Ido zai raina fata

Kotun daukaka kara, inda Shugaban Majalisar Dattijai, Bukola Saraki ya garzaya a kokarinsa na kai kararraki kotuna daban-daban don a hana kotun da’ar ma’aikata sauraron karar da aka kai gabanta, ta yi watsi da karar, tana cewa ba ta da ikon hana waccan kotun aikin da ke gabanta. A sakamakon haka kotun da’ar ma’aikatar za […]

Ido zai raina fata
Ido zai raina fata

Kotun daukaka kara, inda Shugaban Majalisar Dattijai, Bukola Saraki ya garzaya a kokarinsa na kai kararraki kotuna daban-daban don a hana kotun da’ar ma’aikata sauraron karar da aka kai gabanta, ta yi watsi da karar, tana cewa ba ta da ikon hana waccan kotun aikin da ke gabanta. A sakamakon haka kotun da’ar ma’aikatar za ta ci gaba da sauraron karar sai dai idan kotun koli ta dakatar da ita sa’anan ne kuma wadanda suka shigar da karar gabanta za su rungumi kaddara ko su yi Allah-Ya-isa.

Kowa dai na sane da irin kudurin Bukola Saraki na ganin an dakile wannan shari’ar. Ya samu cikakken goyon baya da daurin gindi daga abokan aikinsa, watau dattijan majalisar da kuma wasu daga majalisar wakilai ta tarayya daga dukkan sassan kasar nan, ya kuma samu nasarar rudar kansa da kuma fadakar da masu yi masa ingiza-mai-kantu-ruwa cewa ba wani abu dai ya sa ake wasan kura da shi ba illa bakar siyasar da jama’ar kasar nan suka gwanance akai. A cewarsa yana kotu ne don ya kwaci kansa, ya kuma kare mutuncinsa daga masu neman tozarta shi sakamakon wafce kujerar Shugabancin Majalisar Dattijai da ya yi.
Yawancin ‘yan Najeriya dai ba za su iya cewa suna da masaniya game da abin da Bukola Saraki da lauyoyinsa ke tunani game da yadda wannan shari’ar za ta kaya ba: ko zai kubuta ne ko dauri zai sha kamar huhun goro, har sai igiya ta ragu, oho? Amma saboda ganin yadda ya dage wajen ganin ya wargaza tsarin shari’ar da ake yi masa ana iya cewa yana cike da fargabar makomarsa dangane da yadda za ta kaya. Ana zarginsa ne da yin za’ida game da kaddarorinsa da kuma rashawa. An rattaba masa zarge-zarge guda 13 ne, kuma wadanda suka dankwafar da shi gaban alkali sun ce suna bukatar kwanaki biyu zuwa uku ne kacal don tabbatar da hujjojin da za su kai ga daure shi.
A takaice dai ana iya cewa zabin da Bukola Saraki zai fi amincewa game da yadda shari’arsa za ta kaya mai ban tsoro ne, domin abubuwan da za su iya biyo baya masu rikitarwa ne, za su kuma kidima kowa. A dauka ma zai daukaka kara zuwa kotun koli game da hukuncin kotun daukaka kara za ta kuma bar kotun da’ar ma’aikata ta ci gaba da sauraron shari’arsa da ke gabanta, ya kuma samu nasara a kotun da’ar ma’aikata, hakan zai iya karfafa matsayinsa a siyasance, ya kuma sanyaya gwiwar jam’iyyarsa ta APC, a sakamakon haka kuma za a kulla wata rikakkiyar gaba tsakaninsu, har sai daya daga cikinsu ya bayar da kai bori ya hau, kuma hakan na iya canja salon siyasar kasar baki daya.
Idan kuma har aka same shi da laifi, to hakan zai zo da sauki, zai sauka daga mukaminsa ne na shugaban majalisar dattijai, ba girma ba arziki, kuma wannan al’amari ne da ba zai yi fatan afkuwarsa ba, duk kuwa da cewa ya zame tsuntsun da ya kirawo ruwa tun da farko. Amma muddin aka samo wata kwakkwarar maslaha tsakaninsa da jam’iyarsa, kamar yadda yake sa ran haka na iya faruwa, to sai kowa ya mayar da wukarsa cikin kubenta, a rungumi juna, a rage fadin rai, a kuma nade tabarmar kunya da hauka. Amma sai dai ko da hakan bai cutar da Bukola da jam’iyyarsa ba, yana iya kawo cikas ga manufar Shugaba Muhamadu Buhari na yaki da rashawa da cin hanci. Bisa ga yadda al’amura ke gudana game da shari’arsa da ke gaban kotun da’ar ma’aikta da kuma sakamakon da zai iya biyo baya, zai yi wuya a ce Sanata BukolaSaraki ya tsallake rijiya da baya.
Idan za a iya tunawa dai babu shegantakun da Saraki bai yi ba don dakile shari’ar da ake yi masa, sa’anan kuma ya sha yin kurari game da kare dimokuradiyya da tabbatar da cewa ana aiki da doka da oda a kasar nan, amma ya sha kokartawa don yin kafar ungulu a shari’ar da ake yi masa, ba tare da la’akari da irin sakamakon haka ga tsarin dimokuradiyya da ci gaban harkokin siyasar kasar nan ba. A maimakon ya mika wuya, ya bi tafarkin shari’a, don a ji dadin bin bahasin zarge-zargen da ake yi masa cikin ruwan sanyi, sai ya tsaya tsilla-tsilla da tsugudidin da ba za su fisshe shi ba. Dangane da haka ne ya zuga wasu abokan aikinsa a majalisun kasa, kuma suka biye masa kamar wasu bi-ta-zai-zai, alhali kuwa dukkansu taron tsintsiya ce babu shara, domin ba za su iya hana a yi masa shari’a ba sa’ilin da suke rufa masa baya duu, idan zai gurfana gaban kotu.
Da farko dai kowa ya tsammaci cewa Sanata Saraki bai son tsugunawa gaban kotu ne saboda a ganinsa hakan cin mutuncinsa ne a matsayin Shugaban Majalisar Dattijai, alhali kuwa yana sane da cewa gaskiya ba ta neman ado, kuma babu yadda za a yi a sauya wa tuwo suna, yana nan dai a tuwonsa. Idan da Sanata Saraki ya tabbatar cewa yana da gaskiya a wannan batun, ai da ba zai tsaya wata-wata ba, yana nuku-nuku don kaucewa gurfana gaban kotu, da sai kawai a matsayinsa na mai yin doka da kuma girmama ta, ya garzaya gaban kotu don a hanzarta sauraronsa, a kuma gaggauta yanke hukunci kowa ya huta. Wannan ce kadai hanyar da ya kamata ya bi don kunyata wadanda ya daddage, yana ta kiransu makiyansa, masu son ganin bayansa da kuma tozarta shi a banza. An dai ce ciki da gaskiya wuka ba ta huda shi. Amma da alama Bukola Saraki bai amince da haka ba, yana tsoron wukar da aka dauko don gwadawa, ga shi nan kuma ido zai raina fata bayan an fiddo ta.