Ikon da ke cikin adalci (4)
Allah cikin alherinSa Ya sake kawo wannan lokaci mai albarka wanda Shi da kanSa Ya shirya tun kafuwar duniya. A yau za mu ci gaba ne da binciken da muke yi muna karatu ne daga cikin Littafin Matta 10: 17 – 48. Ina so mu sake karantawa yanzu domin mu iya ci gaba da wannan […]
Allah cikin alherinSa Ya sake kawo wannan lokaci mai albarka wanda Shi da kanSa Ya shirya tun kafuwar duniya. A yau za mu ci gaba ne da binciken da muke yi muna karatu ne daga cikin Littafin Matta 10: 17 – 48. Ina so mu sake karantawa yanzu domin mu iya ci gaba da wannan koyarwa tamu. Maganar Allah tana koya mana cewa: “Kada ku zaci na zo domin in warware Attaura da Annabawa, ba na zo domin in warware ba, amma domin in ciccika. Gaskiya fa nake fada muku, har sama da duniya (su kare) ko wasali daya da digo daya ba za ya shude daga Attaura ba, sai dukan abu ya cika.
Dukan fa wanda ya ketare guda daya mafi karanta daga cikin dokokin nan, har ya koya wa mutane haka, za a ce da shi mafi karanta a cikin mulkin sama: amma dukan wanda za ya aikata su har ma ya sanar, za a ce da shi mai girma a cikin mulkin sama. Gama ina ce muku, idan adalcinku bai fi na Marubuta da Farisawa ba, ba za ku shiga mulkin sama ba ko kadan. Kun ji aka fada wa mutanen da, ba za ka yi kisan kai ba da kuma ko wane ne ya yi kisan kai ya shiga hadarin hukunci, amma ni ina ce muku, ko wane ne ya yi fushi da dan uwansa ya shiga hadarin hukunci, kuma, ko wane ne ya ce wa dan uwansa Raka, ya shiga hadarin Sanhedrin; kuma ko wane ne ya ce, kai wawa, ya shiga hadarin Jahannama mai wuta. Idan fa kana cikin mika baiwarka a wurin bagadi, can kuma ka tuna da dan uwanka yana da wani abu game da kai, sai ka bar baiwarka can a gaban bagadi, ka yi tafiyarka, a sulhuntu da dan uwanka, kana ka zo ka mika baiwarka. Ka shirya da abokin husumarka da sauri, tun kana tare da kan hanya, domin kada ya zama abokin husumarka ya bashe ka ga alkali, alkali kuma ya bashe ka ga dogari, a jefa ka cikin kurkuku. Gaskiya ina ce maka, dadai ba za ka fita daga can ba, sai ka biya iyakar anini tukuna. Kun ji aka fadi, ba za ku yi zina ba, amma ni ina ce muku, duk wanda ya dubi mace har ya yi kyashinta, ya rigaya ya yi zina da ita a cikin zuciya tasa. Kuma idan idonka na dama yana sa ka tuntube, ka cire shi, ka yar; gama gara gare ka gabarka daya ta lalace da a jefa jikinka dungum a cikin Jahannama. Kuma idan hannunka na dama yana sa ka yi tuntube, ka yanke shi ka yar, gama gara gare ka gabarka daya ta lalace da jikinka ya shiga dungum cikin Jahannama. Kuma aka fadi, duk wanda za ya saki mata tasa, sai ya ba ta takarda ta saki, amma ni ina ce muku, ko wane ne ya saki mata tasa, in ba domin fasikanci ba, yana sa ta ta zama mazinaciya: kuma dukan wanda ya auri sakakkiya, zina yake yi. Kuma, kun ji aka fada wa mutanen da, ba za ku yi rantsuwa da karya ba, amma sai ku cika wa’adojinku ga Ubangiji, amma ni ina ce muku, ba za ku yi rantsuwa ko kadan ba; ko bisa sama, gama Kursiyyin Allah ce, ko kuwa bisa duniya, gama matashin sawayensa ne, ko kuwa wajen Urushalima, gama birnin madaukakin Sarki ce. Ba kuwa za ku yi rantsuwa bisa kanka ba, gama ko gashi guda daya ba ka da iko ka maishe shi fari ko baki. Amma bari zancenku ya zama, eh, eh; da a’a, a’a: abin da ya wuce wadannan duka daga wurin mugun ne. Kun ji aka fadi, ido maimakon ido, hakori, maimakon hakori, amma ni ina ce muku, ba za ku yi tsayayya da wanda yake mugu ba: amma iyakar wanda ya mare ka a kumatu na dama, juya masa wancan kuma. Idan kuma wani yana so ya kai shari’a, ya karbe maka rigarka, bar masa mayafinka kuma. Kuma duk wanda ya tilasa maka tafiyar mil daya, tafi tare da shi har biyu. Kun ji aka fadi, ka yi kaunar makwabcinka, ka ki magabcinka: amma ni ina ce muku, ku yi kaunar magabtanku, kuma wadanda suka tsananta muku, ku yi musu addu’a; domin ku zama ’ya’yan Ubanku wanda ke cikin sama: gama yakan sa rana tasa ta fito wa miyagu da nagargaru; yakan aiko da ruwa bisa masu adalci da marasa adalci. Gama idan kuna kaunar wadanda ke kaunarku, wace lada ke gare ku? Ko masu karbar haraji, ba haka suke yi ba? Idan kuwa kuna gai da ’yan uwanku kadai, ina kun fi wadansu? Ko al’ummai ba haka suke yi ba? Ku fa ku zama cikakku, kamar yadda Ubanku na sama cikakke ne.”
Akwai albarka mai yawa duk lokacin da muka samu zarafin karutu daga cikin Littafi Mai tsarki. Yesu Kiristi ya ce mana maganarsa rai ce, kuma tana da ikon tsarkake mu daga zunubanmu. Mu yi dogon karatu daga cikin Littafin Matta, Sura 5, koyarwar Yesu Kiristi ne da kansa, yana koyarwa ne ga almajiransa game da yadda za su yi rayuwa daban da ta sauran masu addini. Dole rayuwarsu ta bambanta da ta sauran mutane. Mun yi bincike a cikin koyarwar da muka yi a wadanda suka gabata; mun ga cewa babu abu guda daya da mutum zai iya yi wanda zai gamshi Allah, domin mutum mai zunubi tun daga lokacin da Adamu ya ki bin umarnin Allah, Allah Ya soma shirin yadda zai iya kawo mutum gare shi, a lokacin Annabi Musa, Allah Ya ba su dokokin da za su yi biyayya da su kafin ainihin shirin Ubangiji. Allah shi bayyana a cikin Yesu Almasihu. Bari mu dauki misalai guda biyu kawai daga cikin koyarwar Yesu Kiristi, ba koyarwar addini ba ne, a’a, yadda rayuwar mai bi ya kamata ta kasance ne: Yesu Kiristi ya ce, “Kada ku zaci na zo in warware Attaura da Annabawa; ban zo domin in warware ba, amma domin in ciccika.” Kowa ya san cewa zina dai yin jima’i ne da mace wadda ba matarka ba, amma Yesu Kiristi ya ce, ba lallai ba ne sai ka kwanta da matar, idan har kai a matsayin namiji, ka yi kyashin kowace mace wadda ba matarka ba, ka rigaya ka yi zina da ita a cikin zuciyarka. Haka nan idan ba ka da aure, kai dan saurayi, kana kallon ’yan mata kana kyashinsu cikin zuciyarka, ka rigaya ka yi zina da su cikin zuciyarka da su, hukumcin ka daya da wanda ya aika wannan. Yesu Kiristi ya yi magana a kan kisan kai, ya ce ba lallai sai ka samo wuka, ko gatari ko kuwa takwabi ka kashe wani ba, amma duk lokacin da kake fushi da dan uwanka, kana cikin hadarin hukunci. Idan kuwa muka duba kamar yadda Allah Ya ce, a yau a ganinka mutane nawa ne mazinata? Mutane nawa ne masu kisan kai? Watakila kai ma kana daya daga cikin irin wadannan mutane! Maganin wannan irin matsala shi ne, zuwa wurin Yesu Kiristi ne cikin ban-gaskiya domin mu karbi nasa adalci maimakon namu wanda yake mai kazanta.
Ina so mu kafa tushe mai karfi domin iya gane irin ikon da ke akwai a cikin adalci. Bari Ubangiji Allah Ya taimake mu, mu iya lura da tafiyarmu cikin ban-gaskiya domin mu gamshe shi.
Sai kuma mako mai zuwa idan Ubangijinmu Yesu Kiristi bai bayyana ba.