Iheanacho da Ndidi sun taimaki Leicester ta lashe kofin Gasar FA
Leicester City ta lashe gasar FA a karon farko cikin shekaru 137 da kafa ta.
’Yan wasan Najeriya biyu, Kelechi Iheanacho da Wilfred Ndidi, sun taimaka wa kungiyar kwallon kafa ta Leicester City, wurin doke Chelsea da ci 0-1 a wasan karshe na gasar FA, na kasar Ingila.
Karo na farko ke nan da kungiyar Leicester City ta lashe gasar FA cikin shekaru 137, tun bayan kafa kungiyar.
- Kofin FA: Karo da Guardiola ba dadi – Kocin Chelsea
- Cutar COVID-19 za ta tsananta a 2021 —WHO
- Hisbah ta kwace daruruwan kwalaben giya a Jigawa
- Saudiyya ta sake bude wuraren shan gahawa da shisha
Kwallom da dan wasa Youri Tielemans ya zura a gaban ’yan kallo mutum 22, 000 a filin wasa na Wembley, ita ce ta raba raini tsakanin kungiyoyin biyu.

Wannan shi ne karo na farko da aka samu ’yan kallo masu yawa a filin wasa a kasar Ingila, tun bayan barkewar annobar COVID-19.
Youri Tielemans, dan asalin kasar Belgium, ya zura kwallon ne a minti na 63, daga bugun kusurwa da kungiyar ta Leicester ta yi.