Idan aka yi sahihin zaben fidda-gwani ni zan samu nasarar rike wa PDP tuta a Sakkwato – Yusuf Suleiman

Alhaji Yusuf Suleiman tsohon Ministan Sufuri na daga cikin wadanda suke son tsayawa takarar Gwamnan Jihar Sakkwato a Jam’iyyar PDP. Ya bayyana wa Aminiya dalilansa na fitowa takara da dangantakarsa da tsohon Gwamnan Jihar Alhaji Attahiru Bafarawa da Mataimakin Gwamnan Jihar Alhaji Mukhtari Shagari da shi ma yake son kujerar: Aminiya: Ga shi ka dawo […]

Idan aka yi sahihin zaben fidda-gwani ni zan samu nasarar rike wa PDP tuta a Sakkwato – Yusuf Suleiman
Idan aka yi sahihin zaben fidda-gwani ni zan samu nasarar rike wa PDP tuta a Sakkwato – Yusuf Suleiman

Alhaji Yusuf Suleiman tsohon Ministan Sufuri na daga cikin wadanda suke son tsayawa takarar Gwamnan Jihar Sakkwato a Jam’iyyar PDP. Ya bayyana wa Aminiya dalilansa na fitowa takara da dangantakarsa da tsohon Gwamnan Jihar Alhaji Attahiru Bafarawa da Mataimakin Gwamnan Jihar Alhaji Mukhtari Shagari da shi ma yake son kujerar:

Aminiya: Ga shi ka dawo da fom din tsayawa takararka na Gwamnan Jihar Sakkwato ga uwar Jam’iyyar PDP ta kasa, mene ne dalilin da ya sa ka fito takarar?
Yusuf Suleiman: Babban dalilin da ya sa na fito takarar Gwamnan Jihar Sakkwato shi ne don in inganta rayuwar al’ummar jihar. Zan fara da bangaren ilimi, domin duk al’ummar da take neman ci gaba sai ta ba ilimi muhimmanci. Zan fara da ilimin yara, inda zan kafa ginshikin da za su amfani al’umma. Daga nan in mayar da hankali wajen horar da malamai, domin a masu ingancin ilimi a bayar da ilimi mai inganci.
A bangaren tattalin arziki, kowace kasa tana da wani abin da take tinkaho da shi wajen bunkasa tattalin arzikinta, don haka Jihar Sakkwato tana da ma’adanai masu yawa, na yi aiki a karkashin gwamnatin jiha har zuwa matakin darakta a Ma’aikatar Bunkasa Masana’antu tsawon shekara 10, wannan ya ba ni damar sanin masana’antu ta bangaren noma da kere-kere da kanana da manyan masana’antu da za a kafa a kananan hukumomin jihar 23. Ina da masaniya kan masana’antar da ta fi dacewa da kowace karamar hukumaa bangaren noma ko ma’adanai. Idan ka ambaci kowace karamar hukuma a Jihar Sakkwato zan iya fada maka amfanin gonar da ake nomawa da ma’adanan da za a samu a cikinta. Wadannan su ne dalilan da suka sanya na fito takara, saboda ina so in mayar da jihar nan sabuwar duniya, na kuma samar da tattalin arziki mai dorewa.
Aminiya: Akwai ayyukan da Gwamantin Wamakko take yi, kamar taimaka wa nakasassu da biyan malamai da limamai albashi da biyan matasa da ake kira ’yan sandan Alu albashi. Idan ka samu nasara za ka ci gaba da yin su?
Yusuf Suleiman: Kowace gwamnati tana da tsare-tsaren ayyukan da ta sa a gaba, idan ka zama Gwamna, abin da za ka fara shi ne ka zabi alkiblar da gwamnatinka za ta fuskanta ta bangaren ayyuka, za ka zabi bangaren da suka shafi tattalin arziki ne ko kuma abin da ya shafi rayuwar jama’a. Idan ka zabi bangaren tattalin arziki kamar yadda na zaba, maimakon ka rika ba nakasassu da malamai albashin Naira dubu biyar ko dubu 10 duk wata, zan samar da shirin noma ne, misali a samu hekta 1000 a kananan hukumomi 23 na jihar nan, sannan in samar da kayan aikin gona na zamani, in samu matasa 1,000, in ba kowanensu hekta 1, sannan in sa ido don ganin yadda za su yi noma har sau biyu ko uku a shekara, idan aka yi haka, za a samu kudin shiga akalla Naira miliyanuku a kowace hekta a shekara. Maimakon in rika ba su kifi, sai in koya musu yadda za su kama kifin.
Aminiya: Ka ce ka san ma’adanan da suke kananan hukumomin jihar 23?
Yusuf Suleiman: A farkon jawabina na ce na san ma’adanan da suke jibge a Jihar Sakkwato, yawancin ma’adanan da ke jihar nan sun hada da ‘gypsum’ da ‘limestone’ da ‘phosphate’ da ‘iron ore’ da ‘copper’ da kuma ‘kaolin’. Za ka samu ma’adanan ‘limestone’ da ‘gypsum’ a yankin Kogin Rima; akwai ‘limestone’ a Kalambaina zuwa dundaye. A da a nan Kamfanin Siminti na Arewacin Najeriya yake. Zan samar da kamfanin siminti a nan. Ni ne makasudin hakar ‘gypsum’ a Dange-Shuni a lokacin da nake darakta a ma’aikatar masana’antu ta jihar. Zan mayar da hankali wajen yin takin zamani, tunda muna da ma’adanin ‘phosphate’, sannan idan ka je karamar Hukumar Kebbi akwai ma’adanin ‘copper’ mafi inganci a duniya, don haka zan hada gwiwa da kamfanonin da suke sarrafa ‘copper’ don bunkasa tattalin arzikin jihar.
Aminiya: Kwanakin bayan shugaban Kwamitin Amintattu na PDP Cif Tony Anenih ya kawo ziyara Jihar Sakkwato don magance rikicin da ka iya biyo bayan zaben fidda-gwani da za a yi, me kuka tattauna?
Yusuf Suleiman: Bari in yi bayani a kan jita-jitar da ake yadawa tun bayan da Cif Anenih ya zo Sakkwato. Anenih mutum ne mai kima ba a idon ’yan PDP ba har da ’yan jam’iyyun adawa a Najeriya. Ya zo Sakkwato mun tattauna yadda Jam’iyyar PDP za ta samu nasara a zaben 2015 a jihar ne, ba ya zo don ya zaba mana dan takara kamar yadda ake ta yadawa a gari ba. Mun tattauna yadda za a samu hadin kai a jam’iyyarmu, mun tattauna yadda za a kwato jiharmu daga Jam’iyyar APC, saboda a zaben baya jama’a PDP suka zaba ba wata jam’iyya ba, za mu yi nasara ne idan muka hada kai.
Aminiya: Ana cewa tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato Attahiru Bafarawa yana dari-dari da kai a jam’iyyar, hakan ya sa magoya bayansa suke fadi-tashi don ganin ba ka samu nasara ba, me za ka ce a kan hakan?
Yusuf Suleiman: Wannan duk jita-jita ce, ba su da tushe balle makama. Bafarawa dan uwana ne. Ni kadai ne a cikin masu neman Gwamna da na fito daga karamar hukuma daya da shi. Ina da alaka mai karfi tsakanina da shi tun kafin mu fara siyasa, tun kafin a kafa Jam’iyyar PDP. Na san ba za ka raba mutane da maganganu ba, hakan ba abin mamaki ba ne. A matsayin Bafarawa na tsohon Gwamna ya samu magoya bayan da za su rika maganganu, amma abin nake so a sani shi ne, ba ya yin wata takara, don haka ban ga dalilin da za a ce yana dari-dari da ni ba. A yanzu idan ka je Sakkwato ka tambayi mutane yaya ake ganina za su ce maka Yusuf Suleiman yana da farin jini, za a kuma fafata da shi. Idan na samu nasarar tsayawa takara a PDP babu abin da zai hana in zama Gwamna in sha Allah.
Aminiya: Wani dan takara a Jihar Sakkwato na cewa tikitin tsayawa takarar nasa ne, domin sakatariyar Jam’iyyar PDP ta kasa ta dankwafe shi aka ba Aliyu Wamakko tikitin a shekarar 2007, inda aka yi masa alkawarin idan Wamakko ya gama za a ba shi, shin har yanzu wannan batu yana nan?
Yusuf Suleiman: Mutumin da yake wannan maganar dan uwana ne, ba na so mu rika sa-in-sa da shi, idan haka yake cewa ba zan ce kada ya ce haka ba, saboda ra’ayinsa ke nan, ba kuma ra’ayin jama’a ba ne. A yanzu a PDP babu abin da yake gabanmu kamar mu ci zabe, ya kamata mu zauna mu tsara abubuwan da jama’a za su yarda da su har zu zabe mu a zaben 2015.
Aminiya: Wasu suna cewa tunda kai dan sarauta ne bai kamata ka shiga siyasa ba?
Yusuf Suleiman: Sunana Yusuf Suleiman, dan Jihar Sakkwato, rayuwata da siyasata da alakata da jama’a ba su taba kimar kasancewata dan gidan sarauta ba, sannan ba wai don kasancewata dan sarauta sai ya kasance na fi sauran ’yan takara hudu samun dama ba, na san cewa fitowata daga gidan sarauta za ta taimake ni a bangaren gidan sarauta ne kawai, amma a fahimtata na taso cikin yi wa jama’a hidima. Sarkin Musulmi kuma uba ne ga ’yan siyasa da ma wadanda ba ’yan siyasa ba.
Aminiya: Idan aka yi zaben fidda-gwani a jam’iyyarku wani ya samu nasara, za ka mara masa?
Yusuf Suleiman: Ni fa dan siyasa ne cikakke, ina kuma biyayya ga dokokin dimokuradiyya. Na fito takara ne saboda ina da yakinin zan samu nasara, na tabbata idan aka yi sahihin zaben fidda-gwani zan samu nasara, idan Allah Ya sa bayan an yi sahihin zaben fidda-gwani ban samu nasara ba, zan goya wa duk wanda ya yi nasara 100 bisa 100. Ina so a gane mu a nan Sakkwato dukkanmu daya ne a PDP, muna da dangantaka da alakar da ta wuce ta siyasa kawai, na tabbata idan na yi nasara sauran wadanda muka fafata da su za su goya mini baya, haka idan wani ya samu nasara ba zan jira ya kira ni ba, ni zan same shi don mu tsara yadda PDP za ta samu nasara.