Idan Neja-Delta suka hana Jonathan takara za mu ba shi a Arewa maso Gabas – Bomboy

Shugaban Matasan Jam’iyyar PDP na Jihar Yobe kuma shugaban kamfanin sufuri na MADALLAH, Alhaji Ado Adamu (Bomboy) ya ce koda yankin Neja Delta ya hana Shugaba Jonathan takara, to su mutanen yankin Arewa maso Gabas za su iya ba shi, kuma ya ce yana goyon bayan sake mayar da dokar ta vaci a jihohin nan […]

Idan Neja-Delta suka hana Jonathan takara za mu ba shi a Arewa maso Gabas – Bomboy
Idan Neja-Delta suka hana Jonathan takara za mu ba shi a Arewa maso Gabas – Bomboy

Shugaban Matasan Jam’iyyar PDP na Jihar Yobe kuma shugaban kamfanin sufuri na MADALLAH, Alhaji Ado Adamu (Bomboy) ya ce koda yankin Neja Delta ya hana Shugaba Jonathan takara, to su mutanen yankin Arewa maso Gabas za su iya ba shi, kuma ya ce yana goyon bayan sake mayar da dokar ta vaci a jihohin nan uku da sauransu:

Aminiya: A gangamin magoya bayanka da ka gudanar a garin Damaturu ka ce kana goyon bayan sake fitowar Shugaba Jonathan takarar Shugaban kasa, kuma koda yankinsa na Neja-Delta ya hana shi takara a karo na biyu, to ku a yankin Arewa maso Gabas za ku iya ba shi takara, mene ne hujjar fadar haka?
Ado Bomboy: Lallai na fadi haka, kuma yanzu ma ina nanata cewa, koda Shugaba Jonathan bai samu tsayawa takara ba, a yankinsu na Kudu maso Kudu saboda tunanin ko ya yi mulki sau biyu, to, yankin Arewa maso Gabas na iya ba shi takara koda sau biyu ne, saboda yana da takardar zama dan asalin karamar Hukumar Gujba a Jihar Yobe wannan shi ne hujjata, domin ya yi zama mai tsawo a garin Buni Yadi da ke karamar Hukumar Gujba a shekarun baya can.
Aminiya: Wadanne dalilai kuke da su kuke cewa, za ku kwace gwamnati daga hannun Jam’iyyar APC a Jihar Yobe?
Ado Bomboy: Lallai akwai wahalar kwace gwamnati daga hannun jam’iyyar da ta shafe sama da shekara 14 tana mulkar jama’a, in har ta yi musu wani aiki na a zo a gani. To amma irin ayyukan raya kasa da jam’iyyarmu ta PDP ta yi ko take kan yi sama da 88 a Jihar Yobe za su sa al’ummar jihar su yi waje rod da Jam’iyyar APC, domin babu abin da masu mulkin jihar suke tsinana musu sai rabawa da tarawa da kuma kwashewa, tare da mayar da gwamnatinsu ta ’yan uwa da abokai.
 Idan har ka ga PDP ba ta ci zave a Jihar Yobe a badi ba, to sai dai in ba a yi zaven ba, amma matukar an yi zave to ko shakka babu su za mu lashe zaven cikin ruwan sanyi don kuwa jiki magayi.
Aminiya: A mafi yawan lokaci kakan caccaki Gwamna Ibrahim Gaidam cewa ya cika tafiye-tafiye na ba gaira ba dalili, duk da matsalolin tsaro a jihar alhali lokaci zuwa lokaci yana zagaya jihar yana bude irin ayyukan da yake yi, anya ba yarfe ba ne irin na siyasa?
Ado Bomboy: Tabbas Gwamna Gaidam na nuna halin ko oho kan rayuwar al’ummar jihar, babu abin da Gwamnan ya sa gaba sai yawan tafiye-tafiye kasashen waje duk da irin halin tavarvarewar harkokin tsaron da ke addabar jihar, savanin dan uwansa Gwamnan Jihar Borno Alhaji Kashim Shettima wanda ba ya zuwa ko’ina in ba Abuja ba, hakan ma sai za a yi taro, kuma hatta iyalansa na garin Maiduguri alhali Gwamna Gaidam shi da makusantansa duk sun kwashe iyalansu zuwa Abuja.
Aminiya: Me za ka ce kan zargin da wasu ’yan jam’iyyarku ta PDP a Jihar Yobe ke yi maka cewa kwanakin baya ka tara kudin jama’a da sunan za a kawo musu babura masu taya uku (Keke-NAPEP) amma har yanzu ba labari?
Ado Bomboy: Wannan ba gaskiya ba ne, kuma lalle duk wanda ya karvi wadannan kudade bai kyauta ba, kuma dan damfara ne kuma ina kiran duk wadanda aka karvi kudinsu da sunan za a ba su baburan da tsohon Ministan Kudi Dokta Yerima Ngama ya nemo rance daga Gwamnatin Tarayya su yi karar wanda suka ba shi kudin don neman hakkinsu. Babura masu taya uku tsohon Minista Ngama ne ya nemo su a matsayin bashi daga Gwamnatin Tarayya don rage radadin talauci ga al’ummar jihar kuma baburan 500 ne a kan Naira dubu 300 kowanensu, kuma an ba da umarni ga duk mai son karva ya sa Naira dubu 50 a cikin wani asusun ajiya da aka keve a matsayin somin tavi wanda da zarar an ba da baburan Naira dubu 250 kawai za a biya tunda an riga an sa Naira dubu 50 wannan shi ne gaskiyar magana.
 Aminiya: Me za ka ce kan dokar ta-vacin da wa’adinta ke gab da cika a jihohin nan uku, inda wasu ke cewa bai dace a kara ta ba, domin ba ta da wani amfani?
Ado Bomboy: Ina goyon bayan a sake mayar da dokar ta-vaci a jihohin nan uku, dari bisa dari don kuwa har yanzu akwai sauran rina a kaba, an kuwa san sai da zaman lafiya ne za a samu sukunin yin wani abu wai shi zave.

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno