Ikon gicciyen Yesu Kiristi (4)
A yau, ina so ne mu kara yin bayani kadan a kan zancen gicciyen Yesu Kiristi da kuma ikon da ke cikin wannan gicciye A cikin Littafin 1Korinthiyawa 2: 6-8, maganar Allah tana cewa; “Duk da haka muna maganar hikima a wurin cikakku: amma hikima ba ta wannan zamani ba, ba kuwa ta mahukuntan wannan […]
A yau, ina so ne mu kara yin bayani kadan a kan zancen gicciyen Yesu Kiristi da kuma ikon da ke cikin wannan gicciye
A cikin Littafin 1Korinthiyawa 2: 6-8, maganar Allah tana cewa; “Duk da haka muna maganar hikima a wurin cikakku: amma hikima ba ta wannan zamani ba, ba kuwa ta mahukuntan wannan zamani ba, da suke shudewa: amma muna maganar hikima ta Allah cikin asiri, wato hikima wadda take a boye, wadda Allah Ya kadara ta kafin farkon zamanu domin darajarmu, hakiman zamanin nan kuwa duka ba su san ta ba; gama da sun san ta, da ba su gicciye Ubangijin daraja ba.” Wane irin asiri ne wadda take cikin gicciyen nan na Yesu Kiristi Ubangijinmu? Wannan iko ya sa Shaidan da kansa yana ta da na sani da ban gicciye wannan Yesu Kiristi din ba.
Gicciyen Yesu Kiristi ya kawo karshen magabtaka wadda ke tsakanin Allah da mutum, wannan magabtaka, kamar yadda muka sani ya soma ne a lokacin da mutum ya yi rashin biyayya ga umarnin da Allah Ya ba shi a cikin gonar Adnin. Magabtakan nan kuwa ita ce ta sa mutumin da matarsa suka gudu suka buya a cikin itatuwan da ke cikin gonar domin ba sa so su ga fuskar Allah kuma, ba sa son su sake zumunci da Allah kamar yadda suka saba; zunubi takan sa mutum ya guji Allah. Shaidan a kullum yakan so ya yi mulki da mutum; shi ya sa, sa’adda ya ga cewa mutum ya samu ’yancin kansa daga kuncin da ya sa shi; abin bai yi masa ba ko kadan shi ya sa yake ta da na sani!
A cikin Littafin Kolosiyawa 2: 6 – 15, maganar Allah tana cewa: “Tunda shi ke kuka karbi Kiristi Yesu Ubangiji, sai ku yi tafiya cikinsa haka nan, dasassu, ginannu kuma cikinsa, kafaffu cikin ban-gaskiyarku, kamar yadda aka koya muku, kuna yalwata cikin godiya. Ku yi hankali kada kowa ya same ku ta wurin iliminsa da rudinsa na banza, bisa ga tadar mutane, bisa ga rukunai na duniya, ba bisa ga Kiristi ba: gama daga cikinsa dukan cikar Allahntaka cikin jiki tana zaune, cikinsa kuwa an kamilta ku, shi wanda yake kan dukan mulki da iko: a cikinsa kuwa aka yi muku kaciya wadda hannu ba ya yi ba, cikin tubewar jikin nama, cikin kaciya ta Kiristi; biznannu ne ku tare da shi cikin baptisma, inda aka tashe ku kuma tare da shi ta wurin ban-gaskiya cikin aikin Allah, wanda ya tashe shi daga matattu. Ku kuma, da ke matattu ta wurin laifufffukanku da rashin kaciya na namanku, ku; nake ce wa, ya rayar da ku tare da shi, ya kuwa gafarta muku dukan laifuffukanmu, ya shafe shari’a wadda ta tsaya mana bisa ga farillanta, tana kuwa gaba da mu, ya kawar da ita daga turba, yana kusance ta da gicciye; bayanda ya tube wa kansa mulkoki, da ikoki, ya nuna su a sarari, yana kirari a bisansu cikin wannan.” Sai mu san wannan cewa, mu, mutane muna rayuwa ne da ma cikin zunubi, Shaidan ne ke da iko a bisa rayuwarmu; ba mu da ’yancin kanmu ko kadan abin da Shaidan ya ga dama ne yake yi da mu har lokacin da Yesu Kiristi ya shigo cikin wannan duniya. Zuwan Yesu Almasihu ya kawo ga karshen dukkan wahala karkashin ikon Shaidan; wannan ba karamin alheri ba ne zuwa ga kowane mutum.
A wurin da muka yi karatu a cikin Littafin Kolosiyawa, mun ga yadda ikon gicciyen Yesu Kiristi ya tube wa Shaidan dukan ikon da yake da shi, tashin Yesu Kiristi daga matattu kuma ya ba shi iko cikin dukkan sammai da duniya da dukkan abin da ke karkashin duniya.
Abin da ya kawo gaba tsakanin mutum da Allah tun daga farkon halitta; zunubi ne, zunubi ne ya shiga tsakanin mutum da Allah, Allah; Shi Mai tsarki ne a cikinSa babu zunubi ko kadan, kuma ba Ya son zunubi koda wasa, Ya rigaya Ya ba da hukuncin zunubi, a cikin maganarSa Ya ce – gama hakkin zunubi mutuwa ne- wannan hukuncin ba ya canjawa har yau; abin da ya faru shi ne wannan shiri na Allah wanda Ya yi domin Ya ceci mutum daga hallaka. Idan mun tuna, a cikin koyarwar da muka yi watanni kadan da suka gabata, mun ga cewa bisa ga maganar Allah, dukkan mutane sun yi zunubi sun kuma kasa ga darajar Allah, idan kuwa dukkan mutane sun yi zunubi sun kuma kasa ga darajar Allah, kuma idan hakkin zunubi mutuwa ne; ashe hukuncin mutuwa tana rataye a bisa kowane dan Adam, wato ni da kai da dukanmu. Amma sai Allah cikin ikon AllahntakarSa Ya shirya mana hanya ta kubuta daga fushinSa ta wurin aiko da danSa Yesu Kiristi ya zo ya mutu a bisa gicciye domin ya fanshe mu daga hannun Iblis wanda ke mulki bisa dukkan marasa bin Yesu Kiristi, wannan Yesu Kiristi ya rigaya ya yi; abin da ya sa Shaidan yana ta da na sani har yau.
Gicciyen Yesu Kiristi ya sa dukkan abin da ya kawo gaba tsakaninmu da Allah an kawar da shi. A yau; dukkan wanda ya karbi Yesu Kiristi a matsayin mai cetonsa ta wurin ban-gaskiya cikin hadayar da Yesu Kiristi ya yi a bisa gicciye; zai samu rai na har abada; aya goma sha hudu (14) ta Kolosiyawa sura biyu tana cewa: “Ya kuma yanke igiyar nan ta shari’a da ta daure mu da dokokinta, ya dauke ta, ya kafe ta da kusa a jikin gicciyensa, (aya 15 ta ce), ya kwace makaman masarauta da na masu iko, ya kunyata su a fili, da ya yi nasara a kansu a kan gicciye.” Nasara wadda Yesu Kiristi ya samu kuwa ita ce nasarar da muke da ita a bisa Shaidan da dukkan ma’aikatansa.
A karshe, za mu dubi kadan daga cikin Littafin Ishaya 53: 1 – 5 inda yake cewa: “Wane ne ya gaskanta abin da muka ji? Ga wane ne kuma hannun Ubangiji ya bayyana? Gama ya yi girma a gabansa kamar dashe mara kwari, kamar saiwa a cikin busashiyar kasa, ba shi da wani fasali, sa’adda mun dube shi, ba wani jamali gare shi da za mu so shi ba. Abin raini ne, yasashe ne a wurin mutane; mai bakin ciki ne, ya saba da cutuka, aka raina shi kamar wanda mutane suka kawar masa da fuska, mu kuma ba mu maishe shi wani abu ba. Lallai da kayan cutarmu ta nauyaya, ya dauki bakin cikinmu; amma muka maishe shi bugagge, dukakke na Allah, mai shan wuya ne. Amma sabili da laifufffukanmu ne aka yi masa rauni, aka kuje shi domin kura-kuranmu; horo mai kawo lafiyarmu a kansa yake, ta wurin dukansa da ya sha mun warke.” Wannan ba karamin taimako ne muka samu ba.
Gicciyen Yesu Kiristi Ya kawo mana warkarwa daga kowace irin cuta ta jiki ko kuwa ta ruhu. Shaidan bai san wannan asirin ba, a ganinsa idan ya gama da Yesu Kiristi, shi ke nan ya samu mutum na har abada, amma ba san asiri da kuma shirin Allah domin ceton mutum ba. Ina so mu yi tunani sosai game da irin rayuwar da muke yi a wannan zamani. Yaya tsakaninmu da Allah yake? Sai mu lura da yadda muke tafiya.
Ubangiji Allah Ya bishe mu cikin wannan tafiya ta ban-gaskiya. Allah Ya taimake mu, amin.