Ikon gicciyen Yesu Kiristi (2)

A yau ina so ne mu yi magana kadan a kan ikon da ke cikin gicciyen Yesu Kiristi. Idan Allah Ya yarda za mu komo ga bincikenmu a kan almajiranci irin na Kirista kashi na takwas. Yau cikin duniya duka ana bikin tunawa da ranar mutuwar Yesu Kiristi bisa gicciye da duk azabar da ya […]

Ikon gicciyen Yesu Kiristi (2)
Ikon gicciyen Yesu Kiristi (2)

A yau ina so ne mu yi magana kadan a kan ikon da ke cikin gicciyen Yesu Kiristi. Idan Allah Ya yarda za mu komo ga bincikenmu a kan almajiranci irin na Kirista kashi na takwas. Yau cikin duniya duka ana bikin tunawa da ranar mutuwar Yesu Kiristi bisa gicciye da duk azabar da ya sha da kuma tashinsa daga matattu. Masu bin Yesu Kiristi da dama sun san wannan rana a matsayin ranar mutuwarsa ne kawai, amma ba su da cikakken sani game da dalilin da ya yarda ya sha wannan wahala.

Abu na farko da kowane dayanmu ya kamata ya gane shi ne, zunubi ya raba dangantaka tsakanin mutum da Allahnsa. Idan mun tuna, lokacin da Allah Ya halicci mutum, daga farko Allah Ya yi shi ne cikin surarsa, mu karanta Littafin Farawa 1: 26 – 28 da ke cewa “Kuma Allah Ya ce, bari Mu yi mutum cikin surarmu, Bisa ga kamaninmu; su yi mulki kuma bisa kifaye na taku da tsuntsaye na sama da bisashe da kuma bisa dukan duniya da kowane abu mai rarrafe wanda ke rarrafe a bisa kasa; Allah fa Ya halita mutum cikin sura tasa, cikin surar Allah Ya halicce shi; namiji da mace Ya halicce su. Allah Ya albarkace su kuma, Allah Ya ce musu, Ku yalwata da ’ya’ya, ku ribu, ku mamaye duniya, ku mallake ta, ku yi mulkin kifaye na teku da tsuntsaye na sarari da kowane abu mai rai wanda ke rarrafe a kasa. Allah Ya albarkace su kuma.” Wannan shi ne takaitatcen labarin halittar mutum; umarnin da muka karanta a nan ya kunshi abin da ya kamata mutum ya yi ne a cikin gonar da Allah Ya sanya shi ciki
A cikin LiTtafin Farawa 2: 15 – 17; maganar Allah na cewa, “Sai Ubangiji ya dauki mutum, ya sanya shi cikin gonar Adnin domin ya aikace ta, shi tsare ta kuma. Ubangiji Allah kuma ya dokaci mutumin, yana cewa, an yarda maka ka ci daga kowane itacen gona a sake, amma daga itace na sanin nagarta da mugunta ba za ka diba ba ka ci, cikin ranar da ka ci, mutuwa za ka yi lallai.” Allah, ba da wasa ya ba da wannan umarni ba, ya ce wa mutumin; ran da ka ki yin biyayya ga maganata, har ka diba daga ’ya’yan wannan itace ka kuma ci, a cikin ranar, mutuwa za ka yi lallai: idan mutum ya yi magana sai ya hada da wannan kalma LALLAI – ma’ana abu daya kawai, wato babu shakka, ba makawa, Wannan umarnin daga bakin Ubangiji Allah mahaliccin komai da kowa.
Yadda tsakanin Ubangiji da mutum ya caci:
Mene ne ya kawo gaba tsakanin mutum da Allah da ya halice shi? Amsar ita ce; kin bin umarnin Allah. Zunubi! A cikin Farawa 3: 6 – 12, maganar Allah na koya mana cewa “ Sa’anda macen ta lura itacen yana da kyau domin ci, abin sha’awa ne kuma ga idanu, itacen kuma abin marmari ne domin ba da hikima, sai ta debi ’ya’yansa, ta ci, ta kuma ba mijinta tare da ita, shi kuwa ya ci. Dukansu biyu kuwa idanunsu suka bude, suka waye kuma tsirara ne su, suka dundunke ganyayen baure, suka yi wa kansu mukuru. Sai suka ji muryar Ubangiji Allah yana yawo a cikin gona da sanyin yamma; mutumin fa da matatasa suka buya daga fuskar Ubangiji Allah a cikin itatuwan gona. Ubangiji Allah kuwa ya kira mutumin, ya ce masa ina kake? Shi kuwa ya ce, na ji motsinka cikin gona, na ji tsoro, domin tsirara nake: na kuwa buya, Ya ce masa, wa ya fada maka tsirara kake? Ko ka ci daga itace wanda na dokace ka kada ka ci? Mutumin ya ce, macen da ka ba ni domin ta zauna tare da ni, ita ta ba ni daga itacen, ni kuwa na ci.”
Wannan shi ne mafarin damuwa tsakanin mutum da Allah, gaba ta shiga tsakaninsu domin rashin yin biyayya. Allah ba ya harka da zunubi ko da wasa. Ainihin mutuwa ba lallai rabuwar jiki da ruhu kadai ba ne, a’a, mutuwa mafi muni shi ne rabuwa da Allah kamar yadda muka gani a inda muka yi karatu a Farawa. Wannan irin rabuwa kuwa, la’ana ne. Mutum ya saba zumunci da Allah kafin ya yi zunubi ko kuwa ya yi rashin biyayya da umarnin Allah. Da zarar ya san ya yi abin da Allah ba Ya so, sai ya gudu da matarsa suka buya cikin gona. Ba sa son ganin Allah kuma. Dalilin kuwa daya ne kawai- wato zunubi.
Zuwan ubangijinmu Yesu Kiristi cikin duniya a kamannin mutum; ba domin komai ba ne, amma domin ya nuna mana kauna sahihiya, ya cece mu kuma daga bautar zunubi, mu kuma mu yi rayuwa da za ta gamshi Ubangiji Allah.
A cikin Littafin Galathiyawa 3:13 – 14, Bulus Manzo ya rubuto ta wurin ikon Ruhu Mai tsarki haka: “Kiristi ya fanshe mu daga la’anar shari’a, da ya zama la’ana maimakonmu, gama an rubuta, kowane wanda an rataye shi ga itace la’ananne ne. Domin albarkar Ibrahim ta sauko wa al’ummai cikin Kiristi Yesu; domin mu karbi alkawarin ruhu ta wurin bangaskiya.”
Abu na farko wanda gicciyen Yesu Kiristi ga dukan mutane wadanda suka ba da gaskiya shi ne, La’anar da take kanmu ya dauke ta gaba daya, maganar Allah cikin Littafin Romawa 6 : 23 na cewa “ Gama hakkin zunubi mutuwa ne; amma kyautar Allah Rai na har abada ne cikin Kiristi Yesu Ubangijinmu.” La’anar da ta zo kan mutum tun daga farko, ta ci gaba da bin dan Adam har sai mun samu kubuta a cikin Yesu Kiristi ta wurin ban-gaskiya cikin mutuwarsa bisa gicciye da kuma tashinsa daga matattu. Wannan kuwa shirin Allah ne da kansa. Kafin zuwan Yesu Kiristi cikin duniya; Allah ya shirya hanya na dan lokaci wa mutum domin shi iya zuwa gabansa ya yi masa sujada, wannan ya kunshi hadaya na dabbobi domin mutum ya daidaita tsakaninsa da Allah, amma ainihin shirin Allah shi ne ya kawo mu ga kafa ban-gaskiyarmu cikin abin ya rigaya ya gama.
Idan har ka bada gaskiya ga Allah cikin shirin ceto wadda ya gama, Littafin Kolosiyawa 2:13 – 15, na cewa “ Ku kuma, da ke matattu ta wurin laifuffukanku da rashin kaciya na namanku, ku, ni ke cewa, ya rayar da ku tare da shi, ya kuwa gafarta mana dukan laifuffukanmu, ya shafe shari’a wadda ta tsaya mana bisa farillanta, tana kuwa gaba da mu: ya kawar da ita daga turba, yana kusance ta ga gicciye; bayan da ya tube wa kansa mulkoki da ikoki, ya nuna su a sarari, yana kirari a bisansu cikin wannan.”
Ikon da yake cikin gicciyen Yesu Kiristi, shi ne ikon da ya ci nasara bisa Shaidan da dukan mulkoki, da ikoki cikin sammai ko kuwa cikin duniya duka. A yau yayin da muke murnar shirin ceto wadda Allah da kansa ya shirya ga dukan dan Adam, sai mu tambayi kanmu ko mun samu wannan ceto. Har yaushe ne za ka ci gaba da zama cikin zunubi? Allah ya rigaya ya shirya hanyar fansarmu ta wurin ban-gaskiya cikin Yesu Kiristi. Ubangiji ya taimake mu.
Sai mu gode wa Allah da ya sa muka yi zaben Shugaban kasa lafiya. Mu kuma ci gaba da addu’a domin zabe na gaba.