1910-2021: Igen Maidoki ta rasu bayan shekara 111

Mahaifiyar Shugaban Hukumar Zakka da Wakafi ta Jihar Sakkwato, Hajiya  Fadimatu wadda aka fi sani da Igen Maidoki, ta rasu bayan shekara 111 a duniya. Dattijuwar a cikin al’umma ta rasu ne bayan doguwar jinya da ta yi a asibitin Koyarwa ta Jami’ar Usmanu Danfodiyo da ke Sakkwato. Malam Igen Maidoki tana da dangantaka da […]

1910-2021: Igen Maidoki ta rasu bayan shekara 111

Mahaifiyar Shugaban Hukumar Zakka da Wakafi ta Jihar Sakkwato, Hajiya  Fadimatu wadda aka fi sani da Igen Maidoki, ta rasu bayan shekara 111 a duniya.

Dattijuwar a cikin al’umma ta rasu ne bayan doguwar jinya da ta yi a asibitin Koyarwa ta Jami’ar Usmanu Danfodiyo da ke Sakkwato.

Malam Igen Maidoki tana da dangantaka da Sheikh Ummaru Mu’alkammu, wanda iyalinsa ke rike da sarautar Magajin Rafin Sakkwato.

Mahaifinta shi ne Malam Abdulkadir wanda aka fi sani da Jikan Bahago, kuma masaniyar addini ce kamar mahaifiyarta Malama Yatu.

Wani jikanta, Abdurrahim Lawal Maidoki ya shaida wa Aminiya cewa ta bar ‘ya’ya bakwai cikinsu har da mahaifinsa, Shugaban Hukumar Zakka da Wakafi ta Jihar Sakkwato, Mihammad Lawal Maidoki (Sadaukin Sakkwato).

Sauran su ne: Malama Hauwa’u (Umma), Malama Hadiza (‘Yajjari), Malama Fadimatu (Rigo), Malama Umaimatu, Malama Hafsat da kuma Malama Sa’adatu. Ta kuma bar jikoki sama da 50 da tattaba kunne.

Gwamna Aminu Waziri Tambuwal da Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar suna cikin wadanda suka halarci sallar janazarta.

Sun roki Allah Ya gafartawa margayiyar Ya isar wa bayanta.