Ilimi shi ne gishirin rayuwa – Hajiya Hauwa Abubakar Muhammad

Zamu so mu san cikaken sunanki da takaitaccen tarihin rayuwarki?Sunana Hajiya Hauwa Dokta Abubakar Muhammad Sakkwato.   An haife ni a shekarar 1963.   Na yi karamar makaranta a St. Micheal Kaduna, na yi babbar makaranta a Sakkwato a wancan lokacin amma yanzu tana karkashin Jihar Zamfara watau makarantar ’yan mata da ke garin Kwatar-kwashi.  Na koma […]

Ilimi shi ne gishirin rayuwa – Hajiya Hauwa Abubakar Muhammad
Ilimi shi ne gishirin rayuwa – Hajiya Hauwa Abubakar Muhammad

Zamu so mu san cikaken sunanki da takaitaccen tarihin rayuwarki?
Sunana Hajiya Hauwa Dokta Abubakar Muhammad Sakkwato.   An haife ni a shekarar 1963.   Na yi karamar makaranta a St. Micheal Kaduna, na yi babbar makaranta a Sakkwato a wancan lokacin amma yanzu tana karkashin Jihar Zamfara watau makarantar ’yan mata da ke garin Kwatar-kwashi.  Na koma makarantar horon dalibai da ke Sakkwato da na gama sai na tafi bautar kasa.  Daga nan na yi digiri na farko a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, bayan haka kuma na kara komawa digiri na biyu. Daga nan ne na fara aiki a Ma’aikatar ilimi da ke Sakkwato (Ministry of Ecdducation) har na kawo matsayin Darakta.   Ina da aure da ya’ya.
Menene dalilin wannan aiki naki?

Ina wannan aiki ne saboda mu koya wa malammai makamar aikin.  Muna zagayawa makarantu don mu ga halin da suke ciki, mu kuma bada shawarar yadda za su tafiyar da aikin su yadda ya kamata.  A ra’ayina duk wani gyara da za ay i na al’umma sai an fara da ilimi, wannan abu ne ya sa na zabi wannan aikin.

Ya kika ga yanayin ilimin mata a arewa?
A gaskiya idan za a kwatanta da inda muka fito zuwa yanzu an samu cigaba sosai a fannin ilimi, ba kamar da ba, da iyaye ba su barin yaransu mata su je su nemi ilimin boko.   Sai dai  kadan ne har yanzu ba su san muhimmancin ilimi ’ya mace ba, amma muna nan muna bugawa har sai mun shawo kan wannan matsalar.

Wane hanya kike ganin idan an bi za a iya shawo kan wannan matsalar?
A kara fadakar da iyaye muhimmancin ilimin mata a al’umma.   Wayar da kan da ake yi shi yas a abin ya kara bunkasa.   Saboda haka mu dore da yin haka har sai mun magance abin kwata-kwata.
Wane kalubale kika fuskanta ta dalilin

wannan aikin?
 Kasancewata mace, a duk lokacin da mace ta fara haihuwa abubuwa za su dan canza, amma da jajircewa komai zai yi daidai.  Sannan ni ban samu matsala a wurin neman ilimi na  da aiki na ba tun daga kan iyaye na har kan miji na, duk sun ba ni goyon bayan su dari bisa dari.   Shi ya sa duk wani kalubalen da na fuskanta bai zo mini da zafi ba.

Mene ne cigaban da kika samu ta dalilin wannan aiki?
Babban cigaban da na samu shi ne, samun ilimi domin kuwa babu inda zan dosa da ban san abinda nake yi ba.  Kuma gwargwadom hali ina bayar da tawa gudunmawa wajen cigaban al’umma.  Ba abin da zance sai Alhamdulillahi.

Ya kike hada rayuwar aure da aiki?
Gaskiya idan mace ta fahinci kanta da kuma inda ta dosa ba za ta bari abu guda ya taba dayan ba.  Aure da sana’a kowane yana da nasa mahimmanci. Sana’a ko aiki guzuri ne da  ke tafiyar da rayuwa sannan kuma shi aure ibada ne da ke sanyaya rayuwa, a ciki ne ake yin guzurin gobe kiyama.   Kin ga kuwa lallai kowane yana da mahimmanci a rayuwar dan Adam.   Alal misali mace, dole ne ta rarrabe wadannan abubuwa, kowane da akwai lokacinsa.

Me kika fi so a rayuwa? Zaman lafiya da kwanciyar hankali.
Ya kike son a rika tunawa da ke?  A tuna da ni a matsayin mace mai son zaman lafiya.
Menene shawarar ki ga matan arewa don samun cigaban al’umma?
Shawarata ita ce mu sani cewa ilimi shi ne gishirin rayuwa.  Mu rungumi ilimi da hannu biyu.  Kuma kada mu yi sake wajen kula da iyalin mu saboda muna aiki ko makaranta.  Mu ba kowane bangare hakkinsa.