‘Idan gwamnati ta inganta magungunan gargajiya za ta samu karin kudin shiga’
Wani mai magungunan gargajiya da ke Jos a Jihar Filato Dokta Muhammad Muhammad Makeri, ya ce idan Gwamnatin Tarayya ta rike tare da inganta magungunan gargajiya ta hanyar gina asibitocin magunguna gargajiya a sassan kasar nan, za ta rika samun kudin shiga masu yawa.Dokta Muhammad Makeri ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa […]

Wani mai magungunan gargajiya da ke Jos a Jihar Filato Dokta Muhammad Muhammad Makeri, ya ce idan Gwamnatin Tarayya ta rike tare da inganta magungunan gargajiya ta hanyar gina asibitocin magunguna gargajiya a sassan kasar nan, za ta rika samun kudin shiga masu yawa.
Dokta Muhammad Makeri ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu a Jos, inda ya ce babu itacen da za a yi magani da ba mu da shi a kasar nan, kuma a duk duniya babu kasar da take da masu magungunan gargajiya kamar Najeriya.
Ya ce idan gwamnati ta inganta magungunan gargajiya, kasashen duniya za su rika zuwa suna amfani da magungunan gargajiyar.
Ya ce magungunan gargajiya suna taimakawa wajen kiwon lafiyar al’umma domin suna warkar da wasu cututtuka baki daya sabanin magungunan Turawa.
Dokta Makeri ya koka kan yadda gwamnatin ba ta damu da magungunan gargajiya da masu su ba, “Wannan babban abin takaici ne idan aka yi la’akari da irin gudunmawar da masu magungunan gargajiya ke bayarwa ga kiwon lafiya.
Ya ce ya kamata Najeriya ta yi koyi da kasashen China da Indiya wajen tallafa wa harkokin magungunan gargajiya, yayin da ya yi kira ga masu magungunan gargajiya su rike harkar cikin amana su guji cutar masu zuwa jinya wurinsu.