IFAD ta kafa kwamatin fadakar da manoma kan bunkasa harkar noma a jihohi 7 Na Najeriya

Hukumar Bunkasa Aikin Gona ta Afrika IFAD ta bullo da shirin fadakar da manoma tare da wayar da kan manoma a fadin Najeriya inda aka ware jihohi bakwai domin bawa manoma horon kuma a daukacin jihohin bakwai aka dauki kananan hukumomi tara a kowacce karamar hukuma aka zabi kauyuka uku inda a kowacce jahar kauyuka […]

IFAD ta kafa kwamatin fadakar da manoma kan bunkasa harkar noma a jihohi 7 Na Najeriya

Hukumar Bunkasa Aikin Gona ta Afrika IFAD ta bullo da shirin fadakar da manoma tare da wayar da kan manoma a fadin Najeriya inda aka ware jihohi bakwai domin bawa manoma horon kuma a daukacin jihohin bakwai aka dauki kananan hukumomi tara a kowacce karamar hukuma aka zabi kauyuka uku inda a kowacce jahar kauyuka 21 za su amfana.

Sakamakon hakan ya sa IFAD z ata bude makarantun a daukacin wadancan kauyuka uku domin koyawa manoma dabarun aikin gona a kananan hukumomi tara dake wadancan jihohi 7 ciki har da Jahar Jigawa, inda a kowacce karamar hukuma za bude guda uku a kauyuka uku da aka zaba a kowacce karamar hukuma daga cikin taran da hukumar ta zaba.

Shi babban jami’in shirin fadakar da manoma na kasa mai kula da shiyyar Katsina da Jigawa da Kano da Yobe da Bauchi da sauran jihohin, Mmalam Abddulahi Sirajo wadda shi ne jami’i mai lura da shirin fadakar da manoma dabarun noman zamani ya shaida wa manema labarai a lokacin da ya kai ziyara gonakin manoma a Jigawa cewa kungiyar manoma ta ziyarci cibiyar fadakar da manoman dake kauyan Katuka a karamar hukumar Kiyawa da kauyan Kwadiya dake karamar hukumar Ddutse a ranar Talatar da ta gabata.

Ya ce za a bude makarantun ne da nufin koyawa manoma dabarun aikin gona na zamani saboda haka nema ita hukumar IFAD ta umarci manoman dake zaune a kauyukan da hukumar ta amince za ta yi aiki da su su kafa kwamatin fadakarwa na ilimi wadda zai rika fadakar da manoma tare da turawa hukumar ta IFAD bayanan halin da manoman ke ciki ta fuskar aikin gona.

Ya kuma tabbatar masu da cewar duk kwamatin da ya fi hazaka shi ne za a dauka zuwa kasashen waje idan wata tafiya ta taso, za a yi da manoma a jahar ta Jigawa, ya ci gaba da cewar wannan aiki ya hada jihohi bakwai ne ciki har da jahohin Borno, Sokoto, Kebbi, Jigawa, Zamfara da Katsina a matsayin shedikwata.

Ya ci gaba da cewar aikin ya hada kananan hukumomin jihohin tara guda 104 inda kauyuka 727 za su ci moriyar wannan shiri na fadakar da manoma sabbin dabarun aikin noma na zamani ta hanyoyin zamani domin ganin an samawa manoma kasuwa akan abinda suke nomawa.

Shi ma babban jami’in shirin na Jahar Jigawa Malam Muhammed Amin ya ce IFAD ta ummarci mutanen kauyukan uku da aka zaba a kowace karamar hukuma daga cikin kananan hukumomin tara da hukumar ta zaba a jahar ta Jigawa su kafa kwamatin fadakar da manoma. Ya ce IFAD za ta rabawa manoma na cibiyoyin da aka zaba domin wayar da kan manoma tallafin naira miliyan takwas a kowanne kauye dake kananan hukumomin tara inda kowacce karamar hukuma daga cikin taran manomanta za su amfana da tallafin naira miliyan 24.

Kamar yadda bincike ya nuna Manoman alkama na yankin Kwadiya dake Dutse sun koka game da matsalar bullar tsutsa mai lalata tumatir a gonakinsu, haka zalika manoman sun nuna damuwarsu game da tsadar man fetur dake kokarin zama cikas saboda tsadarsa.

Dagachin Kwadiya, Malam Ali Musa Kwadiya shi ne ya wakilci manoman yankin ya ce manoma a yankin na Kwadiya dake yin aikin gona a dajin Shimadara suna cikin matukar damuwa saboda tsadar man fetur lamarin da yasa manoma da yawa cikin wani hali.

Ya yi korafin ne a daidai lokacin da IFAD ta kai ziyarar aiki gonakin manoman yankin domin ilimantar da manoman yadda za su yaki dumamar yanayi tare da koyawa manoman sabbin dabarun aikin gona.

Dagacin ya ce wannan tsadar ta man fetur tana yi wa manoman barazana kuma za ta iya sawa manoma da dama su ajiye maganar aikin gona dan haka ya bukaci IFAD da su saka baki ga gwamnatin tarayya domin samar wa manoman na alkama da na shinkafa mafita kan tsadar man fetur da ya addabi kowa a Najeriya.

Ya kuma shawarci hukumar ta IFAD da ta a gazawa manoman na alkama da shinkafa dake yankin na Kwadiya dake yankin karamar hukumar ta Dutse da takin zamani, ya ce aikin noman rani zai kara tunbatsa a yankin na Kwadiya. Ya kara da cewar shi babban burinsa a rayuwa ya zama zakaran gwaji a fagen aikin gona musamman a bangaren noman alkama ace babu kamarsa a fadin Jahar Jigawa.

Shi ma sakataren kungiyar manoma na yankin, Malam Mahmood Abdullahi Kwadiya cewa ya yi babu abinda ya addabi manoman yankin kamar wata tsutsa dake lalatawa manoman tumatir, kuma sun yi iyakacin kokarinsu wajan yi wa tumatirin magani amma tsutsar ta ki mutuwa.

Saboda haka ya bukaci hukumar ta IFAD da ta kawowa manoman yankin na Kwadiya agajin maganin feshi domin ceto su daga yin hasarar amfanin gonarsu ya ci gabada cewar akwai alamar idan aka agazawa manoman da magani manoma a yankin za su sami riba mai yawan gaske.

Shi kuma babban jami’in aikin gona na hukumar ta IFAD, Malam Umar Abubakar Danzomo nuna takaicinsa ya yi ga manoman jahar ta Jigawa cewar bas a neman iri mai inganci a lokacin noma, dan haka ya bukaci manoman da su rika amfani da iri mai inganci a gonakinsu yayin shuka.

Ya kuma nuna takaici game da yadda manoma suke yin hasarar amfanin gona a lokacin girbin gonar saboda ba sa yin amfani da kayan girbi irin na zamani suna yin amfani da kayan gyaran gona irin na gargajiya, lamarin da yake sawa manoma suke zubar da irin a gonnarsu basu kai ga cimma burinsu ba.