Ilimi ne gaba da komai a rayuwa – Hajiya Maimuna Bala

Tarihina: Sunana Hajiya Maimuna Mohammed Bala. An haife ni a  Zuru da ke Jihar Kebbi a ranar 5 ga Mayun 1954. Na shiga makarantar firamare a 1958 mai suna L.G.A Primary School, Zuru daga nan na wuce  Kwaleji da ke Katsina daga 1966 zuwa1968.   Da ma an kai mu a matsayin wucin gadi ne bayan […]

Ilimi ne gaba da komai a rayuwa – Hajiya Maimuna Bala

Tarihina:

Sunana Hajiya Maimuna Mohammed Bala. An haife ni a  Zuru da ke Jihar Kebbi a ranar 5 ga Mayun 1954. Na shiga makarantar firamare a 1958 mai suna L.G.A Primary School, Zuru daga nan na wuce  Kwaleji da ke Katsina daga 1966 zuwa1968.   Da ma an kai mu a matsayin wucin gadi ne bayan shekara biyu sai na koma Kwalejin ’Yan mata (WTC) da ke Birnin Kebbi inda na samu takardar shaida malanta ta mai daraja ta biyu.

Kafin jarrabawa ta fito sai na fara koyarwa a wata firamare a Zuru a tsakanin 1970  zuwa1971. Da sakamakon jarrabawa ya fito sai na wuce Kwalejin Horar da Malamai ta Kano a 1972 zuwa 1975.  Ina Kano kafin in gama makarantar sai na yi aure. Ina gidan mijina a 1978 sai na samu shiga Jami’ar Usman danfodiyo ta Sakkwato inda na samu digiri na farko a Ingilishi.  Daga nan na wuce hidimar kasa (NYSC) inda aka tura ni Kwalejin WTC Bodinga.  Ina wannan makaranta kafin in gama hidimar kasa sai hukumar ilimi ta Jihar Sakkwato ta ba ni shugabar rikon kwarya a makarantar. Ina shugabancin rikon kwarya sai Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Sakkwato ta ga abin da na yi ya yi kyau kwarai na nuna bajinta, ban kare hidi,ar kasa ba sai suka tura ni Makaranta GGSS Rabah a matsayin Shugabar Makarantar. Daga nan sai aka kai ni WATC,  Gusau a 1983.

A 1989 sai aka koma da ni Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Sakkwato.   Ina Ma’aikatar Ilimin sai aka samu wata matsala a Rabah sai aka sake tura ni makarantar a matsayin shugabar makarantar. Wata uku kacal na yi a makarantar na sake mayar da ita bisa hanya madaidaiciya.

Daga nan sai aka koma da ni inda nake aiki wato Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Sakkwato. Ina wannan ma’aikata sai aka shirya yin jarrabawa ta daukar Shugabar Kwalejin GGC Sakkwato. Ina cikin wadanda suka yi jarrabawar, Allah Ya ba ni sa’a na ci jarrabawar.

A 1991 da aka kirkiro Jihar Kebbi sai na koma jiharmu, sai aka tura ni Ma’aikatar Kimiyya da Fasaha a matsayin Mataimakiyar Darakta mai kula da sashin jarrabawa. Ina nan a wannan ma’aikata sai matar Gwamna Abubakar Musa, ta nuna tana son jami’a mai kula da tsare-tsare a Ma’aikatar Kula da Harkokin Mata sai aka tura ni ma’aikatar. Bayan nan a 1994 sai aka tura ni ofishin Gwamna, a matsayin Daraktar Mulki mai kula da Al’amuran Siyasa.  A  1996 aka ba ni Kwamishinar Ruwa da Albarkatun kasa. Ni ce kwamishina ta farko a wannan ma’aikata da aka kirkiro a Jihar Kebbi.   Daga nan sai aka tura ni Ma’aikatar Al’amuran Mata a matsayin kwamishina a tsakanin 1998  zuwa 1999. Na yi digiri na biyu a shekarar 2002 a Sakkwato.

Bayan  na gama aikin kwamishina, a matsayina na ma’aikaciyar gwamnati sai na rubuta wa gwamnati na koma bakin aikina, daga nan sai suka tura ni Ma’aikatar Ayyuka  a matsayin Daraktar Harkokin Mulki, daga nan sai aka ba ni  matsayin Babbar Sakatariya inda na zauna a wadannan ma’aikatu kamar haka:   Na zauna a   Ma’aikatar  daukar Ma’aikata da Ma’aikatar Ruwa da Ma’aikatar Lafiya da Ma’aikatar Matasa da Wasanni.  Na yi ritaya a matsayin Babbar Sakatariya a Ma’aikatar Ilimi ta Jihar  Kebbi  a shekarar 2010.

Bayan na yi ritaya daga aiki a 2010 sai Mai girma tsohon Gwamnan Jihar Kebbi, Alhaji Sa’idu Usman Nasamu dakingari ya nada ni Mai ba shi Shawara ta Musamman kan Harkokin Ilimi.

kalubalen da na fuskanta:

Akwai lokacin da aka tura ni makarantar mata ta Rabah inda na tarar da matsala kwarai da gaske. Akwai rashin da’a da abubuwa wadanda ba su dace ba a makarantar. Allah Ya taimake ni makarantar ta koma daidai; amma kafin in gyara makarantar na fuskanci kalubale sosai musamman a wajen malamai da dalibai. A rayuwata  ban taba samun haka ba, har yanzu da muke yin wannan hira.

Haka kuma a Gusau, koda na je makarantar na iske dalibai na fada a tsakaninsu,  su ma malamai na fada a tsakaninsu, kuma ranar da na isa makarantar na tarar da tana ci da wuta. Hankalina ya tashi sosai yaran makarantar manya-manyan ’yan mata ne ko da na je suna ganin kamar ba zan iya ba, amma cikin ikon Allah, cikin kankanen lokaci na gyara makarantar ta koma daidai amma sai da na shekara 7 kafin a canja ni.

Abin da ba zan manta da shi a rayuwa ba:

Gaskiya abin da ba zan taba mantawa da shi ba wanda bai shafi aikina ba shi ne rasuwar mahaifiyata, wadda ta ba ni goyon baya na yi karatu, ta nuna mini amfanin karatu, na kuma ga amfaninsa.

Shawara ga iyaye:

Shawarar da zan ba iyaye musamman mata ita ce, su koya wa ’ya’yansu neman ilimi da rayuwa tagari, wanda ko iyayen suna da rai ko ba su da rai suna iya zama da kowa.  Sannan su dora su a kan sana’o’i. Bai dace ba a ce mace sai ta je tana roko ko yin bara don biya wa kanta wata bukata, amma idan tana da iliminta ba za ta wulakanta ba.  Ko ba ta yin aiki, akwai sana’o’i wadanda in ba ka da ilimi ba za ka yi su ba.

Ina kara yin kira ga mata su koyi sana’a, domin taimaka wa ’ya’yansu  da mazansu, idan iyaye ba su nuna wa ’ya’yansu ilimi na da amfani ba, su ma ba za su damu da ilimin ba.

Mace mai ilimi za ta iya kula da gida da mijinta da yaranta da makarantarsu da lafiyarsu da tsabtar gida.  Idan ba ta da ilimi ba za a samu haka ba, komai sai ka ga ana ta dora wa maigida, abin da bai kai ya kawo ba sai ka ji uwargida na cewa a jira maigida  ya dawo, shi kuma yana can wajen neman abinci  ko yana ofis ko yana kasuwa. Da kyar za ka ga  mace mai ilimi ’ya’yanta ba su da tsari da koshin Lafiya.

Abin da na fi sha’awa a rayuwa:

Ni mace ce mai sha’awar rubuce-rubuce da karance-karance, a kan haka ne ma tun ina sakandare na fara rubuta littafi. Littafi na farko da na fara rubutawa shi ne Sadik and Ten Regulations. Na kaddamar da shi ne a 1991. Na samu alheri sosai domin a lokacin Naira dubu 100 kudi ne masu yawa.  Daga baya na rubuta littattafai  tara na Ingilishi da Hausa. Daga cikinsu akwai Dikko dan Maiceda da Kada Mai Rikida da Kowa Na Son Nagari da Wasiyyar Sarki Gambo da kuma ’Ya’yansa. Daga cikin na Ingilishi akwai  A Joy in The Cradle da He Who Laugh Last sai kuma Career berses for Unibersal Basic Education dukan wadannan littattafai na Ingilishi da na Hausa, suna koyar da halaye nagari, yara su kasance ’ya’ya nagari su bar miyagun halaye kamar shan giya da zina da caca da luwadi da rashin da’a ga iyaye ko shugabanni da shan taba da sauran kayan maye. Kuma suna koya wa yara su gyara Turancinsu.  Yanzu haka ina nan ina rubuta wasu amma ban sa musu suna ba, domin sun shafi tarihin Annabawa 5 ne.

kasashen da na ziyarta:

kasashen da na taba zuwa su ne wani kwas a International Training Centre, Worthing, kasar Ingila. Kuma na je Brazil da Indiya da Sudan da Nijar da Saudiyya da Suwizilan.  Iyakar kasashen da na taba zuwa a kasashen waje ke nan.

Zamantakewa da maigida:

Lokacin da nake tare da maigidana ba a jin kanmu, don hatta cefanen gida ni nake yi, ba na jiran sai ya kawo. Duk abin da na ga zai taimaka mana da ni da shi da ’ya’yanmu, nakan yi ne kai-tsaye ba tare da sai na jira ya yi ba. Haka abin yake a bangaren sutura, ni nake daukar nauyin komai, suturata da ta yarana da har shi kansa maigidan nawa. Tunda Allah Ya hore mini, ba na jira in ce sai ya yi. Sai dai idan ya kara yi mana, to sai mu karba a matsayin kari da kuma kyautatawa daga wajensa. Wannan ta sa mun yi zama na amana da aminci da soyayya ba ka sanin cewa akwai wata matsala.

Haka kamar gyaran gida  ko wani wuri ya lalace a cikin gida ko gyaran kujeru ban tsayawa in ce lallai sai ya yi ba, amma kuma duk abin da na yi a gida ba wanda yake sani hatta ’ya’yanmu ban nuna musu cewa ni na yi. Sai dai in nuna maigida ne ya yi ko kuma in nuna cewa hada gwiwa muka yi da shi muka yi. Wannan ya karfafa dankon zamantakewa a tsakaninmu, kuma mun yi zama na amana.