ɗauke da makamai suka sace da bakin bindiga a gidansa a Kaduna a zamanin El-Rufai.
A yayin hirar da BBC ta yi da tsohon gwamnan ne aka yi masa tambaya kan ɓacewar Dadiyata, mai yawan sukan Gwamnatinsa, amma ya amsa da cewa bai san da Dadiyata ba sai bayan ɓacewarsa.
A cewarsa, Dadiyata ya kasance mai yawan sukar gwamnatin Jihar Kano ta lokacin, ƙarƙashin tsohon Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, don haka gwamnatin Kano ya kamata a tambaya kan ɓacewar matashin.
Sai dai tsohuwar gwamnatin Kano ta Ganduje ta mayar martani da ƙaryata zargin, a yayin da ’yan adawar El-Rufai ke bayyana cewa sanannen abu ne yadda Dadiyata ke sukan gwamnatinsa kuma a Kaduna aka sace shi.
Ana zargin dambarwar El-Rufai tsantsar siyasa ce da ke da alaƙa da raba garinsa da Gwamnatin Jam’iyyar APC ta Shugaba Bola Ahmed Tinubu wadda tun ba a je ko’ina ba ta ki ba wa El-Rufai muƙamin minista.
Tsohon gwamnan, wanda ya sauya sheƙa daga APC zuwa jam’iyyar ADC ya kasance kakkausan mai sukan gwamnatin Tinubu, yana mai cewa za su yi duk mai yiwuwa domin ƙwace mulki daga Tinubu a zaɓen shekarar 2027 da ke ƙara matsowa.
A yayin hirarsa da Arise ya bayyana cewa ko da Gwamnatin Tinubu ta nada shi muƙamin minista, da ba zai daɗe ba zai bar gwamnatin.