Idan ’yan Arewa suna zuwa Kudu karatu za a samu karin hadin kai – Sarkin Barebari

Sarkin Barebarin Jihar Ogun ya yi kira ga al’ummar Arewa su rika turo ’ya’yansu zuwa Kudancin kasar nan domin yin karatu a manyyan makarantun yankin saboda hakan zai sanya cudanya da gogayya a tsakanin daliban Arewa da na Kudu, kuma ya kara dangon zumunci da hadin kai a tsakanin manyan gobe da al’ummar kasa baki […]

Idan ’yan Arewa suna zuwa Kudu karatu za a samu karin hadin kai – Sarkin Barebari

Sarkin Barebarin Jihar Ogun ya yi kira ga al’ummar Arewa su rika turo ’ya’yansu zuwa Kudancin kasar nan domin yin karatu a manyyan makarantun yankin saboda hakan zai sanya cudanya da gogayya a tsakanin daliban Arewa da na Kudu, kuma ya kara dangon zumunci da hadin kai a tsakanin manyan gobe da al’ummar kasa baki daya.

Sarkin Barebarin ya yi wannan kira ne a tattaunawarsa da Aminiya inda ya ce, “Dalibanmu na Arewa ba su cika zuwa su yi karatu a Kudu ba, idan ka ga dan Arewa a nan Kurmi akasari ’yan ci-rani ne laburori ko ’yan kasuwa da tsirarin ma’aikatan Gwamnatin Tarayya da akasari suke zaune a Kurmi suke aiki don dole ba don suna so ba. Wannan hali na ’yan bokonmu na rashin son barin gida yana janyo mana koma-baya wajen gogewa da gwagwarmayar rayuwa. A jami’o’in Kurmi akwai guraben da ake ware wa ’yan Arewa amma dalibanmu ba sa zuwa su cike guraben, idan suka zo za a dauke su su yi karatu cikin sauki, inda za su ci riba biyu, za su yi karatu sannan su yi gogayya da wadanda ba a yankinsu ba, masu iya magana ma kan ce yawon duniya mabudi ne.”

Ya ce a makon jiya Mai martaba Shehun Borno wanda shi ne Uban Jami’ar Legas ya ziyarci Jihar Legas inda aka yaye dalibai da dama da suka kammala karatunsu, “Mu al’ummar Barebari mun tashi baki dayanmu a karkashin jagorancin Sarkin Barebarin Jihar Legas Alhaji Mustafa Muhammad Mai Kanuri na Legas, inda muka ga yadda al’amura suka gudana, amma da an samu ’yan Arewa da dama a cikin daliban da abin zai kara armashi, su ’yan uwanmu na Kurmi suna kokarin zuwa Arewa su yi karatu amma mu ’ya’yanmu ba sa zuwa nan Kudu don yin karatu,” inji shi.

A karshe ya yi kira ga matasa su guji tu’ammali da miyagun kwayoyi su kasance ’yan kasa nagari, “Ka ga kwaya da sauran kayan maye su ne tushen duk wata tashin-tashina don haka kamata ya yi iyaye su rika sanya idanu a kan ’ya’yansu,” inji shi.