Idan babu tsarin sufuri na zamani tattalin arziki zai tawaya – NSC
Shugaban Hukumar Sufurin Jiragen Ruwa ta Najeriya (NSC), Barista Hassan Bello ya bayyana sashen sufuri a matsayin turakun da suke juya tattalin arzikin Najeriya. Shugaban na Hukumar NSC ya kara da cewa muddin gwamnati ta gaza samar da ingantattun hanyoyi da zamanantar da sufuri, tattalin arzikinta zai gamu da tawaya sosai. Bello ya ce ba […]
Shugaban Hukumar Sufurin Jiragen Ruwa ta Najeriya (NSC), Barista Hassan Bello ya bayyana sashen sufuri a matsayin turakun da suke juya tattalin arzikin Najeriya.
Shugaban na Hukumar NSC ya kara da cewa muddin gwamnati ta gaza samar da ingantattun hanyoyi da zamanantar da sufuri, tattalin arzikinta zai gamu da tawaya sosai.
Bello ya ce ba ma tattalin arzikin zai samu koma baya ne kawai, za a kai matsayin da zai tsaya cik ne. “Sashen sufuri da Kuma kakkafa tasoshin sauke kaya na tudu za su kawo sabon sauyi ga tattalin arzikinmu. Fitar da kayayyaki zuwa waje shi ma sufuri ne, kamar yadda lamarin yake a fannin sufurin jirgin kasa. Wuraren sauke kaya da muke kokarin kafawa za su kawo sauyi kuma mun yi kyakkyawan shiri a kan haka,” inji shi.
Da yake magana kan kudirin dokar Hukumar Sufuri ta kasa da ke gaban Majalisar Dokoki ta kasa, ya ce, “Ana sa ran cewa sabuwar hukumar za ta kasance mai sanya ido da tabbatar da bin ka’ida wajen gudanar da sashen sufuri na kasar nan. “Tsarin tattalin arziki na zamani ne. Ba za ka zamo mai sanya ido, sannan kuma mai yin wannan harka ba a lokaci guda. Sai dai ka zama daya daga ciki. Kuma a yanzu kudurin ya samu amincewar Majalisar Wakilai tare da na sufurin jiragen kasa da na tasoshin ruwa da kuma tsibirai. Abin da za su yi shi ne su ceto wadannan sassa daga babakeren jama’a,” inji shi.
Bello ya kara da cewa, “Muna da cikakken yakini cewa sassa masu zaman kansu za su shiga a dama da su, tare da ba su damar taka rawa wajen bunkasa tattalin arziki. Kuma duk da muna fatan samun sassa masu zaman kansu su kasance na kwarai, akwai bangaren kula da doka da sashen sufurin ke gudanarwa. Kuma idan aka kafa hukumar za ta karbi aikin tabbatar da bin ka’idojin daga daga Hukumar Tashohin Jiragen Ruwa. Kuma hanyoyin mota da na jiragen kasa da tasoshin ruwa, kila ma a gaba har da jiragen sama, za su kasance a karkashin kular wannan hukuma. Wannan abin maraba ne ga ci gaban Najeriya.”