Ilimi ne darajar mace ba iya daura dankwali ba – Yalwa Abubakar Tafawa balewa
Babbar sakatariyar hukumar yaki da jahilci ta jihar Bauchi (Aduit And Non Formal Education) kuma diya ga Firayiministan Najeriya marigayi Sa Abubakar Tafawa balewa, Hajiya Yalwa Abubakar, ta bayyana cewa ilimin ’ya’ya mata na daga cikin abubuwan da ya kamata a bada kulawa ta musamman, domin babu wata al’umma da za ta samu cigaba da […]

Babbar sakatariyar hukumar yaki da jahilci ta jihar Bauchi (Aduit And Non Formal Education) kuma diya ga Firayiministan Najeriya marigayi Sa Abubakar Tafawa balewa, Hajiya Yalwa Abubakar, ta bayyana cewa ilimin ’ya’ya mata na daga cikin abubuwan da ya kamata a bada kulawa ta musamman, domin babu wata al’umma da za ta samu cigaba da kwanciyar hankali sai da ilimi, saboda shi ne sinadarin da yake jawo cigaba cikin hanzari a tsakanin al’umma.
Ta kara da cewa, tana ’yar shekara 14 a duniya aka cire ta daga makaranta aka yi mata aure, amma bayan ta yi auren ta cigaba da karatu har zuwa wannan lokaci, “saboda haka zan cigaba da shiga kafafen watsa labarai domin wayar da kan iyaye game da mahimmancin karatun ’ya’ya mata,’’ inji ta.
Hajiya Yalwa, wadda ta bayyana haka a lokacin da take zantawa da wakilinmu a ofishinta da ke Bauchi, ta kara da cewa, “kowa ya san cewa ilimin ’ya’ya mata ya fi komai mahimmanci a rayuwar wannan al’’umma. Kuma sama da kasha 85 cikin 100 na maza sun fi son auren mace wadda take da ilimin addini da na zamani, domin duniyar yau ana gasa ne da ilimin da mace take da shi, ba yawan daura dankwali ba.’’
“Duk inda ma ce ta kai da rangwada da jiji da kai, matukar ba ta iya karatu da rubutu ba, to tabbas za ta dauki tsawon lokaci kafin ta samu mijin aure, saboda haka ko da an yi aure a cigaba da karatu, domin gemu ba ya hana neman ilimi,’’ inji Yalwa Abubakar.
Ta ci gaba da cewa, akwai wadansu daga cikin maza da zarar sun auri mace babu abin da suke bukata sai ta zauna a gida ta cigaba da girka wake da shinkafa, maganar neman ilimi addini da na zamani ba ya gabansu. “Kuma yin haka babbar kuskure ne, domin kamar yadda neman ilimi ya zamo wajibi ga namiji haka ya zamo wajibi ga mace, don haka za mu cigaba da gwagwarmaya domin nuna wa al’umma illolin da ke tattare da jahilci.’’
Daga karshe, ta yi amfani da wannan dama inda ta bayyana godiyarta ga Allah bisa nasarorin da aka samu, “tun lokacin da aka bude makarantun yaki da jahilci a jihar Bauchi akwai da yawa daga cikin mata da yanzu suke iya karatu da rubutu sakamakon wayar musu da kai da muke yi ta kafafen watsa labarai na ciki da wajen jihar Bauchi.’’
“Abun bakin ciki ne a rika ganin mata suna zaune babu karatu, babu aikin yi, sai yawon tsegumi daga nan zuwa can, muna fatan mata za su sauya tunaninsu,’’ inji Yalwa Abubakar.