Idan kura na maganin zawo…

Bahaushe kan danganta dan fari da wauta, watau aikata abubuwan da ba su dace da tsari ko yanayin rayuwa ba, kuma hakan bai sa mai irin wannan dabi’ar ya fahimci haka har ya gane cewa abin da ya aikata wawanci ne. A nan Najeriya an yi rashin sa’a, an samu shugaban da ya kasance tamkar […]

Idan kura na maganin zawo…
Idan kura na maganin zawo…

Bahaushe kan danganta dan fari da wauta, watau aikata abubuwan da ba su dace da tsari ko yanayin rayuwa ba, kuma hakan bai sa mai irin wannan dabi’ar ya fahimci haka har ya gane cewa abin da ya aikata wawanci ne. A nan Najeriya an yi rashin sa’a, an samu shugaban da ya kasance tamkar dolo ko wani sauna, wanda ke gudanar da al’amuransa cike da gabanci, ko kuma a ce susanci, domin kuwa idan ya tafka wata ta’asar sai a dade ana ji masa kunyar bankaurar da ya aikata, amma shi kuwa ko gezau, domin ba zai ji a jikinsa ba. Kowa dai ya san yadda harkokin Shugaba Goodluck Ebele Jonathan ke wakana da kuma yadda al’amuran gwamnatinsa ke tafiya a hagunce, kuma a gurgunce, ba domin komai ba sai don lusarancinsa da rashin kamun kansa da kuma gaulancinsa. Wadanna ne ke haddasa rashin fahimtar yadda zai yi abin son barka, wanda za a yi ta kwanzartawa, ana yaba masa, sai dai tafka tabargazar da za ka ji ko ina ana tsaki, ana ta cewa assha, domin abin da ya aikata ba shi da wani kan-gado, ya kuma saba wa tunani da hankalin jama’ar da suka san inda kawunansu ke yi masu ciwo.

Shi ya sa a dukkan lokutan da Shugaba Jonathan ya yi aikata wata kasassaba babu wani mai mamaki, domin an san zai aikata, saboda ya taba yin wacce ta fi haka. Idan ba domin sakaci da rashin sanin ya kamatansa ba, ta yaya za a ce kasarsa na cikin mummunar bala’in rashin zaman lafiya sakamakon tabarbarewar harkokin tsaro na tsawon lokaci da ya janyo hasarar dubban rayukan bayin Allah, da gudun hijiran talakawa zuwa kasashen makwabta don guje wa bala’o’in da hakan suka haddasa, amma shi da gwamnatinsa ba su dauki kwararan matakan kawo karshensu ba akan kari, aka bari suka yi ta tabarbarewa, har suka buwayi kowa da kowa?
Hakan ya sanya jama’ar kasar nan cikin mummunar damuwa, amma babu abin da ya dada Jonathan da kasa; an yi awon gaba da ‘yan matan makarantar babbar sakandaren garin Chibok sama da 219, ya ki zuwa ya jajanta wa iyayensu; an jejjefa bama-bamai a garuruwa da yawa fiye da shurin masaki, sun kuma karkashe daruruwan mutane, amma hakan bai dame shi ba, bai kuma yi wa iyaye da ‘yan uwan wadanda suka halaka gaisuwar rashin da suka yi ba; babu abin da ya yi don sakake matsalolin da suka karya kashin bayan yankin Arewacin kasar nan har hakan ya janyo mummunar karayar tattalin arziki da tabarbarewar harkokin kasuwanci,inda ya fi auki shi ne fifita wani addini bisa wani da kuma zuga-zugin wutar kabilanci da habaka bambancin bangaranci.
Hakika Shugaba Jonathan ya kasa magance matsalolin da rashawa da cin hanci ke haddasawa balle kuma ya hukunta manyan jami’an gwamnatinsa da ministocinsa da suka mayar da wadannan kaba’iran abin ado. Wadannan ne ummul-haba’isin haddasa rashin tsaron da ya kasa magancewa, kuma wannan matsalar ce za ta kai ka wargajewar gwamnatinsa a 2015, domin kuwa ga shi nan tun yanzu an fara ganin tana daddarewa; harkokinta na sukurkucewa; manyan jami’anta na kidemewa; shugabannin jam’iyyar da ta kafa wannan gwamnati suna gigicewa, ba abin da suka dukufa akai illa su tabatar sun bi mumanan hanyoyin sake kafa gwamnati, don ta haka ne za su rufa asirin baram-baramar da suka aikata, su kuma ji dadin ci gaba da daukar matakan daidaita wasu sassan kasar kamar yadda kasashen Yahudu da Nasara suka kitsa musu. Wannan ita ce akida da manufar da aka kafa Gwamnatin Shugaba Jonathan, wacce kasashen Turai da Amurka ke karkata akalarta, suna kuma koya mata saka da mugun zare.
Sanin kowa ne dai Turawa ne ke tsara yadda yanayin siyasar Najeriya da ma na wasu kasashen duniya masu tasowa ke kasancewa, su ne kuma ke nuna musu dabarar yin amfani da gurguwar dimokuradiyya, don dora jigari-jigarin shugabannin da za su yi ta karkatawa. Shi ya sa irin wadannan shugabannin kasashe masu tasowa ba su da katabus, dole su bi abin da Turawa suka tsara masu, domin kuwa su ne suka yi sanadiyyar hayewarsu karagar mulkin kasashensu.
Dangane da haka ne Turawa ke ta tarairayar Shugaba Jonatha, domin yana yi masu fiye da abubuwan da suka bukace shi da yi don amfaninsu, ba domin jama’ar kasarsa ba. Shi ma ya san da haka, shi ya sa yake ta zakewa wajen tozarta jama’ar kasarsa da kuma sayar da ‘yancinta ga wadanda ba su kaunarta. Dalili kuwa shi ne ya san sun rigaya sun tabbatar masa cewa ko ana-ha-maza-ha-mata ba za su bari ‘yan adawar kasarsa su ga bayansa ba. Dangane da haka ne suka ingiza shi kasar Burkina Faso, tare da wasu shugabannin kasashen Afrika,‘yan koren Turawa, don su tsara wani yanayin da zai share masu hanyar dora wani dan korensu bisa mulkin kasar bayan sun gama ayyana wanda suka ga ya fi dacewa da mulkin kasar daga cikin ‘yan barandarsu a waccan kasar. Da ma ta haka ne shugabanni irin su Jonathan ke rama wa kura aniyarta, ta hanyar bin manufar dankwafar da burin jama’a na danka wa gwarzonsu ragamar jan kasashensu.
To yanzu dai wautar Shugaba Jonathan ta fito fili, ya kuma yi baya ba zani, ya biye ra’ayin Turawan da suka kunna gagarumar wuta a kasarsa, suka kuma hana shi kashe ta, sa’anan suka ingiza shi kashe wata ‘yar karamar wutar da ta tashi a Burkina Faso, don kar ta lakume manufarsu ta tatse ta karkaf. To amma mai bunu a gindi bai gudummawar gobara. Wai shin idan kura na da maganin zawo to, ta yi wa kanta mana. Amma Shugaba Jonathan bai san haka ba. Kaico!