Ilimantar da matasa da inganta rayuwarsu ne burin kungiyarmu – PREHYA
Wata kungiya mai zaman kanta wacce ba ta gwamnati ba, mai kula da harkokin lafiya da rajin tallafawa matasa wajen farfado da rayuwarsu ta ‘Pioneers Reproductibe Health and Youth Association’ (PREHYA) ta sha alwashin ganin ta mayar da yara 900 marasa gata makarantun boko nan da karshen wannan shekara. Malama Jamila Salihu, ita ce jami’a […]
Wata kungiya mai zaman kanta wacce ba ta gwamnati ba, mai kula da harkokin lafiya da rajin tallafawa matasa wajen farfado da
rayuwarsu ta ‘Pioneers Reproductibe Health and Youth Association’ (PREHYA) ta sha alwashin ganin ta mayar da yara 900 marasa gata makarantun boko nan da karshen wannan shekara.
Malama Jamila Salihu, ita ce jami’a mai kula da shirin na wannan kungiyar ce ta bayyana hakan a lokacin da take zantawa da Aminiya, inda ta ce suna shiga lunguna da sako suna zakulo ‘ya’yan talakawa su na ba su tallafin karatu don ganin su sami ilimin zamani.
Jamila Salihu, ta kuma ce wannan kungiya tasu ta yi rijista da hukumar nan ta CAC a shekara ta 2007, dan ganin cikar burinta wajen taimakawa dan inganta sha’anin lafiya da ilimi da kuma samarwa da matasa aikin yi tare da samar da tsari mai inganci a tsakanin al’ummar karkara.
Wannan kungiya ta PREHYA tana aiki ne a jihohi shida na Arewa maso Gabashin Najeriya, amma tana da babban ofishinta ne a karamar hukumar Misau ta jihar Bauchi, sannan kuma tana da ofisoshi guda biyu da suke aiki daya da Yobe daya kuma a Borno. Kuma tana da hadin gwiwa da ma’aikatun gwamnati daban-daban kamar ma’aikatun mata da ta lafiya da kuma ta harkokin addini har ma da albarkatun ruwa, da bangaren kula da karatun manya.
Har ila yau Malama Jamila Salihu, ta kara da cewa bayan nan suna da alaka mai karfi tsakaninsu da hukumar nan mai yaki da cuta mai karya garkuwar jiki ‘Agency for Control of HIb AIDS’ da masu kula da Tarin Fuka sanna kuma da kungiyoyi na kasashen waje wadanda za su rika taimakawa idan aka bullo da wani aiki da zai taimaka wajen inganta rayuwar al’umma.
A cewar jami’ar shirin, yanzu haka wannan kungiya tasu tana gudanar da wasu aikace-aikacen ta a jihohi 3 na shiyar Arewa maso Gabas da suka hada da Bauchi da Borno da kuma Yobe, sannan kuma akwai wasu ayyukan raya kasa da suke yi wa al’umomin kananann hukumomin Misau da Gamawa da Itas Gadau da Bauchi da Jama’are da Darazo da Katagum duka a Jihar Bauchi. Sanna suke yin wasu a kananan hukumomin Potiskum da Nguru dake jihar Yobe, sai kuma Jere a karamar hukumar Borno.
Daga nan sai ta ce yanzu haka ma kungiyar tasu ta kai wa yara tallafin kayayyakin karatu a kauyen Beti dake karamar hukumar Misau a jihar Bauchi sannan ta ce akwai cibiyoyin ilimi 20 a wannan gari kuma kowacce cibiya ana son yara 45 ne, inda kafin karshen wannan shekara suna son bai wa yara 900 ilimi ta bangaren yaki da jahilci.
Sannan a karshe ta ce za a koyar da su ne tsawon watanin tara a karkashin (NEI) ‘Northern Education Initiatibe’ wadanda su suka bada kayayyakin karatun da ake raba musu, amma bayan sun gama watanin tara duk mai son ya ci gaba da karatu za a nemi makarantar da ta fi dacewa da shi.