Idan na zama shugaban kasa Najeriya za ta fara fitar da tabar wiwi- Dan takarar shugaban kasa
Mai wallafa jaridar Sahara Reporters wanda take a yanar gizo, kuma dan takarar shugaban kasa Omoyele Sowore ya ce lallai idan har ya zama shugaban kasa, Najeriya za ta fara fitar da tabar wiwi zuwa kasashen waje. Dan takarar shugabancin kasar ya bayyana hakan ne a wajen taro a akn ‘yancin more rayuwa, “Ya kamata […]

Mai wallafa jaridar Sahara Reporters wanda take a yanar gizo, kuma dan takarar shugaban kasa Omoyele Sowore ya ce lallai idan har ya zama shugaban kasa, Najeriya za ta fara fitar da tabar wiwi zuwa kasashen waje.
Dan takarar shugabancin kasar ya bayyana hakan ne a wajen taro a akn ‘yancin more rayuwa, “Ya kamata mu fara lura da tabar wiwinmu domin bunkasa kudin shigarmu. Tabar wiwin da ake nomawa a Jihar Ekita na cikin mafi inganci a duniya. Da gaske nake, mutane suna samun biliyoyin kudi.
“Ina sanar da Hukumar NDLEA da su sani cewa Najeriya za ta fara fitar da tabar wiwi zuwa kasashen waje. Wannan umarni nake basu tun yanzu. Wannan ita ce maganata, na san maganar za ta jawo cece-kuce, amma idan kana son karin bayani zan yi.”