Idan Amurka ta kawar da Al-Assad ba za a kare muradunta ba -Dempsey
Janar Martin Dempsey, Mai bai wa Shugaban Amurka Shawara kan harkokin soja, ya bayyana dalilin da ya sanya Gwamnatin Amurka ta ki kawar da shugaba Bashar al-Assad, domin Amurka ba za ta fa’idantu ba. Don babu bangaren masu adawa da al-Assad da zai kare muradunta.A cikin wasikar da ya rubuta wa dan majalisar wakilai Eliot […]

Janar Martin Dempsey, Mai bai wa Shugaban Amurka Shawara kan harkokin soja, ya bayyana dalilin da ya sanya Gwamnatin Amurka ta ki kawar da shugaba Bashar al-Assad, domin Amurka ba za ta fa’idantu ba. Don babu bangaren masu adawa da al-Assad da zai kare muradunta.
A cikin wasikar da ya rubuta wa dan majalisar wakilai Eliot Engel, wadda Kamfanin Dillancin Labarai na AP ya samu, Janar Dempsey ba za ta kai dauki ba, ko na makami ko sojojin kasa.
“Halin da ake ciki a Siriya babu wani zabi a tsakanin bangarori. Matukar za mu goyi bayan wani bangare, dole ya yi shirin kare manufarmu, inda ragama ta koma hannunsu. Sai dai a yau babu wanan zabin a cikinsu,” kamar yadda yake kunshe a wasikarsa ta ranar 19 ga Agustan bana.
Wannan shugaba na sojojin Amurka bai gamsar da masu adawa da gwamnatin Siriya ba, haka su ma jami’an gwamnatyin Obama, wadanda suka zaku da son ganin an kai wa ’ya tawaye dauki, don kawo karshen mulkin shekara 40 na iyalan Al-Assad, ba su ji dadin yadda yake tafiyar da al’amuransa ba.