Iftila’i: Ya kamata ’yan Najeriya su taimaka wa Morocco da Libya —Malamai
Kimanin mutum 20,000 ne ake fargabar sun rasu a ambaliyar Libya, wasu 3,000 kuma suka rasu a girgizar kasar da ta auku a Morocco.
Kungiyar malaman Musulunci ta Najeriya ta bayyana cewa iftila’in girgizar kasa a Morocco da kuma ambaliya a Libya sun isa zama izna ga mutane su koma ga Allah.
Kimanin mutum 20,000 ne ake fargabar sun rasu a ambaliyar Libya, wasu 3,000 kuma suka rasu a girgizar kasar da ta auku a Morocco.
- Peter Obi ya san bai ci zaben 2023 ba —Wole Soyinka
- An haramta wa jiragen ruwa tafiyar dare a Taraba
Kungiyar ta bukaci al’ummar Musulmi da su tausaya wa wadanda iftila’in ya samu, ta hanyar taimaka musu da abubuwan bukata na yau da kullum.
“Wannan ya ishi mutane izina su koma ga Allah (SWT), wanda ke busa rai kuma Ya zare shi a lokacin da Ya ga dama, ko Ya sanya damuwa ko Ya yaye ta bisa hikimarSa.
“Muna tuanatar da al’ummar kasahsen Morocco da Libya su runugmi kaddarar da ta same su, su koma ga Allah domin samun lada.
“Muna kira a al’umma Musulmin Najeriya da su taimaka wa ’yan Morocco da Libya da wannan iftila’i ya shafa ta hanyoyin da suka dace.