Idan na bayyana halin da Najeriya ke ciki ba mai sake barci – Janar Danjuma
Tsohon Ministan Tsaro, Laftana Janar Theophilus Yakubu Danjuma (mai ritaya), ya ce idan ya fadi abubuwan da suke faruwa a kasar nan, to ’yan Najeriya ba za su sake barci ba. Janar Danjuma ya bayyana haka ne lokacin da yake jawabi a wajen wani taron kaddamar da wani littafi mai taken shekara 70 da ci […]
Tsohon Ministan Tsaro, Laftana Janar Theophilus Yakubu Danjuma (mai ritaya), ya ce idan ya fadi abubuwan da suke faruwa a kasar nan, to ’yan Najeriya ba za su sake barci ba.
Janar Danjuma ya bayyana haka ne lokacin da yake jawabi a wajen wani taron kaddamar da wani littafi mai taken shekara 70 da ci gaban aikin jarida: wanda aka gudanar a Jami’ar Ibadan a Jihar Oyo.
Ya ce: “A yankin Yarbawa, kusan kowa ya rasa bakin magani, abin tsoro ne. Kuma ma mutane ba su ma damu da abin da ke faruwa ba. Idan da zan gaya muku abin da ke faruwa a Najeriya, to kuwa ba za ku iya sake barci ba.
“Don haka, gargadi da kuma shawarwarin da Cif Ayo Adebanjo ya bayar a kan gaba suke. Idan kuna son karin haske, to zan yi muku, a kebe.
“Mun auka cikin babban rami a matsayinmu na kasa. Kuma wadanda suka tsunduma mu ciki har yanzu suna nan. Don haka, ya kamata mu farka daga barci. Mu ne kawai za mu iya kare kanmu da kanmu.
“Munafukan cikinku da ke kai- komo daga jama’arku, suna bata tafiyar. Allah Ya ci gaba da dafa wa kasar na tare da yi mata albarka. Amma dai mu kwana da sanin cewa lallai mu ne da kanmu za m iya kare kawunanmu,” inji T.Y. Danjuma.
Tun farko Adebanjo, wanda jagora ne na kungiyar Yarbawa zalla ta Afenifere ya ankarar da su cewa yankin Yarbawa yana cikin hadari, inda ya ce: “Ruwa ya ci mu.”
Kalilan daga cikin gwamnanonin yankin Kudu maso Yamma ne kawai “Suka san ya kamata,” sun toshe dukkan komai. Ba sa iya tunkarar Shugaban Kasa, kawai saboda wani nuksaninsu.
“Buhari ba shi ne yake jan ragamar kasar nan ba. So yake ya mamaye mu. Ba na tsokaci a kai. Akwai zalunci a kasar na. Ga kuma Fir’aunanci da tabarbarewar al’amura. Idan Shugaban Kasa ya ce ba a mutunta tsarin doka da oda, to ina lauyoyin suke? Da zarar an ce babu bin doka da oda a kasa, to ai babu ita ma kanta gwamnatin, ke nan akwai tabarbarewar al’amura gaba daya,” inji Adebanjo.
Shi kuma Alaafin na Oyo, Oba Lamidi Adeyemi, ya musanta ta ikirarin gwamnati cewa ta kakkabe mayakan Boko Haram. Sa’annan ya kuma yi fatali da kudirin dokar nan da ke gaban Majalisar Dattawa kan kalaman batanci.