Idan aka samu gwamnati mai adalci za a samu zaman lafiya a Filato – Farfesa Emmanuel Garba
Farfesa Emmanuel Garba na daya daga cikin maso son tsayawa takarar Gwamnan Jihar Filato a karkashinJam’iyyar APC. Farfesan wanda ya fito daga karamar Hukumar kuan Pan, malami ne a Jami’ar Jos, a tattaunawarsada wakilinmu ya ce idan aka samu gwamnati mai adalci a jihar za a samu lafiya, kuma ya bayyana abin da ya karfafa […]
Farfesa Emmanuel Garba na daya daga cikin maso son tsayawa takarar Gwamnan Jihar Filato a karkashin
Jam’iyyar APC. Farfesan wanda ya fito daga karamar Hukumar kuan Pan, malami ne a Jami’ar Jos, a tattaunawarsada wakilinmu ya ce idan aka samu gwamnati mai adalci a jihar za a samu lafiya, kuma ya bayyana abin da ya karfafa masa gwiwar shiga harkokin siyasa da fitowa neman takarar Gwamnan Jihar:
Aminiya: Mene ne ya karfafa maka gwiwar fitowa takarar Gwamnan Jihar Filato a karkashin Jam’iyyar APC?
Farfesa Garba: Babban abin da ya karfafa mani gwiwar shiga siyasa shi ne damuwa kan abubuwan da suke faruwa a Jihar Filato. Domin a gaskiya yawancinmu ba mu ji dadin irin abubuwan da suke faruwa a jihar nan ba, musamman kan rashin zaman lafiya. Domin mun yi imanin idan babu zaman lafiya, babu yadda za a yi a samu a samu ci gaba. Kuma muna ganin babban abin da ya kawo rashin zaman lafiya a Jihar Filato, shi ne rashin gwamnati mai kyau. Matukar ba a samu gwamnati wadda ta iya tafiyar da mutane bisa gaskiya da adalci ba, dole ne a samu rashin zaman lafiya. Amma idan aka samu gwamnati mai gaskiya da adalci mai tafiya da kowa da kowa to za a samu zaman lafiya da ci gaba. A lokacin da muka taso muna yara, ba mu san ana fadan addini ba. Domin ko a cikin gidajenmu akwai addinan nan guda biyu wato Kiristanci da Musulunci. Don haka a lokacin da muka taso babu ruwanmu da rikicin addini. Amma a yanzu saboda rashin adalci an jawo rikicin addini, wanda ya kawo tashin hankali a jihar nan. Mu a ganinmu idan da adalci da gaskiya za a samu zaman lafiya. Don haka na shigo siyasa kuma na fito takarar kujerar Gwamnan Jihar Filato ne, don na ba da gudunmawata wajen ganin an samu zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar.
Bayan haka game da maganar ilimi babu shakka ilimi ya samu koma baya sosai a Jihar Filato, domin a da an san Jihar Filato da ilimi amma a yanzu ilimi a jihar ya samu koma baya. Jihohin Arewa da dama sun wuce jihar nan a ci gaban harkokin ilimi. Ina ganin wannan matsala ta faru ne saboda ba a ba harkokin ilimi muhimmanci ba.
Don haka idan Allah Ya kai mu ga nasara, babban abin da zan fi mayar da hankali a kai shi ne bunkasa harkokin ilimi. Domin idan babu ilimi babu abin da za a iya yi. Komai ya dogara ne kan ilimi. Don haka zan tabbatar na karfafa harkokin ilimi a jihar nan. Misali nan da shekara 5 masu zuwa yawaicin ma’aikatan Gwamnatin Tarayya za su fito ne daga Jihar Kano. Saboda yadda gwamnatin jihar ta bai wa harkokin ilimi muhimmanci a halin yanzu. Musamman ta hanyar mutanen da tura dalibai karatu zuwa kasashen waje a fannonin da ba mu da su a kasar nan. Don haka ni ma idan na samu nasara abin da zan yi ke nan a jihar nan.
Aminiya: Ganin irin rikice-rikicen da aka samu a jihar nan, ka samu nasara wadanne hanyoyi ne za ka bi, ka sake hada kan al’ummarta?
Farfesa Garba: Kamar yadda na fada rashin zaman lafiyar da aka samu a nan Filato, ya taso ne saboda rashin adalci. Idan aka kafa gwamnati ba tare da an yi gaskiya da tafiya da kowa ba, dole ne ba za a samu zaman lafiya ba. Don haka idan muka samu nasara zan tafi da kowa.
Aminiya: Jihar ta samu koma baya a harkokin kasuwanci sakamakon rikice-rikicen, yay aka shirya tunkarar wannan lamari?
Farfesa Garba: Babu shakka matsalar nan ta rashin zaman lafiya a jihar nan, ta shafi harkokin kasuwanci. Domin duk inda babu zaman lafiya, babu wanda zai zo daga waje ya zuba jarinsa. Idan muka samu nasara za mu bi hanyoyin jawo mutane daga waje don su zo su zuba jari. A wani bincike da aka yi a kwanakin baya kan masu zuba jari a jihohin Arewa, ya nuna cewa babu Jihar Filato a cikin jihohin da masu zuwa daga waje suka zuba jari. Abin da ya sa masu zuba jari ba sa zuwa Jihar Filato a yanzu shi ne suna ganin har yanzu babu zaman lafiya a jihar. Don haka mu tsara hanyoyin bunkasa harkokin kasuwanci masu inganci, kuma za mu bunkasa harkokin yawon bude ido, don mu rika samun masu zuwa yawon bude idanu a jihar nan. Bayan haka za mu bunkasa harkokin noma, musamman noman dankalin Turawa, muna da yanayi mai kyau a jihar nan. A Najeriya babu inda ake samun dankalin turawa kamar Jihar Filato, don haka za mu bunkasa harkokin noma, ta hanyar tallafa wa manoma da samar masu da ingantatun irin shuka da taki da magungunan feshi da sauransu.
Aminiya: Ganin rikicin da jam’iyyarku ta APC ke fama da shi a jihar nan ba ka ganin wannan zai iya kawo muku matsala?
Farfesa Garba: Idan ka dubi wannan rikici da ke cikin Jam’iyyar APC a jihar nan, za ka ga cewa ba wani rikici ne mai tsanani ba. Babu shakka idan aka zauna za a warware wannan rikici.
Aminiya: Wane sako kake da shi zuwa ga al’ummar Jihar Filato?
Farfesa Garba: Sakona ga al’ummar Jihar Filato shi ne su yi watsi da rudin da ake yi musu cewa Jam’iyyar APC, jam’iyya ce ta Musulmi. Wannan ba gaskiya ba ne, a cikin dukkan jam’iyyun da muke da su a Najeriya babu jam’iyyar da ba ta dan mabiya addinan da muke da su a kasar nan. A Jam’iyyar PDP akwai Musulmi akwai Kirista haka a Jam’iyyar APC akwai Musulmi akwai Kirista, don haka babu maganar addini a cikin jam’iyyun da muke da su a Najeriya. Bayan haka ina kira ga al’ummar Jihar Filato idan sun tashi yin zabe su zabi ‘yan takarar da suka cancanta, domin a samu a ceto jihar da Najeriya baki daya daga mawuyacin halin da muke shiga.