Idan baki ya ci…
Yanzu dai an tabbatar da cewa zababbun shugabanni da ‘yan majalisun tarayya da na jihohin ne matsalar kasar nan, ko kuma a ce tarnakin da ke tauye ci gabanta, kuma a sakamakon haka ne harkokin dimokuradiyya ke tsumburewa, tattalin arziki na shiga mawuyacin hali, rashin zaman lumana da kwanciyar hankali na kara kamari. Kamata ya […]
Yanzu dai an tabbatar da cewa zababbun shugabanni da ‘yan majalisun tarayya da na jihohin ne matsalar kasar nan, ko kuma a ce tarnakin da ke tauye ci gabanta, kuma a sakamakon haka ne harkokin dimokuradiyya ke tsumburewa, tattalin arziki na shiga mawuyacin hali, rashin zaman lumana da kwanciyar hankali na kara kamari. Kamata ya yi a ce ‘yan majalisa ne ginshikan tattalaban ayyukan ciyar da Najeriya gaba, amma kash! Sai ga shi nan sun kasance dundurusun rusa kasa, wadanda ba su damuwa da jama’ansu sai kawunansu da ‘ya’yansu da kuma kokarin samun abin da za su jefa a aljiffansu walau na halas ko na haram.
Wannan al’amari ba haka nan yake ba a Jamhuriya ta farko, inda ‘yan majalisu suka san ciwon kansu, suke kuma kokarin kyautatawa don su samu daman sake komowa idan lokaci a sake zagayowa. Dalili kuwa shi ne zababbun shugabannin da ke gudanar da al’amuran gwamnati sun san mutuncin ‘yan majalisa, suna ba su hakkinsu, suna kuma taka-tsantsan don kada su saba masu don gudun sakamakon da zai biyo baya. To amma tun daga wancan lokacin al’amuran suka canja, gwamnatocin da sojoji suka kakkafa ba ruwansu da ‘yan majalisar, balle su nemi shawarar da za ta taimaka masu don kyautata ayyukansu.
Haka nan kuma babu ruwan sojojin da aiki da kundin tsarin mulki da jama’a suka taru suna tsara don inganta matakan iko, hasali ma da shi ne suke fara fatali bayan sun habarar da zababbiyar gwamnatin farar hula. A madadin majalisar da za ta dinga yin dokoki da yawun jama’a sojojin ne za su bullo da na su dokokin kama karya da suke kira dikiri, kuma yadda suka tsara haka nan za su aiwatar, ba wani mahalukin da ya isa ya kalubalance su. Haka nan aka yi ta tafiya a zamanin mulkin soja, babu wakilan jama’a da za su yi dokokin gudanar da gwamnati, kuma duk sauran gwamnatocin mulkin soja haka nan suka yi ta mulki, ‘yan siyasa na bayan fage. Daga karshe sai yadda sojoji suka ga dama za su dama, su ba kowa, kuma tilas ya kurba haka nan, ba dama ya furzar saboda da daci ko baurin damun?
To shi ne tun daga lokacin da sojoji suka fara gwada bayar da mulki ga farar hula a shekarar 1979, bayan sun dandana har tsawon shekaru goma sha uku, da kuma lokacin da suka sake mayar da shi bayan sun yi wasu shekaru ashirin suna sharholiya, sai zababbun shugabannin siyasa, musamman ma shugaban kasa da gwamnonin jihohi suka fara gwada dabi’u irin na mulkin soja, domin kuwa giyar mulkin sojojin ba ta saki kasar ba. Irin wadannan shugabannin sun dauka daidai suke da gwamnoni ko shugaban kasa irin na soja, saboda haka nan sai suka yi ta kakkarya dokokin da ke kunshe cikin kundin tsarin mulkin da suka yi rantsuwa da shi; kuma da zaran sun fara aiki sai su saye ‘yan majalisu, su jejjefa su cikin aljiffansu ta yadda ba za su iya yin wasu dokokin da za su saba ra’ayoyinsu ba, ko su kuma tursasa masu don aiwatar da abin da ba su yi niyya ba, ko tilasta masu daukan hanyar kyautatawa jama’arsu alhali kuwa ba su da ra’ayin haka. Dangane da haka ne ake ta bin tafarkin dimokuradiyya a karkace, ana mulkin kama-karya irin na soji wadanda ba ruwansu da kundin mulki ko dokokin majalisa.
A yanzu wannan al’amari ya kazanta, domin kuwa gwamnoni da shugaban kasa sun mayar da majalisunmu tamkar kyanwar Lami, wacce ba ta cizo, ba ta kuma yakushi, sai dai a shafa ta kawai, ba kuma za ta iya yin gurnani ba idan ta hango abin da zai cutar da ita, ko wanda zai halaka maigidanta. A yanzu ‘yan majalisun kasar nan ba su da wani amfani ga jama’an da ake cewa suna wakilta, muhimmin abin da ke gabansu shi ne kyautatawa gwamna ko shugaban kasa wadanda suka yi ruwa suka yi tsaki wajen tafka magudin da ya kai su bisa kujerun majalisun. Shi ya sa wadanan shugabanni ke sheke ayarsu yadda suka ga dama, suke kuma karkata akalar majalisar don samun biyan bukatun masu munanan bukatunsu ta bayan gida wadanda suke janyo wa kasar da talakawan cikinta fitintinu da masifu daban-daban.
Idan da Shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya dauki ‘yan majalisun tarayya da muhimmanci ai da ba zai kafa wata haramtacciyar majalisa ba, ya kuma nemi ta yi aiki irin na waccan din da ya kauce wa don tsara wasu manufofin da ba su da fa’ida ga hadin kan kasar da harkokin tattalin arzikinta da zamantakewa. Daga bisani bisani wadancan manufofin ne za a mika wa ‘yan majalisar tarayya don nemar amincewarsu, kuma haka nan za su mika kai bori ya hau, su amince ba tare da wata kwakkwarar muhawara ba. Irin abin da Jonathan ke son ya faru ke nan da sakamakon babban taron kasa, wanda jama’a suka nuna rashin amincewarsu da shi. To amma ko an ki, ko an so, daga bisani dole ‘yan majalisar tarayya da na jihohin da ke cikin aljiffan gwamnoni su amince, domin kuwa idan baki ya ci tilas ido ya ci kunya. Sun rigaya sun ci ladan kuturu, dole ne su yi masa aski.