‘Idan mata suka samu ilimin zamani Najeriya za ta bunkasa’
Shugabar Makarantar Sabil Sunlight da ke GRA, Bauchi, Misis Mercy Agene John ta nuna damuwar kan yadda wasu iyaye suke dora wa ’ya’yansu talla dare da rana maimakon tura su makaranta a wannan lokaci da duniya ke tinkaho da mata masu ilimi.Misis Mercy John ta ce idan mace daya ta iya rubutu da karatu ba […]
Shugabar Makarantar Sabil Sunlight da ke GRA, Bauchi, Misis Mercy Agene John ta nuna damuwar kan yadda wasu iyaye suke dora wa ’ya’yansu talla dare da rana maimakon tura su makaranta a wannan lokaci da duniya ke tinkaho da mata masu ilimi.
Misis Mercy John ta ce idan mace daya ta iya rubutu da karatu ba ita kadai ce za ta amfana ba.
Misis Agene John ta bayyana haka ne lokacin da take zantawa da Aminiya a ofishinta da ke makarantar a ranar Larabar makon jiya.
Ta ce talauci na daya daga cikin abubuwan da suke haddasa ltabarbarewar ilimi a Najeriya domin akwai mutanen da suke son ’ya’yansu su samu ilimi amma ba su da kudin da za su sa su a makaranta. “Sakamakon haka sai iyaye mata suke dora musu tallar goro ko gyada ko shinkafa ko masa da sauransu. Ina ba da shawarwari ga al’umma baki daya koda za a dora wa yarinya talla don Allah a sa ta a makaranta domin binciken ya nuna sama da kashi 85 cikin 100 na maza ba sa kaunar zama da macen da ba ta iya karatu da rubutu ba,” inji ta.