Idan malamai suka rike mutuncinsu za a magance matsalolin kasar nan – Sheikh Na’annabi

Wani malamin addinin Musulunci da ke Jos fadar Jihar Filato Sheikh Abdulkadir Mu’azu Umar wanda aka fi sani da Malam Na’annabi ya ce idan malaman kasar nan suka koma suka su tsaya kan matsayin da Allah Ya dora su na karantar da al’umma tare da bayar da kyakyawan misali na tsaron Allah, za a magance […]

Idan malamai suka rike mutuncinsu za a magance matsalolin kasar nan – Sheikh Na’annabi
Idan malamai suka rike mutuncinsu za a magance matsalolin kasar nan – Sheikh Na’annabi

Wani malamin addinin Musulunci da ke Jos fadar Jihar Filato Sheikh Abdulkadir Mu’azu Umar wanda aka fi sani da Malam Na’annabi ya ce idan malaman kasar nan suka koma suka su tsaya kan matsayin da Allah Ya dora su na karantar da al’umma tare da bayar da kyakyawan misali na tsaron Allah, za a magance matsalolin rashin tsaron da ake fuskanta a kasar nan.
Sheikh Abdulkadir Na’annabi wanda makaho ne ya bayyana haka ne a lokacin da yake rufe tafsirin da ya gabatar a Jos, a makon jiya inda ya ce malamai su ne shugabanni saboda hatta shugabannin kasa suna karkashinsu ne. Don haka idan shugabannin kasa suka yi kuskure babu wanda zai iya yi masu magana sai malamai.
Ya babbar matsalar da muke fama da ita a Najeriya, ita ce kowa na bukatar ya ga ya tara abin duniya. “Wannan ne ya jefa mu a halin da muke ciki, don haka ina kira ga al’ummar Najeriya mu koma ga Allah domin nemo mafita. Idan muka koma ga Allah muka rungumi addu’o’i, babu shakka za a samu mafita kan halin da muke ciki,” inji shi.