Idan PDP ba ta yi gyara ba za ta sha mamaki a zaben 2019 – Hassan Ningi

Alhaji Abdulmumini Hassan Ningi tsohon dan Majalisar Dokoki ta Jihar Bauchi ne daga karamar Hukumar Ningi kuma yana daya daga cikin na hannun daman tsohon Gwamnan Jihar Malam Isa Yuguda. A tattaunawarsa da wakilinmu ya yi fashin baki game da makomar Jam’iyyar PDP nan da zaben 2019, inda ya ce zai yi wahala PDP ta […]

Idan PDP ba ta yi gyara ba za ta sha mamaki a zaben 2019 – Hassan Ningi
Idan PDP ba ta yi gyara ba za ta sha mamaki a zaben 2019 – Hassan Ningi

Alhaji Abdulmumini Hassan Ningi tsohon dan Majalisar Dokoki ta Jihar Bauchi ne daga karamar Hukumar Ningi kuma yana daya daga cikin na hannun daman tsohon Gwamnan Jihar Malam Isa Yuguda. A tattaunawarsa da wakilinmu ya yi fashin baki game da makomar Jam’iyyar PDP nan da zaben 2019, inda ya ce zai yi wahala PDP ta kai labari matukar ta ci gaba da dauki-dora:

Aminiya: Akwai mutane da dama da suka fice daga PDP a Jihar Bauchi ciki har da tsohon Gwamnan Jihar Malam Isa Yuguda, kai ma ka fita ko kana cikinta har yanzu?
Har yanzu ina cikin Jam’iyyar PDP sai dai kuma muna ci gaba da tattaunawa da magoya bayana da sauran masu ruwa-da-tsaki da muke tare da su. Domin ni duk abin da al’umma suke goyon baya shi ne ra’ayina, amma duk da haka mun san cewa akwai wasu kananan rigingimu a Jam’iyyar PDP tun daga matakin shugabancin jam’iyyar a kasa. Kuma jam’iyya tana tafiya ne da manufofi idan ka fahimci wasu manufofin sun saba wa al’ummarka, sai ka sake nazari da tunani domin siyasa ’yar lissafi ce.
Me mutane suke cewa game da fitar Isa Yuguda daga PDP?
Abin da mutane suke fada shi ne gara da ya fita daga jam’iyyar, wadansu kuma suna ganin bayan ya ci moriyar jam’iyyar ne sai ya fita. Kowa da yadda yake fassara abubuwan da suka faru, tabbas Malam Isa Yuguda yana daya daga cikin wadanda suka yi hidima ga PDP a Jihar Bauchi. Yana aikin banki ne aka dauke shi aka ba shi mukamin Ministan Sufurin Jiragen Sama a lokacin mulkin tsohon Shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo. Kuma lokacin da ya fito domin tsayawa takarar Gwamna a karkashin Jam’iyyar PDP sai wadansu suka yi masa yarfe cewa shi ba dan Jihar Bauchi ba ne. Daga bisani ya fita daga PDP ya shiga Jam’iyyar ANPP kuma ya lashe zaben Gwamna. Daga baya kuma ya sake dawowa jam’iyyarsa ta PDP tunda yana da goyon baya na jama’a. Ya ce ya koma PDP ne domin ta haka ne zai samu damar da zai yi aiki ga al’ummar da ta zabe shi domin Shugaban kasa dan PDP ne, wato marigayi Alhaji Umaru Musa ’Yar’aduwa.
Sama da kashi 95 cikin 100 na al’ummar Jihar Bauchi yanzu sun fahimci cewa tabbas Malam Isa Yuguda ya yi kokari wajen tallafa wa al’ummar jihar, domin a lokacin mulkinsa talakawa sun ji dadi sannan mata da matasa sun ci gajiyar mulkin dimokuradiyya. Lokacin da yake mulki ba a ganin kokarinsa, sai bayan da ya sauka kuma babu wani dan siyasa da yake da farin jinin Malam Isa Yuguda a yanzu a Bauchi duk inda ka zaga sai ka ji ana yabonsa.
A kananan hukumomin  Jihar Bauchi 20 duk karamar hukumar da mutum ya je sai ya nuna ayyukan alheri na gwamnatin Malam Isa Yuguda domin baya da mugunta a zuciyarsa, kuma mutum ne mai alheri da son kyautata wa marasa karfi da ke cikin al’umma.
Akwai masu kiran Yuguda ya kafa sabuwar jam’iyya me za ka ce?
Muna da jam’iyyu sama da 40 a Najeriya amma biyu ne kawai suke motsi wato PDP da APC sai kuma APGA da take da tasiri a wasu jihohi na kudancin kasar nan. Domin haka bata lokaci ne Yuguda ya kafa sabuwar jam’iyyar siyasa, a ganina a nemi wadda take da rijista a shiga, yana da damar da zai shiga duk jam’iyyar da manufofinta ya kwanta masa a rai.
Yaya kake ganin makomar PDP?
Makomar Jam’iyyar PDP ta fara gani tun a zaben shekara ta 2015 duk lokacin da aka yi magana, sai a ce duk Afirka babu jam’iyyar da ta kai ta girma, an manta cewa Jam’iyyar ANC a kasar Afirka ta Kudu ta girmi PDP. Abin da ya fi komai girma shi ne adalci idan PDP ta ci gaba da dauki-dora, to tabbas ba za ta kai labari ba a zaben shekarar 2019. Idan kuma ta dawo ta yi adalci ga ’ya’yanta aka daina son zuciya da kama-karya a cikinta, to, za ta iya kafa gwamnati a shekara ta 2019.
A fahimtata kura-kuran da za ta sake yi a nan gaba sai sun fi na baya muni, domin har yanzu akwai wadanda ba su da niyyar gyara da tsaida adalci a tsakanin ’ya’yan jam’iyyar.
Bayan ficewar Isa Yuguda daga PDP sama da mutum dubu 30 suka bayyana ficewarsu daga cikinta domin suna ganin ba a dauki hanyar gyara jam’iyyar ba tsakani da Allah.
Ficewar Malam Isa Yuguda daga PDP illa ce babba amma ba kowa zai fahimci haka ba, sai nan da lokaci kadan mai zuwa. Dillalan ’yan siyasa da suke cewa ficewarsa daga jam’iyyar ba wani abu ba ne sai ranar zabe za su sha mamaki Allah Ya kai mu 2019 da rai da lafiya.
Nan da yaushe za ka fice daga PDP?
Babu wani lokaci da na ware domin ficewa daga Jam’iyyar PDP domin ficewa daga jam’iyya habo ne, a kowani lokaci zai iya zuwa. Ba zan yanke hukunci ni kadai ba, amma dai muna nan muna ci gaba da tattaunawa.
Mene ne sakonka ga wadanda ka kira dillalan ’yan siyasa?
Babban sakona ga dillalan ’yan siyasa shi ne su kama sana’a domin babu al’ummar da za ta samu ci gaba da kwanciyar hankali sai kowa yana da hanyoyin samun kudin shiga a rayuwa. Duk lokacin da aka rasa masu fada wa shugabanni gaskiya, to tabbas babu inda za mu je. Duk mutumin da ba ya da abin yi, ba zai iya fada wa shugaba gaskiya ba, domin yana kwadayin kayan hannunsa, don haka duk abin da shugaba ya yi daidai ne. Tabbas al’ummar Jihar Bauchi suna cikin mawuyacin hali sakamakon yadda gwamnatin jihar ta gagara biyan ma’aikata da ’yan fansho na jihar da na kananan hukumomi albashi da hakkokinsu. Jihar Bauchi, jihar ’yan albashi ne ya kamata gwamnati ta tausaya wa al’umma.
Talakawan jihar nan suna cikin mawuyacin hali sakamakon yadda gwamnatin jihar ta gagara biyan albashinsu da fansho, jama’a suna shan bakar wahala a wannan gwamnati ta APC wadda ta shekara daya a Bauchi amma babu abin da ta tsinana wa al’umma. Abin da ake fada na yau daban, na gobe daban ya kamata shugabanni su rika fada wa talakawa gaskiya.