Ilimin ’ya mace na da tasiri – Hajiya Rakiya Isma’il Ahmad

Hajiya Rakiya Isma’il Ahmad ita ce Shugabar Sakandaren ’Yan Mata ta G.G.S.S. da ke Kawo Kaduna.  A zantawarta da wakilinmu ta bayyana tarihinta da nasarorin da ta samu da kuma irin kalubalen da ta fuskanta kafin ta kawo wannan matsayi.  Ta nuna ilimin ’ya’ya mata na da tasiri ga al’umma, musamman a wannan lokaci da […]

Ilimin ’ya mace na da tasiri – Hajiya Rakiya Isma’il Ahmad

Hajiya Rakiya Isma’il Ahmad ita ce Shugabar Sakandaren ’Yan Mata ta G.G.S.S. da ke Kawo Kaduna.  A zantawarta da wakilinmu ta bayyana tarihinta da nasarorin da ta samu da kuma irin kalubalen da ta fuskanta kafin ta kawo wannan matsayi.  Ta nuna ilimin ’ya’ya mata na da tasiri ga al’umma, musamman a wannan lokaci da zamani ya canja.  Ga yadda hirar ta kasance:

Takaitaccen tarihin rayuwa:

Sunana Hajiya Rakiya Isma’il Ahmad. An haife ni a Kawo da ke Kaduna a shekarar 1966. Na yi karatun firamare a L.E.A Primary School Kawo, Kaduna daga nan bayan mun yi jarrabawar shiga sakandare da aka fi sani da Common Entrance sai na samu makarantar horar da malamai ta ’yan mata da ke Katsina watau WTC Katsina. Na shekara biyar a can kuma na samu shaidar karatu na Grade 2. Amma kafin nan a lokacin da nake aji hudu na so na canza layi daga bangaren koyarwa zuwa wani bangare kamar Lauya don haka sai na zauna jarrabawar GCE tun ina aji hudu, to a gaskiya manhajar karatun sakandaren gwamnati ya fi na bangaren horar da malamai tsanani a wancan lokaci don haka sai na fadi jarrabawar, daga nan ne na hakura na karbi harkar koyarwa a matsayin kaddara. A shekarar 1984 na gama Kwalejin Horar da Malamai ta mata WTC Katsina daga nan na wuce Kwalejin Horar da Malamai watau College of Education ta Kafanchan inda na karantar Biology/Chemistry inda na kammala a shekarar 1988. Amma dai kafin na kammala ne na yi aure kuma auren bai hana ni yin karatun ba. Hasalima haihuwar farko na yi ta ne a lokacin da nake karatu. Bayan na kammala karatun ne sai na dawo gida na fara aiki a shekarar 1989 a matsayin malamar makaranta, inda na koyar a bangaren Kimiyya a Dalet Girls Junior Secondary School da ke Kawo Kaduna. A shekarar 1990 kuma sai na lura daga cikin malaman da ke koyarwa akwai masu digiri yayin da ni kuma nake da NCE a nan ne na koma Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya inda na samu digiri a bangaren Biological Sciences (Bsc Ed.). Daga nan na zama Assistant H.O.D na zama H.O.D na sake zama Senior Mistress daga nan kuma na zama bice Principal. Duk wadannan mukamai na rike su ne a makarantar Dalet da ke Kawo. Kwalejin Dalet kuma mallakar gwamnatin jiha ce.
Na fara zama shugabar makaranta ce watau Principal a wata makaranta da ke Rafin Guza a shekarar 2004. Daga nan aka yi mini canjin wurin aiki zuwa wata makaranta a Hayin Banki, da ake kira Dokta Ahmed Mohammed Makarfi Secondary School a shekarar 2005, watau makaranta ce hade da maza da mata (mided school). Na shekara 10 a wannan makaranta inda na yi kokari wajen bunkasata musamman wajen daga martabarta daga Junior Secondary zuwa Senior. A shekarar 2009 ne aka fara yin jarrabarwar GCE ta farko. To a shekarar 2014 ne aka yi mini canjin wurin aiki inda aka mayar da ni Kwalejin ’yan mata ta G.G.S.S. Kawo a matsayin shugaba, watau Principal kuma har yanzu a nan nake aiki.

Yadda na hadu da maigida:
Maigidana shi ma an haife shi ne a Kawo, hasalima layin mu daya da shi kuma akwai dangantakar makwabtaka. Mun yi aure ne a shekarar 1985 wato ina gama karatun sakandare. Shi ma’aikacin banki ne amma yanzu haka ya yi ritaya inda yake yi wa gwamnatin Kaduna aiki a matsayin kwantaragi.

Yawan iyali:
Ina da ’ya’ya uku, mata biyu, namiji daya.

kalubalen da kike fuskanta a G.G.S.S. Kawo:
Alhamdulillah. Gaskiya muna fuskantar kalubale da dama. Na farko yaran yanzu ba su son mayar da hankali wajen yin karatu, sai an matsa musu. A da za ka tarar dalibai suna gasa ne a tsakaninsu inda suke yin rige-rigen wuce juna don samun sakamako mafi kyau amma abin ba haka yake a halin yanzu ba. kalubale na biyu akwai matsalar samun goyon baya daga wajen iyayen yara. Iyaye a da idan ka hukunta yaro ba sa kallo amma yanzu sai ka yi taka tsan-tsan don wadansu iyayen ma har cin mutunci suke yi ga malami ko malama idan ya ko ta hukunta dalibi ko daliba. Wasu suna ba mu goyon baya daidai gwargwado amma wasu kam, sai addu’a. Sannan hankalin dalibai kan yawan gushewa wajen latse-latsen wayoyin hannu da yawan kallon fina-finan da ba su da tasiri ga harkar karatunsu. Wannan ma wani yanki ne na kalubalen da muke fuskanta da daliban. A da dalibai suna gasa ne a kan yawan litattafan da suka karanta watau Nobels amma yanzu ba haka abin yake ba. Zan iya tunawa a lokacin da muke yara, mukan leka mu ga wanda yake karanta jarida inda muke fakar idonsa idan ya tashi mu dauka don mu karanta saboda mu karu, amma yanzu abin ba haka yake ba.

Tallafin da kuke samu daga wajen gwamnati:
Muna samun tallafi sosai daga wajen gwamnati, musamman ma gwamnati mai ci yanzu ta Gwamna Nasir Ahmad El-Rufa’i. Hasalima gwamnatin ta fi ba irin makarantunmu na kwana fifiko fiye da na jeka-ka-dawo (day). Misali a bangaren malaman kimiyya, gwamnati ta dauki malamai su kimanin dubu 2 inda ta raba su ga irin makarantunmu. Ka ga ba haka abin yake a baya ba. Musamman a bangaren darussan lissafi da Ingilishi da kuma na Kimiyya, Gaskiya gwamnati ta yi mana kokari a wannan fanni. Sannan shirin gwamnati na soke biyan kudin makaranta ga daliban da ke aji na daya da na biyu da kuma na uku watau JSS 1 da JSS 2 da JSS 3, shi ma wani tallafi ne daga gwamnati, kuma ya taimaka wajen sa ’ya’ya mata a makaranta fiye da a baya. Sannan gwamnati tana taimaka mana da sababbin gadaje da katifu ga sababbin dalibai. Ana raba irin wadannan kaya ne ga sababbin dalibai. A takaice dai tallafin da muka samu daga gwamnati sun hada da dauke wa dalibai kudin biyan makaranta da na ciyarwa da samar musu da rigunan makaranta da katifu da gadaje da sauransu duk a kyauta.

Nasarorin da na samu:
Babbar nasarar da na samu a rayuwa ita ce yadda na gina wadansu ’ya’ya mata a matsayina na malamar makaranta inda a yau suke alfahari da irin rayuwar da suka tsinci kansu a kanta. Na lura
ilimin ’ya’ya mata na da tasiri a al’umma. Sannan na samu nasarar kafa wata kungiya da ake kira Rahamaniyya Co-operatibe Soceity a lokacin da nake Hayin Banki. kungiyar ta tallafa wa mata marasa karfi da jari inda suka