Idan ba ka yi ba ni wuri

A ranar 14 ga watan  Afrilu ne bamabaman da aka tarwatsa da sanyin safiya  a tashar motar Nyanya a birnin tarayyar Abuja suka yi sanadidiyyar asarar rayuka 75, har yanzu kuma babu amo ko labarin wadanda suka haddasa wanan ta’asar, duk kuwa da cewa Shugaba Jonathan ya hakikance cewa ‘yan Boko Haram ne suka tafka […]

Idan ba ka yi ba ni wuri
Idan ba ka yi ba ni wuri

A ranar 14 ga watan  Afrilu ne bamabaman da aka tarwatsa da sanyin safiya  a tashar motar Nyanya a birnin tarayyar Abuja suka yi sanadidiyyar asarar rayuka 75, har yanzu kuma babu amo ko labarin wadanda suka haddasa wanan ta’asar, duk kuwa da cewa Shugaba Jonathan ya hakikance cewa ‘yan Boko Haram ne suka tafka aika-aikar, sa’anan aka ce kungiyar Boko Haram din da kanta ta sanar cewa da hannunta a cikin ta’asar. A kashe-garin wannan ranar ce kuma  aka wayi gari da labari mara dadin ji game da sace dalibai 234 daga Kwalejin ‘yan mata da ke garin Chibok a Kudancin Jihar Barno, kuma har ya zuwa yau babu labarinsu, sun bace bat kamar ido a tsakar ka.
Haka nan kuma bayan kwanaki biyu da afkuwar masifar Abuja sai aka samu labarin cewa wasu daliban wata babbar makaranta a kasar Korita ta Kudu sama da 500 sun tagayyara a wani hatsarin kwale-kwale kuma guda 174 ne suka tsira, sauran kuma aka ce sun halaka.  Wadannan jaza’o’i ne da suka afkawa Najeriya da takwarar ta nahiyar Asiya, watau Koriya ta Kudu, kuma sun addabi iyayen yaran makarantun da kuma gwamnatocinsu da ma daukacin jama’ar  kasashen biyu. A dukkan lokutan da irin wadannan masifun suka faru  a Najeriya jama’a za su yi ta hargowa, ‘yan jaridu su yi ta hayagaga, ‘yan siyasa kuma su yi ta nuna yatsan zargi ga shugabannin  gwamnati, amma irin haka bai sa  shugabannin da hakkin kare rayukan jama’a da dukiyoyinsu  ke wuyansu bazama wajen hukunta mai hannu cikin matsalar da ta tayar da zaune tsaye, ba kuma za su dauki matakan kiyaye gaba ba.
Kururuwar iyayen yara bai kidima su, salwantar dimbin  rayuka bai damunsu, asarar da aka yi ta dukiya ba ta dada su da kasa, jimamin  mawuyacin halin da jama’a ke shiga sakamakon sakacin jami’an gwamnati abu ne da suka jahilta, ba su kuma yin jaje ko ta’aziyya ga wadanda  aka kwara ko  wadanda suka yi rashin ‘ya’ya da ‘yanuwa.  Shi ya sa wadanda ke aikata ta’asar da ke haddsa jidali ke bacewa kamar iskar da ba mai iya kama ta, masu jejjefa bama-bamai kuma ke ta cin karensu ba babbaka, ba wanda ya isa ya hana, makasa da barayin bil-adama na sheke ayarsu yadda suka ga dama, kuma ba wanda aka kama.
To ko da aka wafce ‘yan matan makarantar Chibok sama da 234, gwamnati da jami’anta da kuma askarawanta ba su iya gano inda suke ba, domin da ma can abin bai dame su ba, ga shi nan kuma an yi sama da mako biyu ba wanda ya damu. To idan da ‘ya’yan manyan jami’an gwamnati ne ko kuma zuriyar manyan hafsoshin askarawar kasar nan ne aka jefa cikin wannan matsalar za a dauki dogon lokaci kamar haka kafin a kubutar da su daga hannun wadanda  ke cutar da su?
 Rahotannin da ba a tabbatar ba na cewa an yi jigilar wadancan ‘yan matan ne zuwa kasashen makwabta, a Jamhuriyoyin Kamaru da kuma Chadi, aka kuma daddaura masu aure akan sadaki Naira 2,000 da aka biya wadanda suka sace su a matsayin waliyyansu. Anya kuwa za a yi haka ba tare da sanin hukumomin wadancan kasashen ba? Wannan ba batar da sawu ne ba ga masu neman inda aka boye ‘yan matan?  Kuma ai ko ba komai Najeriya na da jakadu a wadancan kasashen, kuma ya kamata a ce sun samu wannan labarin, sun kuma bincika, sun sanar da gwamnatin Najeriya halin da ake ciki. To idan har sun aiko da rahotanni dangane da wannan matsalar me gwamnatin tarayya ta yi game da haka?  Idan kuma har sun aiko, shugabannin Najeriya ba su dauki wani mataki ba, to da wane dalili za su ci gaba da darewa bisa madafun iko?
Amma a kasar Koriya ta Kudu, inda aka san ya kamata, ake mutunta rayukan bayin Allah, ake kuma tausaya wadanda suka yi rashin rai ko asarar dukiya, shugabanni ba su nokewa, ko su yi kunnen uwar shegu da kururuwar da jama’an dake cikin wata matsala. Firayim Ministar kasar Koriya, Chung-Hong-won ya sauka daga mukaminsa  don ya nuna damusarsa game da yadda ake ta tsattsagarsa saboda hatsarin kwale-kwalen da ya janyo hasarar rayukan daliban kasar. Wannan jirgin dai ba nasa ba ne, ba kuma shi ne ke tukawa ba, ba kuma shi ne Ministan sufurin kasar ba balle a ce ya wajaba a gare shi ya ajiye mukamin nasa. Ya yi haka ne domin shi ne ke rike da sitiyarin gwamnatin kasar, kuma idan har  ya kasa kai ta gaci, to ba shi da sauran amfani. Tun da kuwa gwamnatinsa ta kasa kiyaye rayukan daruruwan dalibai daga salwanta, tilas ne a zarge shi. Ya kuma amince da haka, ya nemi gafarar jama’ar kasar, ya kuma kauce wasu kuma su gwada.
To wannan babban darasi ne ga shugabannin Najeriya, wadanda suka kasa aiki da ka’idojin kundin tsarin mulki don kare rayuka da dukiyoyin talakawansu. To idan har sun nuna rashin iyawa sai su kauce, su ba wasu wuri, tun da dai abin ba gadon gidansu ne ba.