Ilimi ne kadai zai gyara al’umma – Bamidele

Shugaban kungiyar da ke rajin canja halaiyar dan adam kan dabi’u masu kyau, Bamidele Dabid Mann ya ce muddin al’umma suka ginu a kan dabi’ar neman ilimi to babu shakka za a samu al’umma ta gari a kasar nan. Bamidele  wanda ya yi furucin ne a wata tattaunawa ta musamman da ya yi da wakilin […]

Ilimi ne kadai zai gyara al’umma – Bamidele

Shugaban kungiyar da ke rajin canja halaiyar dan adam kan dabi’u masu kyau, Bamidele Dabid Mann ya ce muddin al’umma suka ginu a kan dabi’ar neman ilimi to babu shakka za a samu al’umma ta gari a kasar nan.

Bamidele  wanda ya yi furucin ne a wata tattaunawa ta musamman da ya yi da wakilin Aminiya a ofishinsa da ke Abuja ya bayyana cewa ya zama wajibi gwamnati ta rika yin amfani da shugabannin al’umma wajen cimma burin samar da ilimi a kasar nan.

“Idan jama’a suka yi watsi da dabi’ar halin-ko-in-kula suka mayar da hankulansu wajen neman ilimi to babu shakka za a samu al’umma ta gari wacce a za a yi alfahari da ita”. Inji shi

Ya bayyana cewa rashin isassun kudi na daya daga cikin kalubalen da ke fuskantar bangaren ilimi a kasar nan.

Ya bayyana cewa ya zama wajibi gwamnati ta ware isassun kudi da bangaren ilimi tare da tabbatar da kudin an kashe su ta hanyoyin da suka kamata.

Ya dage a kan cewa muddin gwamnati za ta ware kudi amma ba za ta bi diddigin kudin ba to ilimi zai ci gaba da tabarbarewa a kasa baki daya.

Ya bayyana cewa rashin ci gaba da gudanar da ayyukan da gwamnatocin da suka shude suka fara shi ma wata matsala ce da ke ci wa ilimi tuwa-a-kwarya.

Saboda haka sai ya shawarci gwamnati da kada ta yi watsi da ayyuka masu inganci da gwamnatocin baya suka fara don cimma burin da aka sanya a gaba.

Ya bayyana cewa ya kafa kungiyar ne yayin da ya fahimci irin dabi’ar da jama’ar Najeriya suke da ita kan ilimi.

Ya bayyana cewa kungiyar ta himmatu wajen ganin an samar da ingantaccen ilimi kyauta ga daukacin ’yan Najeriya.