Igiyar ruwa ta juya mu kamar na’urar wanki – Ba’Japaniya mai ninkaya

Kamfanin Dillancin Labarai na AFP, ya ruwaito yadda Saori Furukuwa, daya daga cikin Japanawa biyar da ke ninkaya a kasan ruwa suka samu ceto a lokacin da masu aikin ceto suka matsa kaimi wajen laluben wata mata da ta bace a cikin ruwa.Furukuwa ta ce yanayi na da kyau a lokacin da gungunsu  masu ninkaya […]

Igiyar ruwa ta juya mu kamar na’urar wanki – Ba’Japaniya mai ninkaya

Kamfanin Dillancin Labarai na AFP, ya ruwaito yadda Saori Furukuwa, daya daga cikin Japanawa biyar da ke ninkaya a kasan ruwa suka samu ceto a lokacin da masu aikin ceto suka matsa kaimi wajen laluben wata mata da ta bace a cikin ruwa.
Furukuwa ta ce yanayi na da kyau a lokacin da gungunsu  masu ninkaya ya nutsa cikin ruwan Nusa Lembongan, a Gabashin kasar Indonesiya, a tsibirin Bali
“Lokacin da muka fara ninkaya babu wata matsala game da yayin teku,” a cewarta, inda ta bayyana cewa a lokacin babu igiyar ruwa.
Sai  kuma kwatasam mu kayi karo da iska. “Saman teku ya fara motsawa tamkar injin wankin tufafi, sai muka rike hannayenmu aka yi ta juya mu,” injita.
Matar ta bnayyana cewa ita da abokan ninkayarta sun haye kan tsaunukan ruwa ne, bayan da suka sha juyi na tsawon lokaci, har masu ceto suka iso, inda suka fitar da su, aka kwantar da su a gadajena sibiti.
Mijin wannan mata Putu Mahardena Sembah, ya shiga cikin gungun masu aikin ceto. “Ina ta fatan ganin mun ganota, duk da cewa ’yan sanda sun bayyana mana cewa da wuya a sameta a raye,” inji shi.
‘yan uwa da abokan arzukan Furuwa daga kasar Japajn sun yiwo ayari don shiga aikijn ceto, kamar yadda AFP ya ruwaito.