Ilimi na kara wa mace daraja – Hajiya Ummulkairi Aminu

Hajiya Ummulkhairi Aminu Muhammed Alkali ma’aikaciya ce a bankin Sterling da ke Bauchi, wakilinmu ya tattauna da ita, inda ta bayyana kalubalen da ke cikin aikin banki. Ta yi bayanin yadda take hada aikin banki da kuma da lura da iyali.Ga yadda hirar ta kasan ce kamar haka.   Tarihin Rayuwa:Dukkan godiya ta tabbata ga […]

Ilimi na kara wa mace daraja – Hajiya Ummulkairi Aminu

Hajiya Ummulkhairi Aminu Muhammed Alkali ma’aikaciya ce a bankin Sterling da ke Bauchi, wakilinmu ya tattauna da ita, inda ta bayyana kalubalen da ke cikin aikin banki. Ta yi bayanin yadda take hada aikin banki da kuma da lura da iyali.Ga yadda hirar ta kasan ce kamar haka.

 

Hajiya Ummulkhairi AminuTarihin Rayuwa:
Dukkan godiya ta tabbata ga Allah madaukacin Sarki.   Sunana Hajiya Ummulkhairi Aminu Muhammed Alkali, an haifeni a cikin garin Bauchi, na yi aure ina da shekara 20 a duniya yanzu kuma ina da shekara 40 da wani abu a duniya.
Na yi firamare a makarantar Shekal da ke Bauchi daga bisani na zarce zuwa Kwalejin ’yan mata da ke garin Azare a karamar Hukumar Katagum bayan na kammala sai na shiga Kwalejin Kimiyya da Fasaha da ke Bauchi (Federal Polytechnic, Bauchi) na samu babban satifiket a fannin aikin banki yanzu haka ina ci-gaba da karatu a Jami’ar Abubakar Tafawa balewa da ke Bauchi.
Har yanzu ina cigaba da neman ilimin addini da na zamani domin Hausawa sun ce gemu ba ya hana neman ilimi sannan kuma babu wata al’umma da za ta samu cigaba da bunkasar tattalin arziki sai da ilimi domin shi ne gishirin zaman duniya.
Bayan na kammala ina zaune sai aka ba ni shawara na nemi aiki da sabon bankin nan mai suna Interprise tunda sun bude reshe a Bauchi kamar wasa sai na rubuta takardar neman aiki daga bisani aka daukeni aiki a bankin.
Muna cikin aiki sai bankin Heritage ya sayi Interprise sai na sake komawa bankin Sterling da ke Bauchi kuma har yanzu anan nake cigaba da aiki. Wannan shi ne tarihin rayuwata a takaice.
Bayan ina aikin banki ina kuma taba kasuwanci daidai bakin gwargwado domin ba na kaunar na ga mace tana zaman kashe zani a tsakanin al’umma ,akwai albarka sosai a kasuwanci idan mutum ya yi hakuri.
Ina sayar da sabulai irin na mata da zannuwa da shadda masu tsada da sauran kayan kamshi na daki da sauransu.
Waddne kalubale kika fuskanta a lokacin da kike karatu?
Gaskiya babu wani kalubale da na fuskanta a lokacin da nake karatu sai dai abubuwan da baa rasawa na yau da kullum amma mijina Alhaji Abdullahi Abubakar Malami ya ba ni dukkan goyon baya a lokacin da nake karatu kuma har yanzu yana cigaba da ba ni goyon baya game da mahimmancin neman ilimin addini da na zamani.
Yaya kike hada aikin banki da kula da iyali:
Gaskiyar magana ita ce aikin banki yana da matukar wahala a wajen mace wadda take da miji domin aikin yana cin lokaci sosai kuma ba kowace mace ce za ta iya aikin ba don za ki fita tun da safe har zuwa yamma saboda haka aikin yana da matukar wahala sosai.
Yanzu ’ya’yanki nawa?
Na haifi ‘ya’ya hudu amma biyu sun rasu saura biyu mace da na miji kuma dukkansu suna karatun Boko-da na addini suna kokari sosai a makaranta kamar yadda nake bincike bayan sun dawo daga makaranta.
Tun ina yarinya nake son karance-karance da duba littattafan addini da na zamani.  ilimi na daya daga cikin abubuwan da ke karawa mace daraja a wajen al’umma.
Binciken da masana sun gano cewa sama da kashi 85 daga cikin 100 na Hausawa basa kaunar zama da mace wanda ba ta iya rubutu da karatu ba.
Menene sakonki ga ’yan mata masu tasowa?
Babban sakona ga ‘yan mata masu tasowa shi ne su zamo masu juriya da hakuri a rayuwa sannan kuma su dage wajen neman ilimi domin yanzu duniya ta sauya mata masu ilimi sun fi daraja a wajen al’umma.   Aure ba ya hana karatu sannan kuma karatu ba ya hana aure.
Ina bada shawari ga ‘yan uwa mata a dage sosai wajen neman ilimi sannan kuma a rungumi kananan sana’oi na cikin gida.
Me ke jawo mace-macen aure a tsakanin Hausawa?
Rashin hakuri na daya daga cikin abubuwan da ke jawo wa mace-macen aure a kasar Hausa bayan haka sai talauci da ya addabi mutanen birni da karkara akwai dimbin mutane da ba sa iya cin abinci sauuku a rana sai kuma rashin ilimi a tsakanin wasu matan da maza.
Amma babban abin da ya kamata kowa ya sani shi ne zamantakewar aure yana bukatar sai kowa ya yi hakuri da abokin zamansa, dole sai wani ya yi ba daidai ba ga dan uwansa idan an ciza sai a hura.
Ina bada shawari ga maza don Allah idan suka fahimci mace tana son neman ilimi yakamata a ba ta dukkan goyon bayan da ya kamata domin idan mace daya ta samu ilimi, mutane da dama za su amfana sabanin maza.
Wace shawara za ki ba mata masu son aiki a banki?
Abin da zan fadawa mata masu son shiga aikin banki shi ne dole su fahimci cewa aikin yana cin lokaci sannan kuma lokaci yana da matukar tsada a wajen ma’aikacin banki domin Asabar da Lahadi ne kawai wasu ke samun hutawa da sauran kula da iyali a wajen mace wanda take da miji.
Na shiga aikin banki ne domin na samu kudi na kyautatawa marayu da masara galihu dake tsakanin al’umma. Maganar tara abun duniya ba shi ne nake dubawa ba kullum bukata shi ne na samu abin da zan yi kyauta ga wanda yake cikin mawuyacin hali.
Alheri na daya daga cikin abubuwan da ke kara wa mutum farin jini a tsakanin al’umma, rowa tana kara wa mutum bakin jini saboda haka ina fatar mata za su zamo masu kyauta da son taimakon marasa karfi da ke tsakanin al’umma.
Babban abinda yake faranta mini rai a rayuwa shi ne mutum ya zo neman taimako a wajena ya koma da farin ciki abin da na fi so kenan a rayuwa.
Wadanne matsaloli ne mata ma’aikatan banki suke fuskanta a Najeriya?
Babbar matsalar da mata ma’aikatan banki suke fuskanta a Najeriya ita ce rashin lokaci sannan kuma ba a komawa gida akan lokaci. Wani lokacin mace za ta kai har karfe takwas na dare tana aiki a ofis. Mace da take da miji wannan babban kalubale ne a gabanta.
Menene sakonki ga mata game da mahimmancin kula da iyali?
Babban sakona ga mata shi ne a rika tsafta sannan kuma a yi wanka ga yara sau uku a rana.   A rika wanke kayan abinci da kayan sawa.   Akwai wasu daga cikin mata wanda kazamai ne idan ka je gidajensu ba za ka iya cin abincinsu ba saboda kazanta mace dole sai da kwalliya.
A rika wanke ban daki da sauran kayayyakin amfanin cikin gida.   Mace mai tsafta a tsakanin al’umma kowa so yake ya zauna kusa da ita.
A karshe menene sakonki ga ‘yan Najeriya?
Babban sakona ga ‘yan Najeriya shi ne mu cigaba da addu’a ga shugabanni domin kowa ya san halin da ake ciki a yanzu na rashin kudi da tsadar rayuwa.  Addu’a ita ce mafita ga matsalolin da muke fuskanta a kasar nan.
Kowa ya gyara tsakaninsa da Allah idan muka yi haka ina tabbatar maka da cewa za mu fita daga cikin matsalolin da suka addabi kasar nan Allah Ya ba mu zaman lafiya da kwanciyar hankali a Jihar Bauchi da ma Najeriya baki daya.