Idan aka zabi Buhari zai magance tashin hankali a Najeriya – Lalong
sdan takarar Gwamnan Jihar Filato a karkashin Jam’iyyar APC, Mista Simon Lalong ya ce idan al’ummar Najeriya suka zabi Janar Muhammadu Buhari a matsayin Shugaban kasa a zaben ranar 28 ga Maris, zai kawo karshen tashin hankal a Najeriya. Mista Simon Lalong ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi ga dubban magoya bayansa […]
sdan takarar Gwamnan Jihar Filato a karkashin Jam’iyyar APC, Mista Simon Lalong ya ce idan al’ummar Najeriya suka zabi Janar Muhammadu Buhari a matsayin Shugaban kasa a zaben ranar 28 ga Maris, zai kawo karshen tashin hankal a Najeriya.
Mista Simon Lalong ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi ga dubban magoya bayansa a garin Jos, a ci gaba da yakin neman zaben da yake a Jihar Filato.
Ya ce, “Janar Buhari ne kadai zai iya kawo mana adalci da zaman lafiya da ci gaba a Najeriya. Babu ruwan Buhari da maganar bambancin addini kamar yadda wasu suke fada, don haka za mu zabe shi a matsayin Shugaban Najeriya a wannan zabe mai zuwa,” inji shi.
Ya ce komai kokarin Gwamna a jiharsa idan aka sake zaben Jonathan za a ci gaba da samun rashin zaman lafiya a Najeriya, domin komai ya gagare shi a kasar nan.
Mista Simon Lalong ya yi bayanin cewa mun san Gwamna Jang ya nuna kabilanci a lokacin mulkinsa a jihar nan, kuma ya ci kudin jihar nan.
Ya ce, “Muna yi masa addu’a Allah Ya juyo da zuciyarsa ya samu ya biya albashin ma’aikata da malaman makarantun firamare da suke bi a jihar wata da watanni kafin ya bar gwamnati. Kuma duk da basussukan da Jang yake so ya bari a Jihar Filato, ba na tsoron na zama Gwamnan Jihar nan. Domin mun san idan Allah Ya sa aka zabi Buhari a matsayin Shugaban kasa zai share mana hawaye,” inji shi.
Tunda farko a jawabin Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Filato Mista Latep Dabang ya cewa tunda aka hada Jam’iyyar APC a Jihar Filato ba su taba jin wani dan jam’iyyar ya bar jam’iyya ya koma wata ba.
Ya ce, “Amma mu a kullum muna samun daruruwan magoya bayan Jam’iyyar PDP da suke dawowa Jam’iyyarmu ta APC. Don haka ina kira ga dukkan al’ummar jihar nan kan su fito kwansu da kwarkwatarsu su zabi Jam’iyyar APC a dukkan matakai domin a samu a fita daga cikin mawuyacin halin da ake ciki a Najeriya.”