Idi-Araba: Garin da tsofaffin sojoji ’yan Arewa suka kafa a Legas
An samu sunan garin Idiyarba ne ta hanyar wasu itatuwa guda uku da suke garin da ake kira Araba.
Garin Idi-Araba (Idiyarba) da ke Karamar Hukumar Mushin a Jihar Legas daya ne daga cikin garuruwan da ’yan Arewa suka kafa a Kudancin kasar nan wanda kuma yake a sahun gaba a fuskar tattaro gidajen ’yan Arewa a waje guda.
Aminiya ta ziyarci garin na domin gano yadda ’yan Arewa suka kafa shi, inda ta zanta da wadansu dattawan garin wanda yake da sarakunan Hausawa biyu da kowanensu yake kiran kansa da sunan Sarkin Hausawan Idi-Araba.
- Tallafin COVID-19: Cikin wadanda suka samu ya duri ruwa
- Kotun Koli ta soke dokar haramta sanya hijabi a makarantun Jihar Legas
Alhaji Ali Aware daya ne daga cikin dattawan garin a wannan lokaci wanda kuma ya yi fice a garin.
Aminiya ta zanta da shi domin jin yadda Hausawa suka kafa garin, inda ya fara da bayar da tarihinsa kamar haka; “Sunana Ali Aware Muhammadu Inuwa Garun Malam.
“An haife ni ne a kasar Ghana, mahaifina haifaffen Garun Malam ne, wanda ya yi bulaguro zuwa kasar Ghana ya kuma haife mu mu 9 a wani kauye na kasar da ke kira Pute, amma dukkanmu da mahaifinmu mun dawo gida Najeriya, a Garun Malam mahaifin namu ya rasu.
“Dalilin dawowa ta Najeriya kanwar mahaifinmu mai suna Hajiya Amina, wacce ta yi aure a Abeokuta ta je Ghana ta dauko ni na zauna da ita a Abeokuta. Daga can na koma wajen wani aminina da yake kasuwancin canji a Legas yana zaune a garin Idi-Araba ana ce masa Abubakar Danja, tare muka taso a Abeokuta.
“Na shigo garin Idi-Arab ne a 1971, ban dade tare da aminin nawa ba Allah ya yi masa rasuwa a 1973,” inji shi.
Yadda aka kafa garin Idi-Araba
Alhaji Ali Aware ya ce ya samu labarin cewa garin Idi-Araba ya kafu ne bayan Yakin Duniya na Biyu, inda sojojin da suka dawo daga yakin ’yan Arewa suka yada zango a garin.
“Su tsofaffin sojojin da suka dawo daga Yakin Duniya na Biyu a tsakanin shekarun 1949 ne suka kafa garin, a wancan lokacin sana’arsu ba ta wuce gadi da fawa da kananan sana’o’i ba kafin daga bisani Allah ya albarkaci garin, inda yanzu kashi 70 cikin 100 ’yan canji ne, sai mahauta da masu sana’ar hannu da sauransu.
“A yanzu babu irin sana’ar da babu, akwai wanzamai da masu dori da sauransu.
“Akwai Hausawa daga dukkan jihohin Arewa, sannan akwai Nufawa da Igala da duk wata kabila ta Arewa kuma su ma duk suna da nasu shugabannin,” inji shi.
A Idi-Araba (Idiyarba) Izala ta fara kafuwa a Kudu
Ya ce kungiyar wa’azin Musulunci ta Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah ta fara kafuwa ne a Idiyarba kafin ta watsu a Kudancin Najeriya.
“Izala ta zo ta kuma bayyana ne a garin Idiyarba kafin daga bisani ta yanzu a sassan Kudancin Najeriya.
“Akwai wani malami mai suna Muhammad Auwal daga Ghana ya zo ya sauka a gidan Alhaji Hassan Bade shi ne ya fara yin da’awar Izala, to a wannan lokaci muna daga cikin sahun farko da muka amsa a lokacin duk wanda ya shiga ko ya karba za a tsane shi a daina mu’amala da shi a tsangwame shi.
“Sai da muka yi shekara biyar muna zuwa kotu domin an ki yarda mu yi masallacin Juma’a amma daga bisani kotu ta ba mu izini, aka ce kowa na da ’yancin ya yi addinin da yake so.
“Dalilin kafuwar Izala a nan Idiyarba ne ya sa hedikwatar Izala ta Kudancin Najeriya take a nan Idiyarba, yanzu haka ma akwai filin da aka saya ana kuma aikin ginin cibiyar Izala a Kudancin Najeriya a nan garin idiyarba” inji shi.
Rikicin ‘June 12’ da na OPC a Idiyarba
Haka zalika tarihin garin Idiyarba ba zai cika ba tare da an ambaci rikicin kabilancin da ya rutsa da garin ba, wanda ya so ya balbalta shi.
A cewar Alhaji Ali Aware manyan rikicin kabilancin da suka auku a garin guda biyu ne, wadanda suka hada da rikicin kabilanci na bayan zaben ‘June 12’ a 1993 sai kuma rikincin OPC, “Shi rikicin OPC shi ne ya fi ta’azzara don ni da nake maganar nan da kai sai da aka kone gidana, na bar unguwar na koma VI wato can cikin birnin Legas inda na shekara 3 zuwa 4, kafin daga bisani na komo bayan na gyara gidan, domin zama cikin al’ummarmu ta Arewa ta fi dadi.
“A lokacin rikicin na OPC garin Idiyarba duk dan Arewa da yake da yadda zai yi ya fita daga garin ya fita, sai ’yan kadan da suka yi zamansu, amma ka ga yanzu an dawo gari ya habaka fiye da a baya ma, don akwai wata unguwa wacce ake kira Bakar Idiyarba wacce Unguwar Idiyarba ta haifa, a baya kananan gidaje ne na katako da kasa, amma daga baya sun rika sayar wa Hausawanmu mutanenmu na yin manyan gine-gine, kai ka ce a Lekki ko VI cikin garin Legas kake, to ka ga arziki ya yawaita ga Hausawa a Idiyarba,” inji shi.
Sarautar Hausawa a Idiyarba
Da ya tabo batun sarauta a garin Idiyarba, Alhaji Ali Aware ya ce a inda ake da matsala a garin Idiyarba shi ne a bangaren sarauta domin garin yana da sarakunan Hausawa biyu ne, kuma kowane na kiran kansa Sarkin Hausawan Idiyarba, “Akwai Alhaji Hassan Auyo, akwai Alhaji Idris Lawal Haruna, kuma kowanensu yana cewa shi Sarkin Hausawan Idiyarba ne, kuma kowa na da magoya bayansa.
“Ni dai a lokacin da na zo garin Idiyarba Sarkin da na tarar guda daya ne ana kiransa Alhaji Garba Ba’are, bayan Allah Ya masa rasuwa to akwai mutum biyu wadanda a lokacin su ne aka fara samun baraka a sarautar kuma dukkansu ’yan majalisa ne na Sarki Ba’are, wato Alhaji Haruna da Alhaji Hassan Auyo, kowanensu ya ce yana son sarautar.
“Ni a lokacin na koma cikin garin Legas, a wancan lokacin Sarkin Hausawan Legas, wato Sarki Dogara ya so ya daidaita al’amarin amma hakan bai yi ba, to a wancan lokaci ma sarautar cikin garin Legas ta rabu gida biyu, domin Sarki Dogara Yaro shi ne ya nada Sarki Sani Kabir a matsayin Hakimi a garin Idiyarba amma da ya ga ya yi karfi ya tasa, sai ya ce shi ma Sarkin Hausawa ne a Ebute Meta kuma ka san nan ma cikin garin Legas ne, to ka ji yadda tarihin sarautar Legas ta rabu gida biyu.
“To a haka wadannan sarakuna kowa sai ya nada nasa hakiman, kowa na kokarin fadada masarautarsa a haka ne Sarki Dogara Yaro ya nada da Sarki Haruna Lawal a matsayin Sarkin Hausawan Idiyarba yayin da shi kuma Sarki Kabir ya nada Sarkin Hassan Auyo a matsayin Sarkin Hausawan Idiyarba.
“Wannan raba masarauta biyu a gari guda na Idiyarba na janyo mana koma-baya. A kwanaki matasan gari sun yi yunkurin gyara lamarin amma hakan ya ci tura.”
Ya kara da cewa akwai auratayya a tsakanin Hausawa garin Idiyarba da abokan zamansu Yarbawa inda kowane bangare ke aura daga daya bangaren, wannan ne ya kara dankon zumunci a tsakaninsu.
Dalilin da sunan titunan Idiyarba na Hausa ne – Sarki Idris Lawan
Aminiya ta zanta da daya daga cikin sarakunan Hausawan garin Idiyarba, Alhaji Idris Lawan Haruna, wanda ya bayyana cewa a garin Idiyarba aka haife shi, a nan kuma aka haifi mahaifinsa, Sarkin Idiyarba Alhaji Lawan Haruna, domin kakanninsa ne suka zauna a garin Idiyarba kuma suna cikin Hausawan farko da suka zauna a garin.
“Kakkaninmu ne suka zo Idiyarba suka haifi iyayenmu, su kuma suka haife mu, gidanmu yana daga cikin gidaje mafiya tsufa a Idiyarba, wanda duk wani Bahaushe idan ya zo nan yake sauka a gidan kakanmu, Alhaji Abdullahi Haruna.
“Kuma mahaifina shi ne wanda ya sanya wa layukan garin Idiyarba suna. Wannan ne ya sa za ka ga yawancin layuka ko loko a unguwar Idiyarba sunayen Hausawa ne, akwai Layin Masallaci, wato inda Masallacin Juma’a yake, akwai Layin Haruna, sunan kakanmu, akwai Malam Gana, akwai Garba Musa da sauransu.
“Mahaifinmu ya sanya sunayen layukan garin Idiyarba ne kafin samun ’yancin kan kasa wato kafin 1960, ni kuma an haife ni a 1965. Lokacin da muka taso garin Idiyarba duk gonaki ne,” inji shi.
Yadda aka samo sunan Idiyarba
Ya ce an samu sunan garin Idiyarba ne ta hanyar wasu itatuwa guda uku da suke garin da ake kira Araba, sunan bishiyoyin ke nan.
“Idi kuma na nufin karkashi ko gindin bishiyar wato Idi-Araba da harshen Yarbanci na nufin karkashin bishiya ko kuma gindin bishiya.
“To su kuma Hausawa ba sa iya fadin Idi-Araba sai suka mayar da sunan ya zama Idiyarba da haka sunan garin ya samo.
“To a lokacin kakanninmu ba sa sayen waje idan za a sayar da gida ko fili, in an tallata masu sai su ce ba zama suka zo ba, to amma a lokacin iyayenmu sun sayi wurare da dama kuma sun ji dadin hakan sai suka kwadaitar da mu, wannan ne ya sa a yanzu kashi 90 cikin 100 na gidajen da ke garin Idiyarba na Hausawa ne, kuma Hausawa sun fi Yarbawa yawa a unguwar.
“Daga cikin abin da ya bambanta wannan unguwa da sauran matsugunai na Hausawa shi ne Idiyarba matsugunin Hausawa ne da ya tara su a wuri guda kuma su ne suke gudanar da al’amuran garin, ko da kiran Sallah ne za ka ji a masallatan Hausawa ne a ke yi, sannan ni ne kansilan farko Bahaushe a garin Idiyarba.
“Bayan Sarki Ba’are ya yi sarauta domin shi ne Sarki mafi dadewa bisa karaga, sai mahaifinmu Alhaji Lawal Haruna ya yi Sarki, sai dai a lokacin ne shi ma Sarki Hassan Auyo ya nuna sha’awarsa a kansa ne Idiyarba ta fara samun Sarki biyu.
“Mahaifinmu Sarkin Hausawan Legas Alhaji Dogara Yaro ne ya nada shi, kuma bayan Allah Ya yi masa rasuwa ni ma wannan majalisa mai girma ce ta nada ni, shi Sarkin Hausawan Legas Aminu Dogara shi ne ya ba ni takardar kuma har gobe ina wannan majalisa tasu da shi da Sarkin Fulanin Legas Alhaji Muhammadu Bambado.
“A lokacin da na taso muna yara na tarar lokacin Sarki Manzo ne yake sarauta a garin Idiyarba, wanda tsohon soja ne, kasancewar garin Idiyarba an jibge tsofaffin sojoji da suka yi Yakin Duniya da na Biyafara,” inji shi.