Idan an ciza, sai a busa
Allah Mahaliccin kowa, Maikomai ya yi mana alkawarin cewa, idan matsi ya yi matsi, sauki na tafe nan take. Babu shakka bayinSa da yawa sun yi imani da haka, suna kuma ganin sauki a dukkan lokutan da suka fada cikin wata bakar ukuba ko matsananciyar wuyar da ke hana su more gardin rayuwa. Duk da […]
Allah Mahaliccin kowa, Maikomai ya yi mana alkawarin cewa, idan matsi ya yi matsi, sauki na tafe nan take. Babu shakka bayinSa da yawa sun yi imani da haka, suna kuma ganin sauki a dukkan lokutan da suka fada cikin wata bakar ukuba ko matsananciyar wuyar da ke hana su more gardin rayuwa. Duk da cewa, a wannan marrar jama’a na cikin wani halin ha’ula’i amma duk da haka nan sun mayar da al’amuransu ga Ubangiji, suna ta fatan samun saukin da ya yi alkawarin samar musu. A halin da ake ciki na matsin rayuwa da karancin abin duniya, za a ga kamilallen magidanci, wanda ya san abin da yake yi, ya kuma san inda kansa ke masa ciwo, yana tafe, yana sambatu, yana ta jujjuya hannu, domin abin duniya ya dame shi. Akwai mutane da yawa da ke yin haka ba a cikin hayyacinsu ba, ba su kuma san lokacin da wasu kalamun ke kubucewa daga bakunansu ba, domin kuwa abin da ya dame su babba ne kwarai, ya isa ya sa kowa dimaucewa da fadawa cikin tsananin damuwa. Dalili kuwa, shi ne, sukan wayi gari gidajensu babu abinci, sa’annan kuma sun fito nema. Wasu babu abin da suka bari a gidajensu daga ruwa sai gishiri, babu abin dafawa, ko tukawa, babu kuma sauran kayayyakin kada miyar hadawa. Sun yi ta jigilar nema, har la’asar sakaliya ba su samu na cefane ba, ga rana kuma ta kusa faduwa, ba su da ikon maido da ita tsakiyar samaniya, su ci gaba da bida kafin komawarsu gida a ci hakuri.
To amma duk da haka nan talaka bai fitar da rai daga rahamar Ubangijinsa ba, da kuma irin taimako ko agajin da zai iya samu daga shugabannin da ke fafutika, ba dare, ba rana don kyautata masa. Sa’ilin da mutane da yawa ke imani game da haka, wasu kuwa gani suke kamar wuyar da suke sha ba za ta wuce ba, za ta dore ne har abada, saboda tsabar gajen hakuri. To, ai ita wuya mawuyaciya ce! Suna ina aka yi ta yankayi cikin tsananin ukuba da wahalhalun da gwamnatocin jam’iyyar PDP suka wanzar cikin shekaru goma sha shida? Me suka yi? Ai hakurewa suka yi, har sai da Allah Ya yi ikonsa, ya wancakalar da su. Ita dai wannan gwamnatin Ta Muhammadu Buhari gyara take kan yi, kuma an ce mai gyara ba ya barna, sai dai idan ba gyaran yake yi ba. Kowa ya san cewa da zafi ake maganin zafi, kuma da ciwo ake cire ciwo.
Sanin kowa ne Shugaba Buhari shi kadai ba zai iya gudanar da dimbin ayyukan gwamnati da ke gabansa ba, tilas sai da taimakon ministoci da manya da kananan jami’an gwamnati da kuma daukacin jama’ar Najeriya. Shi ya sa tun farkon nada shi yake taka-tsan-tsan wajen zaben abokan aiki don gudun kar ya yi zaben tumun dare, ko kuma ya rufe kofa da barawo. Sai bayan da ya yi watanni uku tukuna, sa’annan ne ya fitar da ministocin da ya tabbata ba su da wani tabo, za su kuma iya daukar nauyin da aka dora musu, domin kuwa a da can sun yi, an gani, an kuma yaba da kwazo da kuma ingancinsu.
To idan akwai wani, ko wasu, wadanda ke ganin wadancan ministocin ba su cancanci kasancewa bisa kujerunsu ba, watakila ana iya yi musu uzuri don ganin irin matsalolin da suka taso, suke kuma addabar jama’a, musaman na rashin wutar lantarki da man fetur da kuma kanfan kudi. Babu shakka Farfesa Ango Abdullahi da Dokta Junaidu Muhammad ba jahilai ne ba, suna sane da al’amuran da suka taso har aka kai ga haka, kuma su ma masu taimakawa ne ta kowane fanni don a magance cikin sauki. A yanzu dai babu abin da ministoci ko manyan jami’an gwamnati za su iya aiwatarwa ba tare da kudi ba, su kuma kudin can an tsara su ne cikin kasafin kudin da bai samu amincewar Majalisar kasa ba, kafin a fara firfitar da kudin, ana shimfida ayyuka da su, ana kuma karkashewa, har kowa da kowa ya samu rabonsa na halaliya daga ciki.
Idan rashi, ko matsin da ake fama da shi a yanzu ya samo asali ne daga wadancan yanayin, to ana iya cewa babu abin da Ministoci za su iya yi a halin yanzu, domin wanda ke sama ma bai ci ba, balle ya jejjefo wa na kasa. Bai kamata masu korafi game da Ministoci, ko furucin da suke yi cewa, Gwamnatin Buhari ba ta tabuka komai ba a halin yanzu, sai su jira bayan shekaru 16 tukuna kafin su fadI haka kamar yadda wacce ta gada ta yi, jama’a kuma ba su gamsu da kamun ludayinta ba.
Amma sai dai babu laifi, a tsaya a saurari korafe-korafen Farfesa Ango da kuma Dokta Junaid, kada a yi saurin katse musu hanzari, ta hanyar watsi da batunsu, domin su ba ’yan adawa ne ba, suna daga cikin wadanda aka yi dawainiyar kafa jam’iyyar APC da su, da kuma wadanda suka hada karfinsu da karafansu wajen bayar da gudummawar da ta kafa gwamnatin Buhari. Dimokuradiyya ce ake yi, kuma ita ce ta bayar da dama har suka furta haka, a matsayin shawarar da Bahaushe ke cewa “gyara kayanka,” watakila ba so suke yi a sauke ne a raba da su ba. Abin da suke so, shi ne, a yi gyara, ko a inganta al’amura ta yanyar karbar shawarwarin da ake ba gwamnati, domin an ce mai karbar shawara aikinsa bai baci.
Furucin Dokta Junaid na cewa, akwai wasu bara-gurbi a Gwamnatin Shugaba Buhari a bar dubawa ce, sa’annan kuma wasu daga cikin wadancan ministocin nadinsu ya tayar da kura a jihohi da yawa, kamar su Kaduna da Kano da Gombe da dai sauransu, don a magance rigingimun da suka haddasa bakar gaba tsakanin jiga-jigan ’ya’yan jam’iyyar APC a wurare da yawa. Yin haka zai kashe bakin tsanya, musamman ma ’yan adawar da ke da’awar muzguna musu su kadai, ana ta amfani da hukumar EFCC ana kakkame su, ana barin na jam’iyya mai gwamnati domin su ’ya’yan mowa ne. Ya kamata dai idan ana cizawa, a rika busawa.
Abin da babba fa ya hango, yaro ko ya hau dutsen kufena ne, ya fado, ba zai gani ba. Saboda haka nan sai a yi hattara, a duba batutuwan su Farfesa Ango da Dokta Junaidu Muhammad domin kuwa komai nisan jifa, kasa za ta fado. To sai mu yi fata kada ta fado mana a kai a lokacin.