Ilimi shi ne gishirin zaman duniya – Mariya Abdullahi

Hajiya Mariya Abdullahi, Garkuwar Bakori na daya daga cikin matan da suka yi fice a aikin jarida, sannan ita ce mace ta farko da ta fara shugabancin karamar hukuma a siyasance a Arewacin kasar nan a lokacin jam’iyyun SDP da NRC.  Kazalika ita ce mace ta farko da wani Hakimi ya bai wa sarautar gargajiya […]

Ilimi shi ne gishirin zaman duniya – Mariya Abdullahi

Hajiya Mariya Abdullahi, Garkuwar Bakori na daya daga cikin matan da suka yi fice a aikin jarida, sannan ita ce mace ta farko da ta fara shugabancin karamar hukuma a siyasance a Arewacin kasar nan a lokacin jam’iyyun SDP da NRC.  Kazalika ita ce mace ta farko da wani Hakimi ya bai wa sarautar gargajiya daga cikin hakiman masarautar Katsina.

 

 

Tarihi: Sunana Hajiya Mariya Abdullahi Bakori. An haife ni a garin Bakori a  1954. Na yi karatun firamare da sakandare duk a garin Zariya. Na yi aure ne bayan na kammala akandare.  
Mijin da na aura yana aiki ne a gidan rediyo da talabijin na Kaduna saboda haka maimakon in wuce da karatun da nake da sha’awar ci gaba sai na samu aiki a nan inda na yi aiki a matsayin mai sanar da shirye-shirye (Announcer) a bangaren rediyo da kuma bangaren talabijin. An kuma dauke ni aikin ne a  1972  bayan shawarar da wani babban ma’aikaci a wajen mai suna Alhaji Rabi’u Bako ya bayar ta irin yadda ya ji ina magana da Ingilishi. Ina cikin wannan aiki ne ba na mantawa sai aka tura ni Legas domin samun horo a kan wannnan aiki.
Zan iya tunawa malamin da ya koyar da mu ana kiransa Bode Alalade. An koyar da mu ne a kan yadda za mu iya furta kalma kamar yadda take da sauran ayyukan da suka jibanci aikina.
To bayan wannan, na kuma kara samun damar wani horon inda na samu diploma a wajen karanta labarai da gabatar da shirye-shirye a rediyo da talabijin, inda horon ya hada da yadda za mu rika yin kwalliya in za mu fito a akwatin talabijin. Na yi tsawon shekara biyu ina karbar wannan horo a Ingila.
Amma fa kada a manta, duk wadannan abubuwa da nake yi ina da aure, saboda haka ana wadannan abubuwa kuma ana samun hayaiyafa, don haka abin sai ya zamo ga aiki sannan ga hidimar gida da ta yara. A takaice na yi wajen shekara 15 ina wannan aiki.
Siyasa: To kamar yadda na shaida muku, na samu kamar shekara 15 ina wancan aiki na jarida a gidan rediyo da talabijin na kasa (NTA) da ke Kaduna.  To sai mutane daga garinmu na Bakori suka zo suka neme ni da in zo in shiga harkar siyasa in kuma tsaya takarar shugabancin karamar hukuma. Na shigo harkokin siyasar inda na shiga Jam’iyyar SDP a wancan lokaci.   
A 1990 kuma Allah cikin ikonSa ya sa na samu nasarar wannan zabe, wanda ya zamo ni ce mace ta farko a Arewa wadda ta fara shugabantar karamar hukuma a cikin harkokin siyasa. Akwai wasu matan daga bangaren Kudancin kasar nan da su ma suka samu nasara, amma a Arewa dai ni ce mace ta farko.  
To kafin in yi nisa ina so ka sani, a duk lokacin da na samu dan sarari ina yin karatu domin ni mutum ce mai son yin karatu don kara zurfafa ilimina. To da na ga na koma sashin mulki sai na yi amfani da wannan dama na ci gaba da karatu inda na yi digiri a kan ilimin kasuwanci a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya. Na yi digiri na biyu a kan hulda da kasashen waje.
A matsayina na Shugabar karamar Hukuma shekara daya kawai na yi aka rushe mu a inda aka kirkiro karamar Hukumar danja daga cikin Bakori. To daga nan ban sake shiga harkar siyasa ba sai a 1992 inda na sake tsayawa takara a matsayin ’yar Majalisar Tarayya.  Nan ma na ci zaben. Ina bisa wannan kujera ce har lokacin da Abacha ya hau mulki inda shi ma ya rusa mu, na dawo gida.
To irin  jajircewar da na yi ne ya sa a wancan lokaci Makaman Katsina, Hakimin Bakori (Allah Ya jikansa) Alhaji Sule Idris ya ba ni sarautar Garkuwar Bakori a shekara ta 2006, wanda a  lokacin ni kadai ce mace da aka taba yi wa irin wannan nadi a masarautar wani hakimi daga cikin hakiman masarautar Katsina.
Har ila yau kabilar Ibo da ke zaune a  Katsina sun nada ni sarautar Uwar Ibon  Jihar Katsina.
Aiki: To bayan na dawo gida a wancan lokaci mulki ne na soja sai aka zabo wasu daga cikinmu kuma aka ba ni mukamin Babbar Darakta a Ma’aikatar Ciniki da Masana’antu ta Jihar Katsina.  Bayan shekara guda a bisa waccan kujera, ai aka yi kwaskwarima a ma’aikatun inda na koma Ma’aikatar Kula da Harkokin Mata a matsayin Babbar Sakatariya. Bayan shekara uku ina bisa wanan kujera daga bisani sai aka sauke ni.
Daga nan ban sake yin wani aiki ba har sai da siyasa ta sake dawowa. Na koma siyasa inda aka ba ni Shugabar Mata ta Jam’iyyar PDP. To bayan an ci zabe sai marigayi Umaru Musa ’Yar’aduwa wanda shi ne ya ci zaben Gwamna ya ba ni mukamin Kwamishina a Ma’aikatar Watsa Labarai.
Bayan shekara daya kuma aka mayar da ni Ma’aikatar Raya Karkara, Jin Dadin Jama’a, Harkokin Mata, Matasa da Wasanni a matsayin Kwamishina har na tsawon shekara uku. Da aka ci zabe karo na biyu sai aka ba ni mukamin Mai bai wa Gwamna Shawara a Harkokin Mata, shi na har tsawon shekara hudu.
To tun daga wancan lokaci kimanin shekara tara ke nan ban sake rike wani mukami na gwamnati ba har zuwa yau. Sai harkokina suka koma a kan harkokin kungiyoyi irin su na tsofaffin shugabannin kananan hukumomi da na ’yan Majalisar Tarayya.
Ta baya-bayan ita ce wadda UNICEF ta kawo ana kiranta HILWA(High Lebel Women Adbocate). Aikin wannan kungiya shi ne wayar da kan mata a kan batun da ya shafi ilImi da muhimmancinsa.
kalubale: Lallai akwai kalubale musamman ga rayuwar  mace, ba ma kamar ta fuskar aiki. Bari in ba ka misali da ni, a lokacin da nake aikin jarida,wanda kowa ya san aiki ne wanda ba kasafai ake ganin mata a cikinsa ba,wannan kawai wani kalubale   a ce mace tana gwagwarmaya a cikin irin wannan aiki da maza suka fi yawa a cikinsa.
Hatta shiga cikin ita kanta siyasa ga mace, wani babban kalubale ne wanda za ta iya samun cikas ta kowane fanni ,wanda dole sai an sanya hakuri a ciki.
Ba zan taba mantawa ba wani lokaci, ina aiki a gidan talabijin, ga nakuda ina ji tamkar zan haihu a wannan lokacin sannan kuma ga shi ni ke aiki.
Har sai da Allah Ya sa na tashi daga aikin a nan aka kawo mota aka kai ni asibiti wanda kafin ka ce kwabo na haihu. Ka ga wannan shi ma wani kalubalen ne. Kai sai da ta kai fagen ni da mijina muna raba ayyukan cikin gida.
Ka san shi aikin jarida aiki ne wanda yake bukatar lokaci wanda wata sa’ar har kwana kana iya yi a wajen aikin. Ina kuma iya tunawa cewa ina cikin mutum biyu da aka dauka wadanda aka tura zuwa Amurka don samun wani horo a kan aikin jarida,wanda ma wannan zuwa har ya ba ni damar samun takardar zama ’yar kasar Amurka wadda duk lokacin da nake so zan iya zuwa can in zauna.
Ka ga wadannan abubuwa duk wasu kalubale a gare ni kasancewata mace. Kuma dukkan wadannan abubuwa sun faru ne saboda juriya da kuma gwagwarmaya da na yi,wanda Allah cikin ikonSa duk Ya kawo mini haka. Ka ga ko lokacin da na shiga zabe na fuskanci wani babban kalubale saboda an yi zaben ’yar-tinke ne. In zan tsaya fadi irin kalubalen da na fuskanta ko in ce mata ke fuskanta suna da yawa.
Ka ga zama na mamba a kwamitin gudanarwa a cikin wasu muhimman wurare irins u Gidauniyar Jihar Katsina da Asibitin kashi da ke Enugu da Hukumar kidaya ta kasa da kuma ta Makarantar Gwamnatin Tarayya ta ’Yan mata da ke Bakori da sauran wurare da dama, duk sun zama wani kalubale ne a gare ni.
Kuma kwanan nan ne Mai girma Gwamnan Jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari ya sanya ni a cikin wani kwamitin da zai  binciko halin da Ma’aikatar Kula da Bayar da Ilimin Mata yake ciki, kuma mun yi aikin mun gama lafiya.
Burina: To farko dai ni babban burina shi ne in gan ni ina karatu. Kuma ina da sha’awar in ga ina taimakon marasa karfi. Ku san cewa mata suna neman ilimi ko yin gwagwarmaya ne don tsira da mutuncinsu, saboda yanzu lokaci ya canja da mace za ta ce komai sai an yi mata.
Kuma ina da sha’awar sanya tufafi na kawa wadanda suka hada har da na gida. Ni mace ce mai son yin tafiye-tafiye domin tafiya mabudin ilimi ce. Na je kasashe da dama irin su Ingila da Amurka da China da Japan da Senegal da sauransu.
A nan cikin gida Najeriya kuwa babu jihar da ban je ba. Ina son sanya turare mai kanshi kuma mai tsada. Daga cikin nau’in launi kuwa, mai ruwan kasa na daya daga cikin launin da nake sha’awa. Ina kuma da sha’awar in ga na yi duk wani aikin da aka ba ni cikin lokaci kuma kamar yadda aka ce wanda hakan zai sa a yaba mini. Ina kuma da sha’awar in ga ko a cikin taro na shiga ya zamo na bambanta da saura a wajen yin shiga mai kyau.
Darasin da na koyo na aikin talabijin ya ba ni damar iya yin shiga ta a-zo-a-gani a wajen yin kwalliya. Ka san mutane suna kallon matsayinka hatta ta hanyar sanya tufafin jikinka. Ina da sha’awar in ga komai na cikin tsabta. Har wa yau,ina da sha’awar in ga na samu lokaci don in roki Ubangijina. Wadannan abubuwa na daga cikin irin abubuwan da nake sha’awa a rayuwata.
korafi: To ni dai babban korafina ga mata shi ne akwai mata da yawa a wannan zamani da suke cewa lallai sai namiji ya yi musu komai.  Su sani yanzu rayuwa ta canja.
Ina so mata su mike tsaye su ga cewa wannan karatu na zamani sun yi shi. Wadanda kuma ba su samu damar yin sa ba, to su tabbatar cewa ’ya’yansu sun samu wannan ilimi na zamani da na addini. Su rika sanin abokan ’ya’yansu da kuma sanin inda duk suka je ko suka shiga, ba wai sai daga baya ba a rika yin da-na-sani.
Kirana: Ina kira da babbar murya musamman ga mata cewa su tashi su nemi ilimi. Ilimi a wannan zamani yana gaba da komai. Mata suna sakaci wajen nemansa.  Rashinsa ne ke sa ana barin mata a baya, amma muddin mace na da ilimi to za ta iya shiga kowace irin gwagwarmaya. Sai kira na na biyu ga jama’a baki daya shi ne mu ci gaba da yi wa kasar nan tare da shugabanninta addu’ar zaman lafiya. Wannan matsala musamman ta Boko Haram Allah Ya kawo mana karshenta.