Idan ’yan Arewa na ganin Jonathan bai musu adalci suna iya kawar da shi – Sanata Ningi

dan Majalisar Dattawa mai wakiltar Bauchi ta Tsakiya Sanata Abdul Ahmed Ningi ya gana da wakilan Jam’iyyar PDP na kananan hukumomin jihar 20, a garin Dutse Jihar Jigawa inda ya bayyana bukatarsa ta tsayawa takarar Gwamnan Jihar Bauchi, kuma bayan ganawar wakilinmu ya zanta da shi: Aminiya: Sanata mene ne makasudin kiran wannan taron a […]

Idan ’yan Arewa na ganin Jonathan bai musu adalci suna iya kawar da shi – Sanata Ningi
Idan ’yan Arewa na ganin Jonathan bai musu adalci suna iya kawar da shi – Sanata Ningi

dan Majalisar Dattawa mai wakiltar Bauchi ta Tsakiya Sanata Abdul Ahmed Ningi ya gana da wakilan Jam’iyyar PDP na kananan hukumomin jihar 20, a garin Dutse Jihar Jigawa inda ya bayyana bukatarsa ta tsayawa takarar Gwamnan Jihar Bauchi, kuma bayan ganawar wakilinmu ya zanta da shi:

Aminiya: Sanata mene ne makasudin kiran wannan taron a Jihar Jigawa?
Sanata Ningi: Na kira wannan taro ne domin kowace karamar hukuma da ke mazabata don bayyana musu cewa kwalliya ta biya kudin sabulu game da aikina a majalisa da suka tura ni, musamman ina son bayyana wa mutanena su sani kasafin kudin shekarun da suka gabata, akwai manyan ayyuka da muka nemo a shekarar 2012 da 2013, yankina ya samu ayyuka na Naira biliyaa hudu da kusan rabi. Mun samu aikin MDGs na Naira biliyan daya da miliyan150 da ya shafi yin famfunan ruwa masu aiki da hasken rana da masana’antu. Mun samo aikin Naira biliyan daya ta hanyar Ningi zuwa Yada-Gungume zuwa Fiskar-Mata. Mun samu aikin kusan Naira miliyan dubu kan aikin madatsar ruwa ta Kafin Zaki da ayyukan Hukumar Kogin Hadeja da Jama’are da Upper Benue da sauran manyan ayyuka da kowa ke gani a yankinsa.
Kuma ina gode wa mutanena tun daga aka kafa wannan siyasa suka tura ni wakili a Majalisar Wakilai sau uku yanzu na zama Sanata, don haka nake mika musu godiyata saboda ba mu wuce mu hudu ba ake damawa da mu a majalisun tarayya tun farkon wannan zubin siyasar. Don haka suke ta yi min kiran na zo na tsaya takarar Gwamna, amma saboda lamuran ana bi a hankali ne ya sa yanzu na zo na gode musu tare da yin na’am kan kiransu.
Wajen kwarewa ina gani ko Najeriya zan iya jagorantarta fiye da yadda Shugaba Goodluck Jonathan ke jagoranta a yau saboda irin kalubalen da muke gani, musamman ’yan Arewa lamarin da a kullum ke ci mana tuwo a kwarya.
Aminiya: Me ya sa ka zabi Dutse a Jihar Jigawa don wannan taro?
Sanata Ningi: Na zabi nan wurin ne don gudanar da taron amsa kiran masu bukatar na fito takarar Gwamna, saboda wurin ya yi kusa da Bauchi ta Arewa da kuma Bauchi ta Tsakiya, kuma wuri ne da zan gana da mutane ba tare da samun hayaniya ba, domin ba taro ne na kamfe ba, ganawa ce da masu kaunata da masu kirana don na fito takara. Kuma ka ga an gama wannan ganawa lafiya kusan mutum dubu sun hadu ba tare da dan sanda ko dan banga daya ba a wurin taron, amma idan da a Bauchi ne dole a samu rudani, wasu ma da gayya za su turo a bata wa mutane rai. Amma akwai tarukan da za mu kira a Bauchi da duk mazabun nan gaba.
Mutanen da suka zo sun fahimci hikimar yin wannan taro a nan, kuma nan ba da jimawa ba zan sake kiran irinsa na matasa, zan kira irinsa na mata da na dattijan jam’iyya. Yanzu wakilai goma daga kowace karamar hukuma ta Bauchi ta Tsakiya ne sai kuma wakilai daga sauran kananan hukumomi da ba na mazabata ba su ma duk sun zo taron don nuna kauna.
Aminiya: Game da batun sake kundin tsarin mulki da ake yi tare da taron kasa, wane kokari kuke yi na ganin hakan bai cutar da Arewa ba?
Sanata Ningi: Canja kundin tsarin mulki ba na zaton abu ne da zai iya yiwuwa a Najeriya, saboda mai sa a sauya kamar Shugaban kasa ko dan majalisa kundin ne ya kawo shi. To idan ya ce a sauya ina matsayinsa? Kuma da wace hujja ko da wane kundi zai yi aiki. daya daga cikin abubuwan da muka yi muhawara a kai shi ne cewa idan za a sauya kundin ba dole ba ne sai dan majalisa ba, kowa zai iya kawo shawararsa, madadin yadda suke cewa a yi yanzu wanda dole sai ka yi zaben wakilai sai an jirkita majalisa wacce ita ce za ta samar da tsari da kudin gudanar da aikin don haka dole a samu tufka da warwara.
Aminiya: Ana ganin ku ’yan PDP kuna son tursasa Shugaba Goodluck ya yi tazarce alhali ’yan Arewa ba sa so saboda matsalolin da suke ciki ko me za ka ce?
Sanata Ningi: Goodluck Jonathan ba shi ne matsala ba, mu bukatarmu ita ce wa zai iya taimakon Najeriya ya taimaki Arewa da Kudu da kowace shiyya ta kasar nan ba tare da nuna bambanci ko kabilanci ba. Don haka ba na goyon bayan wani dan Najeriya da zai iya zama Shugaban Najeriya ya kasa yi wa kowa adalci. Bukatarmu ita ce a samu mai adalci ga Arewa da duk sassan Najeriya kuma daga kowace kabila ya fito. Kuma mutanen Arewa su ne ya kamata su samar wa kansu hanya madaidaiciya da za su bi don ta fitar su daga cikin mawuyacin halin da suke ciki. Idan ’yan Arewa na ganin Jonathan ba ya yi musu adalci, su ne za su tashi tsaye su kawar da shi da kuri’unsu, su nemi wanda zai kai su tudun mun tsira su hada kai da sauran mutane su taimaka a kawar da shi. Dole idan muna son kawar da Jonathan dan takararmu ya shiga kasashen Yarabawa da Kudancin Najeriya. Mu ’yan siyasa namu shi ne mu bi abin da talakawanmu ke so, illa iyaka muna da hakki na nuna ga abin da ya dace a yi idan an zabi wane. Mu dai bukatarmu ita ce a yi mana adalci.
Aminiya:Yaya ku ’yan majalisa daga Arewa kuke ji a ranku game da abubuwan da ke faruwa a Arewar, kuma kuna gani taron kasa da ake yi zai kawo maslaha?
Sanata Ningi: Ni ban san abin da taron kasa zai iya cimmawa ba, domin mutane suka zauna suka zabo abokansu da ’yan gidansu da ’yan uwansu da abokan aikinsu da kabilarsu da ’ya’yansu, domin idan da a ce mutane suka zabe su kamar yadda tsarin ya ce, shi ne za a iya cewa za a samu ganin wani haske kan lamarin. Ban yarda wannan taro zai iya samar da wata dama ta magance matsalar kasar nan ba wanda ba mu samar da ita ba.
Ku ’yan jarida ku ne ya kamata ku ci gaba da wayar da kan mutane game da irin zaman da ake ciki a kasar nan. Haka su ma talakawa su sani duk wanda ya ba ka kudi ka zabe shi, to babu zancen Arewa ka yi aikin kudi ne, amma idan ka yi zabe na akida, to, ka san kana da ta cewa. Abu na gaba akwai mutanen da suka yi kida da waka wajen gyara Arewa amma yanzu kowa ya kauce ya bar su su kadai saboda son abin duniya ba gudunmawa ba kariya saboda rashin alkibla kuma ko ka zo da abu na ci gaba sai son rai ya shigo ciki.
Tunanin dan siyasa a yau yadda zai ci zabe ne ba nuna akida da sanin ya kamata, tunanin talaka kuma wanda zai ba shi kudi ko ta wace hanya aka samu kudin. Saboda sanin kowane mutane da dama sun yi magana kan Arewa an buge su an take hakan ya sa a yanzu zukatan mutane sun yi sanyi saboda ganin irin kisan gwanin da ake yi mana. Akwai mutanen da idan maganar Arewa ta gaskiya za a yi bai kamata a ce ma suna da abokan takara a jihohinsu ba. Amma a kasar Yarabawa ko Amurka duk wanda aka san ya kware wajen kishi da aiki da nuna sanin ya kamata ko takara ba a yi da shi, amma ba a Arewa ba, inda kullum kowa so yake yi ya nakasa dan uwansa.
Don haka ’yan jarida akwai aiki a kanku na yi wa mutane bayani sosai don su fuskanci gaskiya da alkibla tagari. Ba kawai kowa ya zo da dan kudinsa a jaka sai a sanya shi a gaba ba, idan muka ci gaba da haka, to akwai abin tausayi a gare mu muna tufka gaba baya na warwarewa wajen nemo wakilan da suka san abin da ya dace. Fatarmu ita ce nan gaba a samu sauyi kowa ya san irin tukun da zai yi don Arewa. Idan ka zuba ido kana ganin bala’i ko masifa sun fada kan wani to ka shafa wa kanka ruwa domin zara ba ta barin dame da fatar Allah Ya yi mana maganin matsalolinmu.

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno