Ilimi: Kwankwaso ya taya Abba murnar lashe lambar yabo ta NUT

Kwankwaso ya buƙaci Gwamna Yusuf ya sake jajircewa wajen cimma manyan manufofinsa.

Ilimi: Kwankwaso ya taya Abba murnar lashe lambar yabo ta NUT

Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya taya Gwamna Abba Kabir Yusuf murnar samun lambar yabo ta NUT.

Ƙungiyar Malaman Najeriya (NUT), ta bai wa Gwamna Yusuf lambar yabo don karrama sa wajen inganta harkar ilimi a Kano.

A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X (Twitter), Kwankwaso ya yaba wa Gwamna Yusuf kan jajircewarsa wajen farfado da ilimi a Kano.

Ya ƙarfafa masa gwiwa da ya ci gaba da aiki tuƙuru a kan shirinsa na gyaran ilimi a faɗin jihar.

“Ina taya Mai Girma Gwamna Abba Kabir Yusuf murna bisa lambar yabo ta NUT saboda nasarorinsa a ɓangaren ilimi,” in ji Kwankwaso.

Haka kuma, ya buƙaci Gwamna Yusuf da ya ƙara zage dantse don cimma manyan manufofinsa na gyaran ilimi.

An bai wa gwamnan lambar yabon ne a lokacin bikin Ranar Malamai ta Duniya ta 2024 da aka gudanar a Dandalin Eagle da ke Abuja.

Bikin ya samu halartar malamai da shugabannin ilimi daga sassa daban-daban na Najeriya domin karrama manyan nasarorin da ɓamgaren ilimi ya samu.

An karrama Gwamna Yusuf da lambar yabo ta NUT saboda ƙoƙarinsa na ceto ilimi a Jihar Kano, wanda ya faɗa mawuyacin hali tsawon shekaru.

Lakurawa sun kashe ma’aikatan kamfanin Airtel 3 a Kebbi

Matashi ya kashe mahaifiyarsa don yin tsafi a Kuros Riba

DSS ta ceto mutum 4 da aka sace a Sakkwato

2025: Wutar lantarkin Najeriya ta ɗauke gaba ɗaya