Ilimi kara wa mace daraja yake a tsakanin al’umma –Asabe Hamma

Hajiya Asabe Hamma Muhammed:ita ce Kwamishinar da ke kula da ma’aikatar harkokin mata ta Jihar Bauchi. Tsohuwar malaman makaranta ce.  Ta shekara 35 tana aikin gwamnati kafin ta yi ritaya a 2003.  A tattaunawarta da wakilinmu, ta yi fashin baki game da matsalolin da ta fuskanta a lokacin da take karatu. Ga yadda tattaunawar ta […]

Ilimi kara wa mace daraja yake a tsakanin al’umma –Asabe Hamma

Hajiya Asabe Hamma Muhammed:ita ce Kwamishinar da ke kula da ma’aikatar harkokin mata ta Jihar Bauchi. Tsohuwar malaman makaranta ce.  Ta shekara 35 tana aikin gwamnati kafin ta yi ritaya a 2003.  A tattaunawarta da wakilinmu, ta yi fashin baki game da matsalolin da ta fuskanta a lokacin da take karatu. Ga yadda tattaunawar ta kasance kamar haka:

Aminiya farko zamu so ki fara da tarihin rayuwa?
Dukkan godiya ta tabbata ga Allah madaukacin Sarki.   Kamar yadda aka sani sunana Hajiya Asabe Hamma Muhammed.  An haife ni a kauyen Duguri da ke yankin karamar Hukumar Alkaleri a Jihar Bauchi.
A shekara ta 1949 na fara makarantar firamare a cikin garin Duguri.   A lokacin da nake karatu, da yawa daga cikin iyayenmu maza ba sa kaunar karatun boko sakamakon haka kadan ne daga cikin yara ke samun zuwa makaranta.
Kusan dukkan malaman da suka koya mana karatu da rubutu turawa ne fararen fata.   Lokacin da na kammala karatun firamare iyayena sun yi bakin ciki da zan ci-gaba da karatu a matakin sakandare.
Ina da shekara 11 na shiga makarantar sakandare.   Da yawa daga cikin wadanda muka fara karatun firamare da su sun watsar sakamakon rashin goyon bayan daga iyaye da sauran ‘yan uwa.
Bayan da na kammala na zarce zuwa makarantar (WTC) Kano makarantar koyon aikin malanta da ke Jihar Kano a lokacin na yi shekara biyar ina karatu kafin na kammala.
Bayan da na koma Jihar Bauchi sai na samu aiki da gwamnatin Jihar Bauchi a matsayar malamar makarantar firamare, aka turani makarantar Shekal na shekara daya a wajen.
Na yi a karamar hukumar Bauchi a sashin ilimi na karamar hukumar na shugabanci makarantu masu dimbin yawa a Jihar Bauchi.
Na yi karatu a Kwalejin ilimi na (COE) Azare da ke yankin karamar hukumar Katagum da kuma makarantu masu yawa da na yi a ciki da wajen Jihar Bauchi.
Kafin na yi ritaya daga aikin gwamnati ni ce jami’ar duba makarantun firamare sama da 11 na yankin karamar hukumar Bauchi.   Tun ina da shekara 11 a duniya nake zaune a cikin garin Bauchi.
Daga nan sai na yi aure ina cigaba da aikina na koyarwa.   Na yi aiki a sassa daban-daban a Jihar Bauchi.   Sai dai na takaita saboda karancin lokaci. Shekara 35 na yi ina aikin gwamnati kafin daga bisani na yi ritaya a shekara ta 2003.
Bayan da na yi ritaya babu abinda nake yi sai hidimar kungiyoyi na mata.   Ina daya daga cikin wadanda suka yi aiki wajen kwamitin mika mulki na shekara ta 2015 bayan da muka kammala aiki sai na gwamnan Jihar Bauchi Barista Mohammed Abubakar ya nadani Kwamishinar ma’aikatar harkokin mata da kananan yara na Jihar Bauchi, kuma yanzu haka ina cigaba da gudanar da aikina.
Wadanne kalubale kika fuskanta a lokacin karatu?
Babbar matsalar da na fuskanta a lokacin karatu ita ce da ma ba a kaunar sanya yara a makaranta, saboda iyayenmu kamar yadda na fada maka sun tsani karatun Boko saboda turawa ne malaman a lokacin komai kyauta ake yi wa mutum. Makaranta kyauta, abinci kyauta, kudin mota kyauta da sauran abubuwa da ake rabawa ga dalibai a makarantu, sabanin yadda yanzu abubuwa ke gudana a makarantu.
Lokacin da nake karatun boko ban yi aure ba amma kuma dukkan gudunmawar da ake bukata maigidana na ba ni domin na samu nasarar gudanar da aiki.  Ba kowane namiji ba ne ke barin matarsa ta yi aikin gwamnati.
Akwai banbanci tsakanin yadda kuka yi karatu da yanzu?
Akwai banbanci sosai tsakanin yadda muka yi karatu a da, da kuma a yanzu.   Lokacinmu kowa yana karatu ne tsakani da Allah sannan kuma babu masu satar jarabawa.  Kafin mutum ya kmamala karatu akwai aikin yi a kasa don haka ilimin ya zamo yana da inganci, sabanin na yanzu.
Da yawa daga cikin wadanda ke karatu yanzu babbar bukatarsu ita ce su mallaki shaidar kammala karatu (satifiket) amma kuma ilimin ba ya da wani inganci a wajen masana.
Akwai mata da matasa a kasar nan wanda suka kamala jami’oi iri-iri amma dan sakandare ya fi su iya turanci da rubutu mai kyau, wasu ma abubuwa da dama basa iya rubutawa daidai amma kuma wai sun kmamala jami’a
Akwai ‘yan mata masu yawa a makarantun kasar nan da jami’oi sun iya kwalliya da daura zani da sa hula mai tsada amma ba sa gane abubuwan da ake karantar da su a makarantu.
Menene sakonki ga ‘yan mata masu tasowa?
 Sakona ga ‘yan mata masu tasowa shi ne su dage wajen neman ilimin zamani da na addini domin yanzu duniya ta sauya, sama da kashi-85-cikin 100 na maza basa kaunar zama da mace jahila wanda babu abinda ta iya sai yawon tsegumi daga nan zuwa can.  Ilimi shi ne babban sinadarin da ke jawo cigaba cikin hanzari ako wacce kasa ta duniya.
Kina da ‘ya’ya nawa a yanzu?
Allah Ya albarkace ni na haifi ‘ya’ya tara mata uku maza shida.   Ina da jikoki sama da 16 da sauran wanda suke cin abinci a karkashina maza da mata da matasa kowa nawa ne.
Wadanne matsaloli ne matan karkara ke fuskanta?
karancin kudaden shiga da rashin ilimin zamani na daga cikin matsalolin da matan karkara ke fuskanta.  Kadan ne daga cikinsu suka san mahimmancin kafa kungiyoyi masu zaman kansu.   Matan Kudu sun fi na Arewa ci-gaba don sun yarda da kafa kungiya.
Mata da maza a yankin arewa mun dogara ne akan gwamnati komai sai ace sai gwamnati, ni ce shugabar kungiyar majalisar mata ta Jihar Bauchi gwamnati tana kokari wajen inganta rayuwar al’umma baki daya.
Lokacin da aka rantsar da ke a matsayin kwamishinan mata a wani hali kika samu ma’aikatar?
Akwai matsaloli sai dai kuma ba masu tayar da hankali ba ne.   Kamar yadda aka sani, mun magance da yawa daga cikinsu sannan kuma ma’aikata na  ba ni dukkan goyon bayan da suka kamata a matsayina na wakiliyar gwamna a ma’aikatar.
Menene sakonki ga mata ‘yan siyasa da suka yi wahala wajen kawo wannan gwamnati ta APC?
 Sakonka ga daukacin matan Jihar Bauchi ‘yan siyasa da sauran matan aure baki daya shi ne mu cigaba da hakuri domin gwamnati tana da manufofi masu kyau na inganta rayuwar al’umma, rashin kudi ya addabemu a gwamnatan ce.
Ina tabbatar maka da cewa ilimin zamani da na addini na kara wa mace daraja a tsakanin al’umma, tun ina malamar makaranta babban burina a rayuwa shi ne in ga mata sun samu ilimi da hanyoyin dogaro da kai. Maza da yawa sun tsani mace mai yawan ba ni-ba ni kullum,  ba ta aikin komai sai zaman kashe zane. Mata ‘yan siyasa kuma ya kamata a rika hadawa da kananan sana’oi domin yanzu duniya ta sauya siyasa ba sana’a ba ce amma kuma wasu sun dauka sana’a ce wanda mutum zai dogara da ita.
Akwai wani shiri da kuke da shi na tallafawa kungiyoyin mata a Jihar Bauchi?
Kwanakin baya gwamnatin jiha ta ba mu gudunmawar wasu kudade inda muka horas da mata sama da-dari bakwai kananan sana’oin kiwon kaji da dinki da sarrafa fulawa da kayan kwalliya na mata. Sakamakon haka mata da dama sun amfana da shirin asassa daban-daban sannan an ba su gudunmawar naira-5,000 a matsayin jari.
Menene sakonki ga al’ummar Jihar Bauchi?
A matsayina na Kwamishinar ma’aikatar harkokin mata da kananan yara ta jihar Bauchi babban sakona shi ne al’umma su cigaba da bada dukkan gudunmawar da ya kamata ga wannan gwamnati ta APC tun daga sama har kasa. Matsalar rashin kudi a tsakanin al’umma duk duniya ne, jihohi da dama a Najeriya ba sa iya biyan albashin ma’aikata amma Jihar Bauchi ta fita zakka, ma’aikata na samun albashi duk karshen wata.
Akwai wata shawara da za ki ba mata masu aikin gwamnati?
Abin da zan fada wa mata masu aiki shi ne wajibi ne su mutunta mazajensu sannan kuma su yi hakuri da yanayin rayuwa.   Duk macen da take son shiga aljanna ya zamo wajibi ta yi biyayya ga mijinta daidai bakin gwargwado. Bayan haka mata a kula da tsaftar gida da sauran kayan abinci. Yara a rika yi musu wanka akan lokaci kafin su tafi makaranta.
Daga karshe akwai matsaloli da kike fuskanta a wannan ma’aikata?
Gaskiyar magana ita ce matsalolin ba su da yawa domin gwamnatin jiha tana ba mu dukkan goyon baya, sai dai akwai wasu lokutan muna son gabatar da wasu shirye-shirye amma rashin kudi na kawo mana cikas. Muna fatar al’umma baki daya za su cigaba da bada dukkan goyon bayan da ya kamata ga gwamnan Jihar Bauchi Barista Mohammed domin na fahimci ya zo da manufofi masu kyau.