Ilimantar da yara ginshikin samun al’umma tagari ce – Hajiya Safiya Mahmoud Baba Bichi
Aminiya ta samu tattaunawa da Hajiya Safiya Mahmoud Baba Bichi, Shugabar makarantar Baba Memorial Schools da ke garin Bichi ta Jihar Kano. A hirarta da wakilinmu ta bayyana cewa samar da ingantaccen ilimi ga yara kanana shi ne ginshikin samun al’uma tagari kuma bisa tarbiyya. Tarihina. An haifeni ne a garin Ingawa ta Jihar […]
Aminiya ta samu tattaunawa da Hajiya Safiya Mahmoud Baba Bichi, Shugabar makarantar Baba Memorial Schools da ke garin Bichi ta Jihar Kano. A hirarta da wakilinmu ta bayyana cewa samar da ingantaccen ilimi ga yara kanana shi ne ginshikin samun al’uma tagari kuma bisa tarbiyya.
Tarihina.
An haifeni ne a garin Ingawa ta Jihar Katsina a shekara ta 1963 inda na yi karatun allo wajen marigayi malaminmu Malam Bawa. daga nan ne na shiga firamare ta Ingawa sannan na wuce sakandaren gwamnati ta Unguwar Kawo da ke Jihar Kaduna a lokacin ana tsohuwar Jihar Kaduna.
Bayan na kammala sakandare sai na shiga Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Kaduna (Kaduna Polytechnic) inda na samu horo kan aikin magatakarda kafin daga bisani na koma Jami’ar Bayero da ke kano watau (BUK).
Abin da ya sa na kafa makaranta:
Abin da yasa na yi tunanin kafa makaranta shi ne bayan mun baro Abuja da zama muka koma garin Bichi mahaifar maigidana sai na so in kai yarana makaranta domin su ci gaba da karatu amma babu makaranta mai zaman kanta. Kawai sai na kafa sabuwar makaranta wacce aka sanya wa suna “Baba Memorial Schools” a shekara ta 2003 kuma na fara da yara na biyu sai daya daga makwabtanmu na dauki malami daya da wani mutum guda a matsayin mai kula da wuri muka ci gaba da tafiya a haka.
Ana nan ana tafiya da wadannan dalibai uku sai abin ya fadada mutane suka yi ta kawo ‘ya’yansu kamar da wasa wanda a yau Allah cikin ikonSa muna da dalibai dari bakwai da malamai arba’in masu koyar wa da kuma ma’aikata na yau da kullum guda goma. Sannan ya zuwa yanzu mun kai ga mataki na karamar sakandare bayan sashen raino da matakin firamare.
Muhimmancin ba da ilimi tun daga tushe:
Bai wa yara kanana ilimi shi ne mataki na farko da yakamata a dauka domin ilimantar da kananan yara shi ne ginshikin samun al’umma mai nagarta wadanda za su ba da gudummawa mai kyau ga kasa da al’umma bisa sanin yakamata.Don haka ne muke aiki tukuru wajen tabbatar da cewa yaran da ke karatu a makarantunmu sun samu ginshiki mai karfi wajen ci gaba da neman ilimi walau a cikin kasa ko kasashen waje.
Yanzu haka wasu daga cikin daliban da muka yaye sun samu guraben karatu a jami’oi kamar su ABU Zariya da Jami’ar Bayero ta Kano da Kwalejojin ilimi har ma da wasu da suka ketara zuwa kasar Rasha wanda hakan abin a yaba ne kwarai da gaske. Don haka lallai ba da limi tun daga tushe abu ne mai matukar amfani.
kalubalen da muke fuskanta:
Duk da cewa muna kokari wajen ba da ingantaccen ilimi a makarantarmu, amma muna fuskantar kalubale wajen wasu daga cikin iyayen yaran da ke karatu a makarantarmu wajen jan lokacin biyan kudaden da suka kamata a biya kamar yadda kowa ya sani, amma muna aiki dare da rana domin ci gaba da ba da ilimi mai kyau a wannan yanki da muke.
Me ya kamata iyaye su yi?
Yana da kyau iyayen yara da masu rike da yara su tsaya sosai wajen tabbatar da cewa ‘ya’yansu suna samun ilimi walau a makarantun gwamnati ko na masu zaman kansu musamman ganin yadda zamani yake canzawa. Idan mutum ba shi da ilimi yakan fuskanci koma- baya a rayuwa saboda kowa ya san cewa ilimi shi ne gishirin zaman rayuwar duniya kamar yadda ake gani a wannan karni.
Gudummawar da makarantu masu zaman kansu ke bayarwa a fannin ilimi:
Kasancewar abubuwa sun yi wa gwamnati yawa, makarantu masu zaman kansu suna taka muhimmiyar rawa wajen daukar wani kaso na yaran da ke samun ilimi a kasar nan. Sannan wanzuwar ire-iren wadannan makarantu suna kokari kwarai da gaske wajen rage yawan zaman yara babu karatu a tsakanin al’umma don haka akwai gagarumar gudummawar da ake bayarwa ba tare da gajiyawa ba.
Yadda ilimin yara ke bunkasa zamantakewa:
A fannin zamantakewa kuwa, bai wa yara ilimi tun daga tushe yana zamowa alheri, idan yaro yana da ilimi ya san irin zaman da zai yi a cikin al’umma tare da kauce wa fada wa cikin rukunin bata gari masu koyar da munanan halaye. A nan ina kara bai wa iyaye shawara da lallai au kara zage damtse wajen ganin ‘ya’yansu suna cikin rayuwa mai kyau da amfani ga kawunansu da al’ummsa da kuma kasa baki daya.
Batun tallace-tallacen ‘ya’ya mata:
Mafi yawan matsalolin da ake fuskanta a cikin al’umma bangaren yara mata su ne yawaitar tallace-tallace da ake dora masu ba tare da yin la’akari da illolin tallace-tallacen ba. Bisa haka ne a kodayashe muke koyar da darussa da suka shafi tarbiyya da kaucewa fadawa duk wani tarko na matsala musamman ga yara mata tun auna kanana.
Yana da kyau iyaye su daure wajen kai yaransu makarantu ta yadda za su samu ilimi da luggogim zaman rayuwa maimakon dora masu tallace-tallace wadanda daga karshe sukan zamo matsala musamman a wannan zamani da ake ciki. Haka kuma ina fata iyaye za su ci gaba da sanya ido a kan yaransu mata tare da sanin su waye kawayen su ko masu hulda da su da kuma yawaita yin addu’oi na neman tsari kamar yadda aka saba.
Matsalolin Rayuwa:
Duk da cewa ana cikin wani yanayi na zamantakewa, amma yana da kyau iyaye da masu rike da yara su rika daurewa suna amfani da dan abin da ake samu wajen bai wa ‘ya’yansu ilimi tun daga matakin farko domin tabbatar da ganin wadannan yara sun tashi cikin tarbiyya da sanin yakamata. Sannan a rika yin la’akari da yadda suke gudanar da mu’amullar su musamman tsakanin su da kawaye ga mata ko kuma abokai ga yara maza saboda juyawar zamani.
Nasarori na rayuwa:
Babu shakka na cimma kyawawan nasarori na rayuwa wadanda su ne tushen kafa makarantar ba da ilimi ga yara kanana. Na samu kyaututtuka na yabo da lambobi na karramawa daga wurare masu yawan gaske a kan kokarin da muke yi wajen bada ingataccen ilimi ga kananan yara. Haka kuma ina mai matukar jin dadin yadda al’ummar yankin Bichi da kewaye suka fahimci makarantarmu tana kokari wajen ba da ilimi da tarbiyya ga yaransu wanda yanzu mun yi nisa wajen bunkasa wannan makaranta ta yadda za ta cigaba da kasancewa amintacciya a kowane fanni.
Godiya ta musamman:
Ina mika godiyata ga Hukumar da ke duba ayyukan makarantu masu zama kansu ta Jihar kano saboda yadda take dora mu bisa hanya mai kyau a kokarinmu na ba da ilimi a mataki na makarantu masu zaman kai.
Sannan ina godiya ga sauran shugabannin makarantu masu zaman kansu saboda bin dokokin gwamnati da ake yi tare da yin aiki tare wanda ina ganin lallai kwalliya tana biyan kudin sabulu, tare da yin fatam alheri ga sauran abokan arziki irin su Hajiya Tauhida Iman, Shugabar makarantar Saudat Memorial School da Khadijah Hafiz Abubakar mai makarantar Raudar da sauran masu ire-iren wadannan makarantu wadanda lokaci ba zai bari in bayyana su duka ba.
Abubuwan da nake sha’awa:
Babu shakka ina sha’awar yin karance-karance da ba da ilimi ga yara kanana da kuma ziyartar ‘yan uwa domin sada zumunci. Sannan zan yi amfani da wannan dama wajen isar da sako ga maigidana da kuma Daraktan makarantar Baba Memorial Schools watau Alhaji Mahmoud Baba Bichi saboda cikakken goyon bayan da yake ba ni tun daga kafa wannan makaranta har zuwa yanzu, da Alhaji Nura Bello daya daga cikin manyan shugabannin makarantar da shugaban kungiyar iyaye da malamai Alhaji Adamu Ibrahim Nagodi da kuma dukkanin rukunin malaman mu na sashen sakandare da bangaren raino da na firamare tare da fatan Allah Ya kara mana lafiya da zaman lafiya a kasa baki daya.