Idris Abdulaziz zai ci gaba da zama a kurkuku saboda gaza cika sharudan belinsa
An zargi malamin da yin kalaman batanci a Bauchi.
Fitaccen malamin addinin Musuluncin nan na Bauchi, Dokta Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi, zai ci gaba da zama a gidan gyaran hali bayan belinsa ya sake gamuwa da tsaiko.
Kotun ta ci gaba da zamanta a ranar Laraba bayan shafe kwana 30 ana ci gaba da tsare malamin a gidan yari na Bauchi.
- Majalisa za ta binciki yadda gwamnatin Buhari ta jinginar da filayen jiragen sama
- Buhari ya kai wa Mangal ziyarar ta’aziyyar matarsa
Lauyoyin da ake tuhuma karkashin jagorancin Barista Abubakar Sadiq, sun bayyana cewa kotun ba ta da hurumin ci gaba da shari’ar biyo bayan karar da aka shigar gaban babbar kotun tarayya ta 7 da ke Bauchi.
Babbar kotun dai ta umarci kotun shari’ar Musulunci da ta dakatar da shari’ar tare da mika bayanan babbar kotun ga babbar kotu ta 7 a Bauchi.
Bayan tattaunawa kan batutuwan da suka shafi bayar da belin limamin da bangarorin biyu suka yi, alkalin kotun, Malam Hussaini Turaki ya bayar da belin bisa wasu sharudda uku da suka hada da gabatar da mutum uku da za su tsaya masa; Hakimi, mai digiri na uku da kuma fitaccen dan kasuwa a cikin birnin Bauchi.
Aminiya ta rawaito cewa an tsare Sheikh Abdulaziz ne a ranar 15 ga watan Mayun 2023 bisa zarginsa da tayar da hankalin jama’a da kuma yin kalaman batanci wanda Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Bauchi, CP Alhassan Aminu ya gurfanar da shi a gaban kotu.
Malamin dai ya shafe kwanaki bakwai a gidan yari duk da cewa an bayar da belinsa saboda wasu sharudda masu tsauri na kudi Naira miliyan daya da kuma wadanda za su tsaya masa.
An saki malamin ne bayan da ya cika sharudan belin da kotun ta yi masa na gabatar da wasu ‘yan kasuwa biyu da wasu fitattun malaman addinin Musulunci guda biyu.