ICPC ta tsare manyan jami’an NAHCON a ofis kan badakalar N90bn

Hukumar ICPC ta kamo jami’an Hukumar NAHCON a ofisoshinsu bisa zargin karkatar Naira biliyan 90 da Gwamnatin tarayya ta fitar don tallafa wa maniyyata da cikon kudin kujerar Hajjin 2024.

ICPC ta tsare manyan jami’an NAHCON a ofis kan badakalar N90bn

ICPC

Hukumar yaƙi da rashawa da dangoginsa (ICPC) ta tsare wasu manyan jami’an Hukumar Aikin Hajji ta Ƙasa (NAHCON) bisa zargin karkatar Naira biliyan 90 na cikon kuɗin kujerar aikin Hajji da Gwamnatin Tarayya  ta fitar don tallafa wa maniyyatan Hajjin 2024.

An damƙe jami’an ne a ofisoshinsu da ke NAHCON bayan sun ƙi amsa gayyatar da hukumar ICPC ta yi musu a baya.

Wata majiya a ICPC ta ce hukumar ta yi wa jami’an da ake zargi tambayoyi na tsawon sa’o’i kan badaƙalar tallafin N90bn ga maniyyata.

Majiyar ta ce, “A ranar Laraba wasu jami’anmu suka je ofishin hukumar NAHCON don kamo wasu jami’ai zuwa  ofishinmu.

“Da farko mun gayyaci waɗannan jami’an, amma ba su zo ba.

“Da aka kawo su, an yi musu tambayoyi a ci gaba da binciken da muke gudanarwa bayan ƙorafe-ƙorafe da aka shigar a kansu dangane da tallafin da aka bai wa maniyyata.”

A ranar Lahadi, kakakin hukumar ICPC, Demola Bakare, ya tabbatar da cewa an kawo manyan jami’an NAHCON ofishin hukumar domin amsa tambayoyi.

Amma ya bayyana cewa tuni aka sallame su bayan sun cika sharuɗɗan belinsu.

Demola Bakare, ya tabbatar da cewa, “Manyan jami’an NAHCON ne, amma banda shugaban hukumar a cikinsu. Ana ci gaba da bincike kan lamarin.”

Kamen ya zo ne kwanaki kaɗan bayan ICIP ta yi wa shugaban hukumar NAHCON, Jalal Arabi, tambayoyi kan zargin karkatar da N90bn na kuɗaɗen tallafin Hajji na 2024.

Bayan ƙorafin da gwamnan Neja, Mohammed Bago ya yi, majalisar dokoki ta kasa ta ƙaddamar da bincike kan hukumar NAHCON bisa zargin karkatar da kuɗaɗen tallafin aikin Hajjin.

Amma da yake jawabi a wani taron manema labarai bayan aikin Hajji a Abuja a ranar 29 ga watan Yuli, Arabi ya dage cewa an yi amfani da kuɗaɗen ne a bayyane, inda ya yi watsi da zarge-zargen almundahana.

A cewarsa, “An tallafa wa kowane maniyyacin jiha da N1,637,369.87 daga N90bn a karkashin shirin tallafin aikin Hajji.

“Don haka, aka bukaci su biya cikon Naira 1,918,094.87 tunda N90bn da Gwamnatin Tarayya ta bayar na tallafi bai isa cika gibin da aka samu ba.”

Tags