Idan aka sace jagororin APC biyu jam’iyyar ta mutu – Sule Lamido

Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Sule Lamido ya tayar da wata kura a fagen siyasa lokacin da ya fito fili ya ce idan aka sace biyu daga cikin jagororin Jam’iyyar APC, shi ke nan jam’iyyar ta mutu kwata-kwata. Gwamna Sule Lamido ya bayyana haka ne a ranar Talata a Legas lokacin da yake jawabi a wurin […]

Idan aka sace jagororin APC biyu jam’iyyar ta mutu – Sule Lamido
Idan aka sace jagororin APC biyu jam’iyyar ta mutu – Sule Lamido

Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Sule Lamido ya tayar da wata kura a fagen siyasa lokacin da ya fito fili ya ce idan aka sace biyu daga cikin jagororin Jam’iyyar APC, shi ke nan jam’iyyar ta mutu kwata-kwata.

Gwamna Sule Lamido ya bayyana haka ne a ranar Talata a Legas lokacin da yake jawabi a wurin taron gwamnonin PDP.
Duk da dai Gwamna Lamido bai bayyana su wane ne yake nufi da jagororin jam’iyyar biyu ba, masu fashin baki suna ganin yana nufin tsohon Gwamnan Jihar Legas Bola Tinubu da dan takarar Shugaban kasa a karkashin Jam’iyyar APC Janar Muhammadu Buhari yake nufi.
A baya gwamna Lamido ya rika bayyana cewa mutanen biyu su ne kashin bayan jam’iyyar da idan suka fice daga cikinta ba za ta kai labari ba.
Sai dai a wani martani da Jam’iyyar APC ta maida ta ce ba za ta dauki maganar da Gwamna Lamido ya yi da wasa ba. A cewarta hakan na nuna cewa wani shiri ne da PDP take yi, na sace jagororin jam’iyyar amma bisa tsautsaye sa Gwamna Sule Lamido ya bayyana shi ga jama’a, don haka ta bukaci hukumomin tsaro su sanya ido don kula da shugabanninta, kuma duk abin da ya faru da su, ba kowa za su zarga ba, sai Lamido da Jam’iyyar PDP.
Kakakin Kwamitin Yakin neman Zaben Shugaban kasa na Jam’iyyar APC, Malam Garba Shehu ya ce an ruwaito Gwamna Sule Lamido ya bayyana wadannan kalamai ne a Legas kuma an nuna shi yana fadin haka kai-tsaye ta akwatunan talabijin.
Jam’ Janar Buhari ya ‘fusata’ inda ya bukaci Gwamnan ya daina furta irin wadannan kalamai ga shugabannin APC da sunan siyasa.
Janar Muhammadu Buhari ya ce yana fata Lamido yana fadin hakan da wasa ne.
Malam Garba Shehu wanda ya kira taron manema labarai a Abuja a ranar Talata ya ce, sace jama’a kamar lamarin Boko Haram batu ne da bai kamata a yi wasa da shi ba.
“Ina gani abin tashin hankali ne a ce gwamna ya tashi a gaban akwatin talabijin yana cewa idan ana son karya Jam’iyyar APC, abin da kawai suke bukatar yi shi ne su sace shugabannin APC biyu, sai jam’iyyar ta karye. Wannan na nuna kamar mutanen ba su san cewa ’yan Najeriya suna da martaba da mutunci da za a girmama ba, idan ba haka ba za su tashi gatsau su tunzura jama’ar kasar nan ba.”
Ya kara da cewa: “Mu a Kwamitin Yakin Zaben Shugaban kasa na APC, satar mutane babbar barazana ce ga kasar nan, kuma ba lamari ne da mutane za su rika ba’a da shi ba tamkar dai Boko Haram. Kuma ga dan takarar Shugaban kasarmu Janar Muhammadu Buhari, manyan batutuwa su ne tsaron rayuka da dukiyar al’ummar kasar nan kamar yadda za ku gani a jawabansa daban-daban, wannan lamari ne da ya yi niyyar bayar da dukkan rayuwarsa a kai.”