Iheanacho ya samu bizar tafiya gasar cin kofin duniya a New Zealand
dan kwallon Najeriya Flying Eagles da yanzu haka yake kwallo a kulob din matasa na kulob din Manchester City na Ingila ya samu bizar da za ta ba shi damar shiga kasar New Zealand don fafatawa a gasar cin kofin duniya na matasa da za a fara a ranar 6 ga watan gobe. Bizar da […]
dan kwallon Najeriya Flying Eagles da yanzu haka yake kwallo a kulob din matasa na kulob din Manchester City na Ingila ya samu bizar da za ta ba shi damar shiga kasar New Zealand don fafatawa a gasar cin kofin duniya na matasa da za a fara a ranar 6 ga watan gobe.
Bizar da dan kwallon ya samu ta kawo karshen rade-radin da ake yi na cewa da wuya dan kwallon ya samu nasarar zuwa gasar bayan ya kasa samun biza.
dan kwallon wanda ba ya cikin ’yan kwallon Najeriya da suka samu horo a sansanin horar da su na Nuremberg da ke Jamus, zai wuce kai tsaye ne zuwa New Zealand inda sauran ’yan kwallon U-20 tare da kocinsu Manu Garba za su tarar da shi a can.
Sauran ’yan kwallon da ake sa ran za su hadu da sauran a can sun hada da dan kwallon Granada na Sifen Isaac Success da kuma Moses Simon da ke yin kwallo a Beljiyum.
Iheanacho ne aka zaba a matsayin Gwarzon dan kwallo a gasar cin kofin kwallon kafa na duniya na ’yan kasa da shekara 17 da ya gudana a Hadaddiyar Daular Larabawa a shekarar 2013 bayan Najeriya ta samu nasarar lashe kofin.
Sai dai Iheanacho bai halarci gasar cin kofin matasa na Afirka da ya gudana a Senegal ba, inda Najeriya ta samu nasarar lashe gasar a karo na bakwai.