‘Idan matata ta sha giya takan yi doguwar tafiya a kasa’
Wani magidanci mai suna Mojeed Mustafa da ke zaune a Ibadan ya ce idan matarsa mai suna Bose ta kwankwadi giya tana iya tafiya da kafa daga Ibadan zuwa Legas ba tare da ta damu ba. Ita kuma wata matar aure mai suna Yetunde cewa ta yi, mijinta mai suna Wande da ya saba kukan […]

Wani magidanci mai suna Mojeed Mustafa da ke zaune a Ibadan ya ce idan matarsa mai suna Bose ta kwankwadi giya tana iya tafiya da kafa daga Ibadan zuwa Legas ba tare da ta damu ba.
Ita kuma wata matar aure mai suna Yetunde cewa ta yi, mijinta mai suna Wande da ya saba kukan rashin kudi yana shan giya ce fiye da kima a kowace rana inda yake komawa gida yana amayar da giyar tare da yin fitsarin kwance a gado.
Bayanan haka sun fito ne daga bakin mutane lokacin da suka shigar da kara suna neman a raba aurensu a kotunan gargajiya na Ile-Tuntun da Oja Oba/Mapo duk a birnin Ibadan.
Da yake yi wa kotun Ile-Tuntun karin haske, Mojeed Mustafa ya ce matarsa Bose “Ta mayar da giya abincinta na safe da rana da dare kuma mafadaciya ce mai yawan fada da makwabta. Ta hana ni sakewa a gidanmu, sai abin kunya take haifarwa a kullum tsawon shekarun da muka yi. Wannan ne dalilin da ya sa nake rokon kotun ta raba aurenmu,” inji shi.
Da take kare kanta Bose, ta shaida wa kotun cewa “Gaskiya ce ina shan giya kwarai da gaske amma sauran bayanin da ya yi karya kawai yake fada. Duk da haka na amince a raba auren domin babu soyayya a tsakaninmu. Ba na sonsa kuma na amince a raba auren.”
Alkalin Kotun Cif Olasunkanmi Agbaje ya dage sauraron karar zuwa ranar 24 ga Satumban nan domin yanke hukunci.
kara ta biyu da Yetunde ke neman a raba aurensu da mijinta a Kotun Oja Oba/Mapo kuwa, an saurari bayanin da ta yi ne cewa, “Mijina Wande mashayin giya ne da zai iya shanye tulu daya ta barasa a rana amma ya kasa kula da daukar dawainiyar ’ya’yanmu 6 da muka haifa a tsawon shekara 25 da muka yi zaman aure tare. Ya saba yin kukan rashin kudi amma a kowane lokaci za ka same shi ya yi tatil da giya ya komo gida yana wari da amai da fitsarin kwance.” Sai ta roki kotun ta raba aurensu.
Duk da Wande ya amince da raba auren sai dai ya karyata matar a kan abubuwan da ta shaida wa kotun, inda ya ce karya take yi.
Bayan sauraron bangarorin biyu, Alkalin Kotun Cif Ademola Odunade ya yanke hukumcin raba auren tare da umartar Bose ta ci gaba da rike ’ya’yan a hannunta. Kuma kotun ta umarci Wande ya rika biyan wasu kudi ta hannun kotu da Yetunde za ta rika amfani da su wajen kula da dawainiyar yaran, musamman abinci da karatu da kula da lafiyarsu.